Addabi nigeria a boye federal ministry of health, nigeria shiri na musamman ga mai kalloYüklə 82,09 Kb.

tarix17.09.2018
ölçüsü82,09 Kb.


TAMOWA: ANNOBAR DA TA 

ADDABI NIGERIA A BOYE

FEDERAL MINISTRY OF HEALTH, NIGERIA

SHIRI NA MUSAMMAN GA MAI KALLO

TAKARDAN BAYANI

CIKAKKEN PASSARA

(MINTI 20)TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE

1

           Gudanarwa za ta fara da bakin bango

 Slide 1: Click Forward (a yi shiru yayin da hoto ya fito na tsawon dakika biyar)

 Slide 2: Click Forward (a jira har sai hoton ya dauke)

 Slide 3: Click Forward

 Idan muka duba shekarun baya, a Najeriya mun samu ci gaba da dama. 

 Slide 4: Click Forward (music starts)

Mutuwar yara yan kasa da shekara biyar ya ragu daga kashi ashirin da biyu cikin dari, zuwa 

kashi goma sha uku cikin dari a dubu biyu da goma sha uku.

1

 

Tattalin arzikinmu yana karuwa ga kowane mutum daga naira dubu dari da hamsin, zuwa naira dubu dari uku da hamsin a shekarar dubu biyu da goma sha daya.

2

Yawan yara mata dake gama karamar makarantar firamare, sun karu da kashi saba’in bisa dari a cikin shekaru ashirin da suka wuce.

3

Sannan kuma mun wadata da Hanyar sadarwa……. Domin kusan mutane miliyan dari da goma sha biyar ne ke amfani da wayar salula.

Kasarmu…. na matukar ci gaba!  

Sai dai kuma, akwai wata matsala daya da ke mai da mu baya…….

 Slide 5: Click Forward 

….

TAMOWA, wato rashin ingantaccen abinci da ke jikin iyaye mata da yara tana jawa 

kasarmu asara, duk da cewar akwai hanyoyi da dama na warwaresu.► Slide 6: Click Forward

A yau, tamowa na sanadin macewar yara sama da rabin miliyan ‘yan kasa da shekaru 

biyar a 

kowace shekara a cikin kasar Nigeria……………. Wato kowane daya daga cikin 

mutuwa buyu na tamowa ne.

 4

  

► Slide 7: Click ForwardSai mu duba mu gani, wadanne darusa ne muka koya a kan tamowa a shekarun nan?

TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI  

NIGERIA A BOYE

LONG VERSION: 20 MINUTES
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE

2

► Slide 8: Click Forward

Mun koyi abubuwa uku ne muhimmai mai nuna mana mahimmancin sana’ar cimaka

5

Na farko dai, sana’ar cimaka mai kyau ta mai wayo ce, soboda tana taimakon rayuwan yara su kai gaci.

► Slide 9: Click Forward

Na biyu kuwa, mun koyi cewar cimaka mai kyau na ainihin bunkasa ci gaban lafiyar yan 

kasa……tare da rage mace-mace da rashin lafiyar uwaye da yara.

► Slide 10: Click Forward

Na uku, mun koyi cewar cimaka mai kyau Sana’a ce ta mai wayo, saboda tana qara wa yan 

qasa lafiya da habaka tattalin arzikin ta.

► Slide 11: Click Forward

Da wuya a samu wani abu da zai fi bunkasa ci gaban kasa fiye da harkar cimaka. Domin 

kuwa, cimaka tana dada bunqasa harkokin mu zuwa gaba.  

 

To ta yaya cimaka ke taimakawa wadannan muradai uku?

► Slide 12: Click Forward

Taimakon na farawa ne tun daga kwanaki dubu daya na farko, wato sanda uwa ke rainon 

ciki har zuwa yaye…..wannan kwanaki ne da ya dace jariri ko jaririya su samu kulawa ta 

musamman kafin wani cikin ko haihuwar.

6

Bari mu duba da kyau don muga mahimmancin wannan lokacin.► Slide 13: Click Forward

Tun daga mahaifa, dan tayi yana cikin hatsari in har mai cikin bata samu abinci mai gina jiki 

ba, ko abinci mai bada kuzari, wanda sune zasu taimakawa ginin kwakwalwa da kashi da 

sassan jiki.Rashin isashen abincin yana kawo karancin jini tare da matsala wurin haihuwa.

Da zarar an haifi jariri….daga haihuwa zuwa wata shidan farko, a shayar da jariri nonon uwa 

zalla, ba tare da wani abinci ba don tabbatar da lafiyar yaro.

Bayan wata shidan farko, karin nagartaccen abinci ga yaro ya zama dole, don tabbatar da 

lafiyar jariri yadda ya kamata domin kuwa ciwuka na shiga a wannan tsakanin.

► Slide 14: Click Forward 

(A dakata sai karan ganga ya wuce)

………….BA GUDU BA JA DA BAYA………
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE

3

Barnar rashin cimaka mai kyau a kwanaki dubun farko (daga haihuwa zuwa yaye) ba ta gyaruwa…….

► Slide 15: Click Forward

•  Domin takan lalata kwakwalwa, ta mai da yara dakikai, masu raunin fahimta  

•  Sannan tana hana su girma yadda ya kamata…….

•  Bugu da kari, tana haifar musu da munanan cututtuka har zuwa girman su► Slide 16: Click Forward 

Kamar munanan ciwawuka irin su ciwon siga, da hawan jini, da ciwon zuciya, wadanda ke 

wahalar da jiki matukar ana raye.

 7

► Slide 17: Click Forward  

Wata babban matsalar shine, mafi yawan jama’a basu gane cewa tamowa ga yara na faruwa 

har tsawon shekaru ba tare da an gane ta ba.

 

Misali wadannan yaran daga kauye daya suke…..ko za a iya kwatanta shekarun su?Duk fa shekarun su daya…….shekarun su takwas-takwas…….amma kun ga akwai 

banbancia giman jikinsu.

Yaron da ke hagu tsamurarre ne, wanda ke nuna jikinsa bai daidai da shekarunsa ba, saboda 

karancin abinci mai kyau. Wannan yaron da wuya ya kamo sauran sa’annin sa kamar abokin 

wasan sa da ke dama.

► Slide 18: Click Forward

Cutar tamowa na haifar da salo daban daban da ake gani daga zamani zuwa zamani…….

Misalin illar tamowa daga zamani zuwa zamani…

► Slide 19: Click Forward

…..yana iya farawa daga matar da bata samu cikaken abinci mai gina jiki ba, to tana cikin 

hatsari matuka tun daga lokacin da zata dauki ciki, har zuwa yaye. Ga kuma hatsarin 

haihuwar da mara kwari.

8

► Slide 20: Click Forward

 …….Kamar wannan yarinyar, wacce ke halin rai kwa-kwai mutu kwa-kwai, tare da hadarin 

kamuwa da karancin ci gaba da rashin fasaha.

 

► Slide 21: Click Forward

 ……..Za ta iya samin nakasu wajen girmanta da tunanin ta……..wanda…TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE

4

► Slide 22: Click Forward 

…….Kasancewan haka kuwa sai 

budurcin ta ya tawaya, domin a wannan locacin ne 

kashi hamsin daga cikin dari na kasusuwan jikinta ke girma.

9

► Slide 23: Click Forward

Kasancewar tamowan da ke jikinta……… kuma, zata dawo kamar wannan matar ta cikin 

taswira, kun ga tamowa ke nan na bibiyar ta tsawan zamani zuwa zamani. 

► Slide 24: Click Forward

Kun ga wannan yarinyar in ta dauki ciki ba mamakin ta haifi jariri mara kwari, yin hakan, na 

karfafa taswirar tamowa.

10

 Abin takaici, iyalai da dama na fama da rashin samun lafiyayyun jarirai a kasar nan………

► Slide 25: Click Forward 

 Me ya sa Najeriya ta ke ci gaba da samun matsalar tamowa? 

► Slide 26: Click Forward

Babban dalili shine iyaye mata ba su san yadda za su kula da jarirai da kananan yara ba. 

Sannan ba su da kyakkyawar fahimta akan sanda ya kamata su fara bada abinci mai nauyi 

da kuma nau’in abinci daban daban, wanda zai taimaka wa jiki wajen girma.► Slide 27: Click Forward 

Wani dalilin shine rashin sa ido akan abinda ake nomawa a kasar, wanda ke jawo iyalai da 

yawa basu samun ishasshen abinci. 

Ba a arewa kawai ake samun haka ba. 

► Slide 28: Click Forward

Idan muka duba taswirar kasar Najeriya, zamu fara da leka cikin babban birnin Abuja, mu ga 

yadda hidimomin su suke. Nan ga babban filin wasan kwallo na gabashin Abuja. 

Shigar mu cikin garin, za mu ga akwai ci gaba sosai a cikin ta, wanda har za a ga cewa 

nan, samuwar tamowa zai yi wuya saboda Abuja ita ce karfin kasar…… amma sam ba 

hakan bane, domin binciken kwanannan ya nuna cewa kowane yaro daya a cikin yara guda 

biyar tsamurarre ne.

11

TELEPORT Yanzu mu juya jahar Lagos, mu maida hankalin mu akan unguwar Mushin, wanda ke da 

tarin jamaa sama da dubu dari biyar. Sun kasance a cakude da junan su, kuma ba tare 

da wadata ba…... Tamowa na kusan kowane gida saboda kashi daya bisa uku na yaran 

unguwar suna da tamowa.

12TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE

5

Duk da ya ke talauci na kara yawan tamowa, ba talakan kadai ke dauke da tamowa ba.

TELEPORT


In muka matsa unguwar Ikoyi, wato unguwar da masu arzikin jihar Legas ke zaune, suna 

da manyan gidaje da wadata. Ba wuya a dauka cewar tamowa ba za ta shiga gidajen su 

ba saboda karfin arzikinsu.  Yaya za a yi a sami Tamowa a irin 

wannan wajen. To amma 

duk da haka, kashi goma sha uku bisa dari na yaran masu arziki a wannan unguwan suna 

dauke da cutar tamowa.

13

 

TELEPORTA ci gaba da tafiyar mu, mun fahimci cewa babu wani bangare a cikin kasar nan da Tamowa 

bata shafa ba

TELEPORT

Gamu a jihar Niger Delta, jiha mai arzikin man fetur….. Sana’ar su ita ce kamun kifi da 

noma don su samar wa kansu abinci mai gina jiki. Amma wannan bai sa jihar ta wadatu da 

ingantaccen abinci ba.

Cutar tamowa babbar matsala ce ga yaran Jihar Delta, saboda kowane daya daga cikin 

yara biyar na dauke da ita.

 14

TELEPORT


A karshe kuma, mun gano cewa cutar tamowa tana nan a wuraren da noma itace sana’ar 

da suka dogara da ita.

Kaman a nan, arewacin najeriya, za ku ga noma ita ce babar sana’ar su, a dalilin hakan, 

suna samun wadatacen abinci na tsawon shekara, har su bawa makotan su ba tare da 

gazawa ba. Haka zalika abinci mai gina jiki baya yanke musu. Amma duk da haka, sai da 

tamowa ta sami wajen zama a yakin.

(A dakata)

Abin takaici ne yanda tun shekarun baya, har izuwa yanzu, ba a samun cikakiyar ci gaba, 

don hana yaduwar cutar tamowa.

► Slide 29: Click Forward 

Ka duba ka gani tun shekaru goma da suka wuce……….► Slide 30: Click Forward 

…….Bincike ya nuna cewa ba a samu kwakkwaran ci gaba ba a harkar yaki da cutar tamowa. 

Amma binciken shekara ta dubu biyu da goma sha uku ya nuna an sami 

dan cigaban da 

ba a rasa ba…

15

► Slide 31: Click Forward 

 ….Duk da haka dai, sama da kashi daya bisa ukun yaran kasar nan tsumburarru ne.

 16TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE

6

► Slide 32: Click Forward

Kamar yanda muka gani a cikin taswira, wadda ta nuna mana misalin yaduwar tamowa 

a kasar mu, babban bangaren da ake ganin ma bata da yawa sosai, a kowane yara biyar 

zakaga akwai daya mai dauke da tamowa,wato a kudu maso kudu da kuma kudu maso 

yamma. A arewa maso gabas kuwa, kusan ma RABIN yaran na da matsananciyar tamowa.

17

► Slide 33: Click forward 

Hukumar samar da lafiya ta majalisar dinkin duniya ta jaddada mahimmancin ba wa jarirai 

abinci mai nauyi mai gina jiki bayan wata shidan farko don samun cikakkiyar kariya daga 

cututtuka………

18

 ► Slide 34: Click Forward

Amma bincike ya nuna cewa jarirai biyu cikin uku ba sa samun cin abincin daya dace.

19

 Mafi 


yawa suna cin abinci mai danko ne, irin su rogo da shinkafa a maimakon ‘ya’yan marmari da 

ganyaye da nama da kifi da kwai -wanda za su gina musu jiki.► Slide 35: Click Forward (TRENDALYZER)

Don mu ga masu samun cikakken nonon uwa a Najeriya, muna iya mu kwatanta Najeriyya 

da kasar Ghana.

► Slide 36: Click Forward 

A ta bangaren hagu, muna da lissafin jarirai yan kasa da wata shida masu shan nonon uwa 

zalla. Wannan kason ya taso daga sifili zuwa kashi tamanin bisa dari.

► Slide 37: Click Forward 

 A bangaren kasa kuwa, akwai lissafin lokaci, daga Alif dubu daya da dari tara da casa’in da 

hudu zuwa shekarar dubu biyu da goma sha uku.

► Slide 38: Click Forward 

Mu lura cewa a shekarar Alif dubu daya da dari tara da casa’in da hudu Nigeria da Ghana 

suna da kashi bakwai bakwai cikin dari na yawan jarirai masu samun nonon uwa zalla. 

In mu kai ta tafiya, mu duba abin da ya faru tsawon lokaci a kowace kasa….zamu ga 

cewa…..kason… 

► Slide 39: Click Forward

…..jariran da ke samun nonon uwa zalla a kasar Ghana kullum habaka ya ke…… yana 

sama….yana kara sama.

► Slide 40: Click Forward

…..Har sai da ya kai ga cewa, kashi sittin da uku ne na jarirai, ko kusan biyu cikin uku na 

jariran Ghana, suna samun cikakken nonon uwa a shekarar dubu biyu da goma sha uku.

 20TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE

7

► Slide 41: Click Forward

…..Sabanin a Najeriya, wanda kashi goma sha bakwai ne kawai (wato kowane daya daga 

cikin shida) suke samun cikakken nonon uwa.

21

  

To me Ghana kasar Ghana tayi data samiwannan ci gabar? ► Slide 42: Click Forward 

 A shekarar alif dubu daya da dari tara da casa’in da biyu sun kirkiri tsarin shayar da nonon 

uwa zalla…..

22

► Slide 43: Click Forward

……Daga kuma shekara ta alif dubu daya da dari tara da casa’in da biyar, suka samar da 

asibitoci na musamman masu goyan bayan shayar da nonon uwa zalla, wannan tsarin yai 

nasara wajen kiwon lafiyar jarirai.

 23


► Slide 44: Click Forward 

A shekara ta dubu biyu, Ghana ta kafa hukumar tabbatar da shayar da nonon uwa zalla, 

sannan kuma ta hana yawan tallace tallacen madarar jarirai don neman samun canji.

 24


 

      


► Slide 45: Click Forward

Duk da haka kungiyoyin karkara sukai ta bin gida gida don ilmantar da al’umma akan 

muhimmancin shayar da nonon uwa zalla ga jarirai.

► Slide 46: Click forward 

Sanan kuma bugu da qari, akayi ta amfani da kafofin yada labarai dan horarwa a kan 

muhimmancin nonon uwa zalla, duk don a kara tabbatar da cewa shirin ya samu karbuwa 

a wajen jamaa.

 25

► Slide 47: Click Forward 

To da a ce Najeriya za ta gabatar da irin wadannan shirye-shirye, wato kafa dokoki, amfani 

da kafafen yada labarai, da neman hadin kan kungiyoyin karkara, lallai 

mu ma zamu samu 

ci gaba da gaggawa ta bangaren shayar da nonon uwa zalla.

 (A dakata)

Mun san ba shakka, wannan matsalar da ke tare da mu za ta iya zama tarihi saboda…..► Slide 48: Click Forward

Mun 


san abubuwan da zasu iya kawo mana canji!

Idan aka jarraba abubuwa hudun nan, za su iya zama kariya ga uwaye da jarirai………… 

Na farko shine……..

26TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE

8

► Slide 49: Click Forward 

Bada nonon uwa cikin minti talatin daga lokacin da aka haifi jariri, sannan a cigaba da nonon 

uwa zalla har tsawon wata shida ba tare da ba jariri ko digo daya na ruwa ba. 

(A dakata)► Slide 50: Click Forward

 ……Na biyu kuma shine in za a tabbatar da bawa jariri nau’in abinci mai gina jiki bayan wata 

shidan farko, tare da ci gaba da bada nonon uwa har tsawon shekaru biyu.

► Slide 51: Click Forward 

Na uku shine, a tabbatar da cewa uwa da jaririnta na samun isasshen abinci, wanda zai 

wadata su……….

► Slide 52: Click Forward 

…….. abinci ingantacce ……sannan iri daban-daban.► Slide 53: Click Forward

Domin iyali su kasance suna samin wadataccen abinci mai gina jiki, a ko da yaushe.► Slide 54: Click Forward

A takaice dai yana da kyau iyaye mata da sauran ma su lura da jarirai su ringa samun bayanai 

akan yadda za su shayar da jariransu dan samun cikakkiyar lafiya.

 (A dakata)

 

► Slide 55: Click Forward 

Idan muka waiwaya kan dalili na uku, wato abin da yasa muka ce samar da abinci mai gina 

jiki sanaar mai wayo ce.…..saboda yin hakan ba faduwa ba ne sai dai karuwa.

► Slide 56: Click Forward

Cimaka mai gina jiki a kwana dubun farko na haihuwa takan samar da amfani mai yawan 

gaske ga iyali da kasashe baki daya. [Kamar wannan nagartacen dan wasan kwallon!!]

► Slide 57: Click Forward 

Lafiyayyun yara sukan fi gama makarantarsu da kyakkyawan sakamako, Don haka yawan 

samin su naiya ninkuwa da kashi goma cikin dari fiye da wadan da basu sami kulawa ba.

 27


► Slide 58: Click Forward

Tunda lafiyayyan abinci a kwana dubu na haihuwa ya na kara kwazon yara a makarantu, 

yaron da aka lura da shi har ya girma yakan zama fitacce…….hakan na iya samun cigaban 

tattalin arzikin kasa har ninki goma sha daya a cikin dari a kowace shekara.

28TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE

9

► Slide 59: Click Forward

Ko nawa aka ware don samar da abinci mai gina jiki ga al’umar kasa bai yi tsada ba- don 

amfanin da ke cikin ta zai ba da kyakkyawan sakamako.-wato sa jari a harkokin samar da 

cimaka yakan ninninka riba har ta fi uwar kudin da aka zuba da kashi 

ashirin da biyar.

29

► Slide 60: Click Forward

Kun ga ke nan kowace naira dubu dari da aka ware wajen samar da abinci mai gina 

jiki………….► Slide 61: Click Forward

……Zai ba da ribar kwatankwacin Naira maliyan biyu da rabi a wajen bunkasa tattalin arzikin 

kasa.

► Slide 62: Click Forward

In da zamu natsu mu duba yadda za mu sami ci gaba, zamu gane cewar a yau….. muna da 

damarmakin ci gaba a harkar abinci mai gina jiki ………fiye da yanda muke a baya.

► Slide 63: Click Forward 

Mun sabinta tsarin nan na kasa akan cimaka mai gina jiki……yanda zai ba da karfi akan 

ka’idojin da za su kare mana burikan mu dan kawar da cutar tamowa. 

► Slide 64: Click Forward

 Mu kafa sababbin dabaru kamar ceto rayuka miliyan daya, da niyyar taimakawa mabukata 

da cimaka mai gina jiki a cikin kasa.

► Slide 65: Click Forward

Sannan mu na da karkarfar cibiya wacce ta tashi tsaye dan habbaka abinci mai gina jiki 

a kasa – wadda kuma take neman hadin kan shugabannin duniya da su yi yaki da cutar 

tamowa.


Nigeria ta hadu da kasashe arba’in da biyar da kungiyoyi na kasa da kasa guda dari da 

kuma kungiyoyi masu bada gudunmawa ga kasashen duniya…..dan su hadu wajen mai da 

hankali akan shawo kan cutar tamowa.sun lashi takobi don yaki da cutar tamowa.

► Slide 66: Click Forward 

Tamowa Annobar kasa ce gaba daya………..

…………………………….saboda haka, samo mafitar ta ma, sai an hada hannu gaba daya.

(A dakata)► Slide 67: Click Forward 

Mu na da hujjoji………….. na irin abubuwan da zasu iya kawo mana canji
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE

10

► Slide 68: Click Forward 

Muna neman ku magantu da yin kira wajen rage cutar tamowa 

……sannan ku ja hankalin al’umma  da gaggawa da su dunfari cimaka mai gina jiki musamman 

ma mata ma su ciki da yara kanana….. sannan muna kira da ku sa ido a kan iyaye mata don 

tabbatar da sun shayar da jariransu nonon uwa har iya tsawon lokacin da ya dace.► Slide 69: Click Forward

Muna dada rokon al’umma da su tashi tsaye wajen tabbatar da cewa an habbaka  cinikin 

cimaka mai gina jiki a kowane bangare na maaikatu da ma su zaman kansu, kamar ma’aikatar 

kudi,da ta tsare-tsare,da ta gona,da ta ilimi,da ta harkokin mata, da ta muhalli da ta ruwa. ► Slide 70: Click Forward 

Muna dada rokon hukumomi su kara hada hannu dan tsai da mafita a kan cimaka mai gina 

jiki a cikin maaikatu…….musamman maaikatun  kudi, da na tsare tsare, da na noma, da na 

ilimi, da na harkokin mata, da na mahalli, da na ruwa. ► Slide 71: Click Forward 

 A karshe mu na dada rokon ku da a agaza mana da karin tallafi....wato, zai yi kyau a 

sami kasafin kudi na MUSAMMAN a cikin asusun maaikatar lafiya, da na gona, da kuma 

asusun jihohi gaba daya, don biya wa bukatar kawar da wannan annoba  ta tamowa.

Ba zai yiwu mu rasa 

duk damarmakin da mu ke da su ba.

► Slide 72: Click Forward 

In da za mu saka jari akan cimaka mai gina jiki….► Slide 73: Click Forward 

•  Za mu iya tabbatar da cewa yaran mu sun yi kwari sun kai gaci…….

•  Mu kuma rage yaduwar cututtuka da mace-mace na uwa da kananan yara   

•  Tare da tabbatar da ganin tattalin arzikin mu ya habaka a gaba. ► Slide 74: Click Forward 

Inda zamu taru mu hada karfi da karfe……..

(A dakata har sai wasu jerin kalmomi sun fito)

…. Zamu iya cimma burinmu nan gaba akan ayyukan mu na baya

(A dakata har sai wani jerin kalmomi sun fito)

Zamu iya 

tsayar da annobar tamowar da ta mamaye mu……TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE

11

Mu agazawa masu bukatar taimako…...(A dakata har sai wani jerin kalmomi sun fito)

Za mu iya kawar da tamowa daga doron kasar Nigeria baki daya.

► Slide 75: Click Forward 

(A tsaya shiru) 
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE

12

REFERENCES1

  World Bank, “Data Bank,” accessed at  http://data.worldbank.

org/indicator/SH.DYN.MORT?page=6, on Nov. 10, 2014; 

and National Population Commission of Nigeria and ICF 

International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013 

(Abuja, Nigeria, and Rockville, MD: and ICF International, 2014).

2

  Index Mundi, “Nigeria: GNI per Capita,” accessed at: www.indexmundi.com/facts/nigeria/gni-per-capita, on Nov. 10, 

2014. The latest value for GNI per capita, PPP (current 

international $) in Nigeria was 2,290.00 as of 2011.

3

  Nigeria Communications Commission, “Subscriber Database,” for year 2012/2013: 113,195,951 active users; 

accessed at: www.ncc.gov.ng/index.php?option=com_

content&view=article&id=125:art-statistics-subscriber-

data&catid=65:cat-web-statistics&Itemid=73, on Nov. 10, 

2014.

4

  Population Reference Bureau calculation based on birth data from: United Nations, World Population Prospects: The 2012 

Revision (New York: UN, 2013); and on the under-5 mortality 

rate from the National Population Commission of Nigeria and 

ICF International, Nigeria Demographic and Health Survey 

2013. 

5

  Ogilvy Public Relations Worldwide and the Academy for Educational Development, A Communications Strategy to 

Mobilize Nutrition Investment (Washington, DC: The World 

Bank, 2009).

6

  1,000 Days Partnership, “Why 1000 Days” (2013), accessed  at www.thousanddays.org/about/, on March 10, 2014.

7

  Cesar G. Victoria et al., “Maternal and Child Undernutrition: Consequences for Adult Health and Human Capital,” Lancet 

371, no. 9609 (2008): 340-57.

8

  United Nations Standing Committee on Nutrition (UNSCN),  6th Report on the World Nutrition Situation: Progress in 

Nutrition (Geneva: UNSCN Secretariat, 2010).

9

  Bonnie A. Spear, “Adolescent Growth and Development,” Journal of the American Dietetic Association 201, no 3, 

supplement (2002): S23-29; Alan D. Rogol, Pamela A. Clark, 

and James N. Roemmich, “Growth and Pubertal Development 

in Children and Adolescents: Effects of Diet and Physical 

Activity,” The American Journal of Clinical Nutrition 72, no. 2 

(2000): 521S-28S; and FAO/WHO/UNU, Energy and Protein Requirements: Report of a Joint FAO/WHO/UNU Expert 

Consultation (Geneva, WHO, 2001).

10

  Cassandra M. Gibbs et al., “The Impact of Early Age at First Childbirth on Maternal and Infant Health,” Paediatric and 

Perinatal Epidemiology 26, no. S1 (2012): 259-84.

11

  National Population Commission of Nigeria and ICF International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013. 

12

  R.O. Abidoye and N.N. Ihebuzor, “Assessment of Nutritional Status Using Anthropometric Methods on 1-4 Year Old 

Children in an Urban Ghetto in Lagos, Nigeria,” Nutrition and Health 15, no.1 (2001): 29-39.

13

  Nigeria National Bureau of Statistics, United Nations Children’s Fund, and United Nations Population Fund, Nigeria Multiple 

Indicator Cluster Survey 2011 (Geneva: Unicef, 2013).

14

  National Population Commission of Nigeria and ICF International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013.

15

  National Population Commission of Nigeria and ORC Macro, Nigeria Demographic and Health Survey, 2003 (Calverton, 

MD: ORC Macro, 2004); National Population Commission 

of Nigeria and ICF Macro, Nigeria Demographic and Health 

Survey 2008 (Calverton, MD: ICF Macro, 2009); and National 

Population Commission of Nigeria and ICF International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013.

16

  National Population Commission of Nigeria and ICF International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013.

17  National Population Commission of Nigeria and ICF 

International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013. 

18  World Health Organization, “Essential Nutrition Actions, 2013,” 

accessed at www.who.int/elena/titles/complementary_feeding/

en/, on Nov. 10, 2014.

19

  National Population Commission of Nigeria and ICF Macro, Nigeria Demographic and Health Survey 2008. 

20

  Ghana Statistical Service, Ghana Health Service, and ICF Macro, Ghana Demographic and Health Survey 2008 

(Calverton, MD: ICF Macro, 2009).

21

  National Population Commission of Nigeria and ICF International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013.

22

  Adom B. Ghartey, Nutrition Policy and Programs in Ghana: The Limitation of a Single Sector Approach (Washington, DC: 

The International Bank for Reconstruction and Development/

The World Bank, 2011).

23

  Richmond Nii Okai Aryeetey and Comfort Liousa Antwi, “Re-assessment of Selected Baby-Friendly Maternity Facilities in 

Accra, Ghana,” International Breastfeeding Journal 8, no. 15 

(2013), doi: 10.1186/1746-4358-8-15.

24

  Anthony Mwinilanaa Tampah-Naah and Akwasi Kumi-Kyereme, “Determinants of Exclusive Breastfeeding Among Mothers in 

Ghana: A Cross-Sectional Study,” International Breastfeeding Journal 8, no. 13 (2013), doi: 10.1186/1746-4358-8-13.

25

  Tampah-Naah and Kumi-Kyereme, “Determinants of Exclusive Breastfeeding Among Mothers in Ghana”; and V.J. Quinn et 

al., “Improving Breastfeeding Practices on a Broad Scale at 

the Community Level: Success Stories From Africa and Latin 

America,” Journal of Human Lactation: Official Journal of the International Lactation Consultant Association 21, no. 3 (2005): 

345-54.


26

  Scaling Up Nutrition, A Framework for Action (Washington, DC: 

BMGF, the Government of Japan, and the World Bank, 2010), 

accessed at www.unscn.org/files/Announcements/Scaling_

Up_Nutrition-A_Framework_for_ Action.pdf, on May 10, 2014.

27

  World Bank, Repositioning Nutrition as Central to Development: A Strategy for Large-Scale Action (Washington, 

DC: World Bank, 2006).

28

  Sue Horton and Richard H. Steckel, “Malnutrition: Global Economic Losses Attributable to Malnutrition 1900-2000 and 

Projections to 2050,” in How Much Have Global Problems Cost the World? A Scorecard from 1900 to 2050, ed. Bjorn 

Lomborg (Cambridge, UK: Cambridge University Press, 2013).

29

  John Hoddinott et al., “The Economic Rationale for Investing in Stunting Reduction,” Maternal & Child Nutrition 9, no. S2 

(2013): 69-82.


Dostları ilə paylaş:


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©genderi.org 2019
rəhbərliyinə müraciət

    Ana səhifə