Bilal dan rabaha yadda musulunci ya yaki kabilanci da banbancin launin fata a tsakanin mabiyansa



Yüklə 154,45 Kb.
səhifə2/2
tarix23.01.2018
ölçüsü154,45 Kb.
#21983
1   2

A KARSHEN ZANCEN:

Ka fadamun gaskiya tsakanin ka da Allah ina girman kai ko jiji daka ka nuna isa da iko da za'ace wannan addini ya cusa a zukatan mabiyan sa? Hakika addinin musulunci wani irin muryan gaskiya ne wanda yake haduwa da zuciya sai ya wanzar ma mutum kusanci da dogaro ga Allah madaukaki, mai kaskantar da kai gareshi wanda hakan zai sa ya manta dukkanin wani radadi da kunci wanda ya sameshi sakamakon bin wannan tafarki, da kuma sanya shi yana mai jin dadin rayuwa da halin da yake ciki kamar wanda masu bin son zuciyarsu irin dadin da sukeji a lokacin da suke aikata son zuciyar nan nasu sai dai kasha tir da son zuciya da sha'awa wanda zai gadar ma mutum nadama da asara daga baya, sabanin mabiya addinin musulunci sahu da kafa su farin cikin da sukeji na rayuwa gadar masu da dawwama zayyi cikin ni'ima saboda sun zabi hanya sahihiya wanda yakaisu inda suka samu kansu aciki na tsira wanda suka samu ta wurin Allah. Lallai samun kaiwa zuwa inda suka kai na tsira bada zufan gushi ake samun sa ba kawai abunda yake bukata shine jarumtaka da jura akan canjin rayuwan da mutum zai hadu dashi, hakika sun sani cewa hanyar da akebi wurin samun Aljanna itace bin wannaan Manzon wanda ba'a taba samunshi da karya ba ko yaudara ko zamba, dan sayrara kaji maganan daya daga cikinsu da yayi kafin ya shiga musulunci, wannan mutumi kuwa bakowa bane illa Abu sufyan dan Harbi, yadda yake cewa: lallai sarki Hirkal ya aiko da wasu mutane zuwa ga Abu sufyan alokacin suna tawagar yan kasuwar kuraishawa da sukaje kasar sham fatauci a tsakayan lokacin da manzon Allah s.a.w yayi sulhu da Abu sufyan da arnan kuraishawa akan zaman lafiya na wasu shekaru, sun iske shi a wurin akwai Iliya'u', sai sarki Hirkal ya kirasu cikin fadarsa a kewaye dashi akwai manya manyan rumawa sannan ya kira masu masa fassara sai yace masu: cikin ku wanene yafi kusanci na dangantaka da wannan mutumin wanda yake kiran cewa shi manzo ne? sai Abu sufyan yace masa nine nafisu dangantaka dashi, sai sarki Hirkal yace ku kusanto min dashi nan kusa dani, sai yace ku saurara kuji zan tambayi wannan mutumin akan wannan mutum mai ikirarin annabta idan ka fadamun karya ku sauran da kuke wurin ku karya tashi, sai Abu sufyan yace ina rantsuwa da Allah badan kada a rawaito karya ba daga gareni dana masa karya, daganan ya fara tambayata farkon tambayansa it ace: ya danganta kansa yake acikinku? Ya fito ne daga babban gida ko kuwa ya fito ne daga gidan talakawa, sai Abu sufyan yace masa ya fito ne daga babban gida, sai sarki Hirkal yace: shin wani mutum acikinku ya taba yin irin wannan ikirari nasa kafin sa? Sai Abu sufyan yace: a'a ba'a taba samu ba, sai sarki Hirkal ya kara tambaya cewa: shin an taba samun sarki cikin iyayensa? Sai Abu sufyan yace a'a ba'a taba samu ba, sai sarki Hirkal yaciga ba da tambaya cewa: shin mabiyansa da yake dashi manya mutane ne ko kuma talakawa? Sai Abu sufyan yace: talakawa ne, sai Hirkal yace: to kara yawa sukeyi ko kuma raguwa sukeyi? Sai Abu sufyan yace: inafa ranka ya dade ai kara yawa sukeyi, sai Hirkal yacigaba da tambaya cewa: shin kun taba ganin wanda yayi ridda bayan ya musulunta saboda kinsa da yakeyi da kuma rashin yarda dashi? S Abu sufyan yace: a'a bamu taba gani ba, sai sarki Hirkal yace: to kun taba tuhumarsa da wani karya fadin yafara wannan ikirari nasa? Sai Abu sufyan yace: a'a bamu tab aba, sai Kirkal yace: to yana yaudara? Sai abu sufyan yace: a'a baya yaudara yanzu haka ma muna cikin wani alkawari da muka kulla dashi sai dai bamusan me zai aikata ba a cikinta, sai Abu sufyan yace bansamu damar da wata kalma ba sai wannan kalma cikin abun da yakeso namai Karin gishiri a miya, sai Hirkal yace: to kun taba yakansa? Sai Abu sufyan yace; eh mun taba, sai Hirkal yace: to ya yakin yakasance a tsakanin ku? Sai Abu sufyan yace: wani lokaci yaci nasara akammu wani lokaci mu rama muci nasara akansa, sai Hirkal yace: wai me yake umurtan ku dashi ne? sai Abu sufyan yace: yana umurtammu ne da mu bautawa shi kadai kada mu hadashi da kowa cikin Ibada, da kuma mu manta da abunda Iyayen mu suke cewa, sannan kuma yana umurtan mu damu tsai da salla da yin gaskiya da yafiya a tsakanin mu da sadar da zumunta, sai Hirkal yace ma masu masa fassara kuce masa na tambayeshi dangantakar wannan mutumi yace mun mutum ne me daraja acikin mu hakika haka ake aiko annabawa daga cikin kabila masu daraja a tsakanin mutanen sa, sannan na kuma tambayanka shin akwai wanda kuka tabaji yayi irin wannan ikirari nasa kafinshi sai kacemun: a'a ba'a taba samu ba, da kacemun an taba samun wani dayayi irin wannan ikirari nasa kafinsa dana ce lallai ya tasirantu ne da maganin da wani ya fada kafinsa, sannan na kara tambayanka shin an taba samun sarki cikin Iyayensa kacemu: ba'a taba samu ba, da kace mun an bata samu dana ce lallai yana neman sarautan babansa ne, sannan na tambayeka shin kun taba tuhumarsa da karya kafin wannan ikirari nasa kace mun: baku taba ba, anan nasan cewa babu yadda za'ayi yabar yima mutane karya ya koma yana yima Allah karya hakan bazai taba yiwuwa ba, sa'annan na tambaya ke manyan mutane ne suke binsa ko kuma talakawa sai kacemun: talakawa ne sue binsa, lallai manzanni talakawa ne suke binsu, nakara tambayanka shin raguwa sukeyi ko karauwa kacemun: karuwa sukeyi lallai haka al'amarin imani yake har sai ya cika, sannan na tambayeka kun taba ganin wani daga cikin mutanen sa yayi ridda bayan yayi imani dashi kace mun: baku taba gani ba lallai hakika haka al'amarin imani yake idan ya hadu da karbuwan zuciya, sannan na tambayeka yana yaudara kacemun: baya yaudara lallai haka Annabawa suke basa yaudara, kuma na tambayeka dame yake umurtan ku kacemun yana umurtan ku ne da bautawa shi kadai kada ku hadashi da wani cikin bauta sannan yana hanaku bautawa gumaka kuma yana umurtanku da sallah da gaskiya da yafiya a junanku lallai kuwa idan haka ya kasance kamar yadda ka fada tabbas zai mulki wurin wannan kafafuwan nawa guda biyu dinnan, hakika ina sane da cewa ya bayyana amma bansan cewa daga cikin ku zai fito ba, lallai da nasan zan hadu dashi da raina yaso haka koda kuwa zai wahalu wur[n hakan, da kuma nakansce a wurinsa da nine zan rika wanke masa kafafuwansa, daganan sai sarki Hirkal yace azo masa da wasikar da manzon Allah s.a.w ya aiko masa dashi abaya abude a karanta masa, sai aka kawo masa wannan wasika da aka bude sai akaga abun da ta kunsa cewa: ina farawa da sunan Allah me rahma me jin kai, sako daga Muhammad bawan Allah kuma manzon sa zuwa ga sarki Hirkal, sarki me daraja na rumawa, amincin Allah ya tabbata ga wanda yabi shiriya, bayan haka lallai ina me kiranka zuwa ga addinin musulunci, ka musulunta zaka tsira da samun aminci na dawwama a wuta, kuma Allah zai baka ladan ka sau biyu, idan kuma kakia musulunta ka sani zaka kwashi laifin Arisawa akanka" kace yaku wanda aka basu littafi kuzo zuwa ga wata kalma wacce zamu hadu akanta cewa bazamu bautawa kowa ba sai Allah, kuma bazamu masa shirk aba da kowa cikin bauta, kuma wasun mu bazasu rike wasu ba Alloli abun bauta koma bayan Allah, idan suka juya maku baya kuce masu kushaida lallai mu musulmai ne masu mika wuya ga Allah".

Sai Abu sufyan yace: lokacin da sarki Hirkal ya gama fadin abunda zai fada ya kuma gama karanta wannan wasika na manzon Allah daya aiko masa sai wurin ya kaure da hayaniya da cece kuce, sai muka fito daga wurin sai nace ma mutane na wanda muka shiga wurin dasu bayan mun fito hakika al'amarin dan baban Kabshata ya girmama((yana nufin Manzon Allah s.a.w)) saboda Abu kabshata sunan kakan manzon Allah ne su kuma a al'adan larabawa shine idan suka so kaskantar da mutum sai su jingina shi da sunan kakansa wanda ba'a be shahara ba.

Ibn kutaiba da Khaddabiyyu da Dara-khudniyyu sun ce game da 'baban kabshatu' shi mutum ne dan taware wanda ya sabawa kuraishawa daga bautan gumakan da sukeyi ya koma yana bautan tauraro sai suka mai inkiya da sunan mutum dan taware saboda saba masu da yayi wurin bauta. (littafin fathul bari ya kawo wannan Magana).

Lallai sarakunan rumawa sun kasance suna tsoronsa, ban gushe ba ina da yakinin cewa lallai tabbas zai bayyana har lokacin da Allah ya shigar mun da son musulunci a zuciya na, Dan nazur abokin Iliya'u da Hirkal ya kasance baban malamin kiristoci a kasar sham, ana cewa lokacin da Hirkal daya gabatar da Iliya'u ya kasance wani rana mai mugun zuciya, sai wasu daga cikin jagororin rundunar yakin rumawa suka ce masa: lallai mun kyamace halinka, Dan Nazur yace Hirkal ya kasance boka ne me amfani da taurari wata rana yace masu lokacin da aka tambayeshi: lallai da daddare lokacin dana kalli taurari na ga sarkin Kaciya ya bayyana, wa nene zayi kaciya cikin wannan al'ummar? Sai sukace babu wanda zayyi kaciya sai yahudawa kada al'amarinsu ya dame ka, ka tura mayaka a karkashin mulkin ka zuwa ga bira ne su kasha duk wani bayahude da suka samu, suna cikin wannan Magana kenan sai akazo ma Hirkal da wani mutum dan sako daga wurin sarkin gassan yazo ma Hirkal da labari game da manzon Allah s.a.w, da yagama bashi labarin sa sai Hirkal yace kuje ku duba ku gani yana da kaciya ko bashi dashi? Sai suka kawo mai labarin cewa yana da kaciya, sai kuma suka tambaye shi game da larabawa shin suna yin kaciya? Sai Hirkal yace wannan shine me mulkin wannan al'umma hakika ya bayyana, sai Hirkal ya rubuta takarda zuwa ga abokinsa a Ilimi, daganan hirkal ya tafi zuwa ga wurin hutawansa cikin fulawa, kafin ya zauna sai ga sako daga wurin abokinsa yana masa muwafaka akan ra'ayin sa na cewa Manzon Allah s.a.w ya bayyana kuma lallai shi annabi ne daga Allah, sai Hirkal yayi umurni ga manyan rumawa cewa su taru acikin gun shakatawar sa, bayan sun shigo sai yace a rufe masa kofofin wurin bayan an rufe sai ya tashi yace masu: yaku taron manya rumawa, shin kuna son rabauta da shiriya da dorewar mulkin ku? To lallai kubi wannan Annabi nan da nan suka tashi suka nufi kofa suna neman ficewa sai suka tarar da an rufe kofofin, yayin da Hirkal yaga yadda suke gudu ga yin imani da kuma debe tsammanin su dashi sai yace a dawo dasu wurinshi sai yace masu, lallai na fadi maganar da na fada dazun ne dan jaraba kwarin sonku da addini to kuma na gani, sai sukayi sujjada gareshi suka yarda da abunda yake fada masu, wannan itace ta zama karshen al'amarin Hirkal.



Salihu dan kaisan da yunus da mu’amar ne suka rawaito wannan labari daga Zuhri.54

../../../../../../../documents/my%20sites%20&%20projects/projects%20&%20sites/islaml

www.islamland.com

../../../../../../../documents/my%20sites%20&%20projects/projects%20&%20sites/islamland/profil



1 Duba cikin littafin musnadi na Imamu Ahmad, mujalladi na biyu, shafi na 361, hadisi lamba na 8721, da kuma cikin littafin sahih wattargib hadisi lamba 2963.

2 Duba cikin littafin siyasa na Aristo

3 Suratu al'imran ayata 75

4 Suratul ma'ida ayata 18

5 Duba cikin littafin mustadrak akan sihihaini, mujalladi na 4, shafi na 437

6 Duba cikin littafin sahihu muslim, mujalladi na 4, shafi na 2222

7 Suratun nisa'I ayata 1

8 Suratu al'imran ayata 59

9 Suratun rum ayata 20

10 Duba cikin littafin musnad na Imamu Ahmad, mujalladi na 2, shafi na 361, lamban hadisi na 8721, da kuma littafin sahihul jami'u lamba na 5482

11 Suratu yunus ayata 19

12 Suratun nahli ayata 36

13 Duba cikin littafin mustadrak akan sahihaini, mujalladi na 4, shafi na 364

14 Duba cikin littafin sahihi na ibn hibban, mujalladi na 14, shafi na 29, lamban hadisi na 6160

15 Suratul hujurat ayata 13

16 Suratul isra'I ayata 70

17 Suratul an'aam ayata 165

18 Suratu zukhruf ayata 32

19 Duba cikin littafi musnad na Imamu Ahmad, mujalladi na 2, shafi na 361, lamban hadisi na 8721, da kuma lttafin sahit targib wattarhib lamban hadisi na 2963

20 Suratun nisa'I ayata 58

21 Muslim ne ya rawaito hadisin

22 Suratul zilzilat ayata 7-8

23 Suratul an'am ayata 108

24 Duba cikin littafin sahihul bukhari, mujalladi na 1, shafi na 37

25 Duba cikin littafin sahihi na dan Hibban, mujalladi na 11, shafi na 469

26 Suratul bakara ayata 168

27 Suratul bakara ayata 21

29 Duba cikin littafin sahihun nisa'I da Ibn majjah

30 Suratul masad ayata 1-3

31 Duba cikin littafin silsilatus sahiha lamaban hadisi na 3190

32 Duba cikin littafin silsilatus sahihah lambar hadisi na 3044

33 Duba cikin littafin sahihul bukhari, mujalladi na 1, shafi na 466

34 Bukari ne ya rawaito hadisin

35 Imumu Ahmad ne ya rawaito hadisin, wanda sheikh shu'aibu yace hadisin sahihi ne ta wani hanya

36 Duba cikin littafin sahihu muslim

37 Hadisi ne Hasan, duka cikin littafin mishkat lamban hadisi na 6167

38 Bukahri da muslim sun rawaito hadisin

39 Bukhari ne ya rawaito hadisin

40 Bukhari ne ya rawaito hadisin

41 Duba cikin littafin mustadrak akan sahihaini, mujalladi na 3, shafi na 551, da kuma littafin sahihul jami'u lamban hadisi na 2294

42 Duba cikin littafin sahihul buhari

43 Tarihin dimashk na Ibn Asakir

44 Tarihin dimashk na Ibn Asakir

45 Duba cikin littafin sihuhul buhari

46 Wahayi yana saukan ma Manzon Allah s.a.w ta hanyan mala'ika Jibril wanda shine mala'ika me saukar da wahayi yana zuwa mai ne a siffofi daban daban kamar yadda manzon allah ya bada labara daga ciki akwai 1- yana zuwa mai ne a siffan mutum sai ya fada masa baki da baki 2- yana zuwa mai kamar karanr kararrawa wanda wannan fissan yafi masa tsanani

47 Suratul an'am ayata 52-54

48 Ibn majjah ne ya rawaito hadisin a takaice, Albani yace hadisi ne ingantacce

49 Duba cikin littafin rijalu haularrasul

50 Duba cikin littanin sahihu ibn hibban, mujalladi na 15, shafi na 558

51 Imamun tirmizi ne ya rawaito hadisin, Albani kuma ya ingantashi

52 Duba cikin littafin sahihul bukhari

54 Duba cikin littafin sahihul bukhari






Yüklə 154,45 Kb.

Dostları ilə paylaş:
1   2




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©genderi.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

    Ana səhifə