DW, Ji Ka Ƙaru. Bari na ba ku labari. Na biyar: Akawal da Kili.
1/7
DEUTSCHE WELLE
JI KA ƘARU
Almara a Afirka domin al’adu da zaman lafiya:
Bari na ba ku labari
Na biyar: Akawal da Kili
Wanda ya rubuta:
Ibrahima Ndiaye
Waɗanda suka tace:
Yann Durand, Stefanie Duckstein, Naïma Guira
Wanda ya fassara:
Ɗanlami Bala Gwammaja
’Yan wasa:
Mai ba da labari
Sarki Gadamurƙi
Gado
Akawal
Kili
Masu gadi
DW, Ji Ka Ƙaru. Bari na ba ku labari. Na biyar: Akawal da Kili.
2/7
MAI GABATARWA:
Jama’a muna yi muku maraba da zuwa kashi na biyar a cikin shirinmu na “Ji
Ka Ƙaru” mai taken “Bari Na Ba Ku Labari”. Shi wannan shiri ne a kan
hikayoyin Afirka masu koya zamantakewa tsakanin al’umma. To, ina zaton
kun taɓa samun kanku a wani yanayi da wani ya so ya cusa muku ra’ayi ku yi
wani abu, duk da cewa kuna ganin abin nan bai dace ba. Idan kuma aka yi
rashin sa’a, wanda yake ƙoƙarin cusa muku wannan ra’ayi mutum ne mai
ƙima, ko wanda kuke so, to fa da wuya a baɗa masa ƙasa a ido. Amma wani
lokacin fa sai an juya musu baya kamar yadda za ku ji. Ku biyo mu domin ku
ji yadda ƙauna ta ’yan’uwantaka ta daƙile maitar wani sarkin yaƙi a cikin
labarinmu na yau mai suna “Akawal da Kili”.
MAI BA DA LABARI:
A wannan rana kuwa ana tsananin zafi, amma iska na busawa kamar
ana fifita da mafici.
An taɓa yin wata ƙasaitacciyar daula mai suna Barade a wani wuri
mai bishiyoyi. A duk lokacin da rana ta hudo, wannan wurin yakan
zamo gwanin ban sha’awa saboda irin haskaka wajen da rana kan yi.
Sarkin wannan daula kuwa wani irin mutum ne mai kwarjini, kuma
ana shakkarsa. Sunansa Gadamurƙi Rana Mudun Aiki. Wannan suna
nasa, wato Rana Mudun Aiki, na nufin rana mai raba wa kowa aiki.
Kowa ya san sarkin nan da halin ba-sani-ba-sabo, kuma yana
tabbatar da hakan a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.
Sarki Gadamurƙi mutum ne mai tsanani son dawakai.
Ba abin da
yake gabansa illa dawakai. Ba inda ba za shi ba don ganin ya samo
irin dawakan waɗanda ba a cika samunsu ba a yankin.
Ana nan wata rana sai Sarki Gadamurƙi ya sami labarin daular
Maraya. Sarkin wannan daular mai suna Dumare yana da dawakai
waɗanda duk shekara sai sun haifa masa kyawawan dawakai. A wata
shekara, sai aka haifa masa wasu kyawawan dawakai guda biyu.
Ɗayan baƙi ne wuluk mai suna Akawal, ɗayan kuma fari ne sal mai
suna Kili. Waɗannan dawakai sun taso tare kuma ba sa rabuwa, har
DW, Ji Ka Ƙaru. Bari na ba ku labari. Na biyar: Akawal da Kili.
3/7
ake kiransu da “kashin awaki”.
Sarki Gadamurƙi na samun wannan labari, sai fa ya kasa tsaye ya
kasa zaune. Wata rana sai ya kira wasu daga cikin barorinsa ya ce da
su:
SARKI GADAMURƘI:
“Kai, ku ɗaura min sirdi. Ina son na gana da Dumare da gaggawa. Ina
so na mallaki kyawawan dawakan nan nasa. Dole ne ya ba ni su!
Maza ku hanzarta!”
MASU GADI:
“An gama, ranka ya daɗe!”
MAI BA DA LABARI:
Nan da nan barorin nan suka bazama don su cika aiki. Amma fa
Sarki Dumare ba ya son rabuwa da kyawawan dawakan nan nasa
guda biyu. Bayan an sha fama, da ƙyar Sarki Dumare ya yarda ya
sayar wa da Sarki Gadamurƙi ɗaya daga cikin waɗannan dawakai da
yake ciwon so, wato Kili, amma ba da son ransa ba, sannan kuma sai
da ya yi nadamar hakan.
Duk da cewa Sarki Gadamurƙi ya samu ya mallaki Kili, amma bai
haƙura ba, sai kuma ya ƙwallafa ransa a kan Akawal. Shi kuwa Sarki
Dumare sai ya tsaya kai da fata ba ya son ya rabu da shi. Wannan
mataki ya ɓata wa Sarki Gadamurƙi rai, don kuwa yana ganin an
kawo masa raini. Saboda haka, sai ya kai wa Dumare hari.
Sarki Gadamurƙi ya tsara yadda zai tunkari yaƙin nan a nutse. Sai ya
hau dokin da ya fi ji da shi a filin daga, wato Kili, bayan an yi masa
cikakken shiri. Sannan kuma manyan dakarunsa na kewaye da shi.
Shi ma Sarki Dumare ya hau Akawal, wanda shi ma da shi ya fi ji,
suka kuma tunkari abokan karawa. Daga nan kuma sai yaƙi ya ɓarke
tsakaninsu a wani fili wanda ba shi da ciyayi sosai.
An tabka ƙazamin faɗa. Mayaƙan ƙasa na Sarki Gadamurƙi wanda ya
hawo Kili sun kewaye shi. Waɗannan mayaƙa sai farmaki suke kai wa
DW, Ji Ka Ƙaru. Bari na ba ku labari. Na biyar: Akawal da Kili.
4/7
abokan faɗansu, waɗanda su kuma Sarki Dumare ke jagorantarsu,
kuma yana haye a kan Akawal. Makaman mayaƙan Sarki Gadamurƙi
da na Dumare sai aman wuta kawai suke yi, sannan mayaƙan na yi
wa juna ruwa kibau, waɗanda aka tsima tsininsu a ruwan dafi. Ba
abin da ake ji sai ƙarar bindigu da haniniyar dawakai da karajin
mazaje, tsananin hargowar yaƙin ta sa ko kunne ba a ji. Haka aka ci
gaba da yaƙi na tsawon lokaci, duk kuwa da asarar rayuka da
kowanne ɓangare ke yi.
Bayan an yi kwananki ana fafatawa sai Sarki Gadamurƙi, wanda har
yanzu yana kan Kili, ya yi wa Sarki Dumare wani jawabi, yayin da shi
kuwa yana kan Akawal:
SARKI GADAMURƘI:
“Kai Dumare, in ba ka ba ni Akawal ba, to zan raba ka da ranka. Don
me ya sa ka ƙi bin umarnina, a matsayina na Sarkin Barade?”
MAI BA DA LABARI:
A wannan lokaci ne Akawal da Kili suka yi ido biyu da juna. suka
kuwa ƙura wa juna ido, kowannensu idonsa ya yi ja wur. Ba wani
daga cikin dawakan nan da iya tuna cewa wuri ɗaya aka haife su,
kuma suka taso tare. Taurin kai irin na iyayen gidansu ya yi tasiri a
kansu, don haka ba su damu da kawunannsu ba, sai kawai dawakan
nan suka tunkari juna, kowanensu yana hura hanci, sai kumfar baki
suke yi. Da farko sai da suka kewaya juna, sannan kwatsam, sai suka
far ma juna kamar maƙiyan da ba sa ga maciji
.
Sai harba kofatansu suka yi ta yi ta ko’ina. Kowane daga Sarakan nan
biyu ya kasa shawo kan dokinsa, don haka wannan hatsaniyar
dawakan sai ta sa aka yi watsi da su cikin taɓon filin daga. Amma
duk da haka, Akawal da Kili sai suka ci gaba da gwabzawa. Suka yi
jina-jina, amma ba wanda ya nuna ya karaya. In sun gaji sai su
dakata su ɗan huta. Amma suna hutawa sai su ci gaba da fafatawa
ba ko gajiyawa. Ina ma a ce za su tuna yadda suka taso a barga
ɗaya, da kuma yadda suke wasan tsere a daji suna raha!
DW, Ji Ka Ƙaru. Bari na ba ku labari. Na biyar: Akawal da Kili.
5/7
Sai dai ina, ba abin da zai sa su daina faɗan nan. Idanunsu ya rufe da
fushi da ƙiyayyar juna. Haka suka yi ta gwabzawa har gajiya ta cin
musu, suka faɗi rigija a ƙasa, kamar an sare reshen bishiyar kuka da
gatari. Sai ga su a kwance ba zato ba tsammani, wannan na kan
wannan a galabaice. Haka suka yi wanwar, ko motsi ba sa iya yi,
barci ya kwashe su suna cikin halin matsananciyar gajiya, kai ka ce
ban da yaƙi ba abin da suka sani.
Da asuba, lokacin nan kuwa dawakan nan na ta sharar bacci, sai ga
wani Gado ya zo zai wuce. Sai ya hau kan wata bishiyar kuka don ya
gane wa idonsa abin da ya razana shi tun daga nesa. Sai kuwa ya ga
ba abin da yake filin nan sai gawarwakin ɗan Adam fululu da na
dabbobi. Filin dagar kuma cike yake da kibau da albarusai da jini
face-face ko’ina.
Wannan Gado yana son ya san me ya jawo irin wannan ɗanyen aiki,
saboda haka sai ya yanke shawarar tashin dawakan nan guda biyu da
suka galabaita.
GADO:
“To, ai ya kamata kuma ku tashi ku yi mini bayani, me ya faru haka?
Mene ne dalilin wannan ta’addancin?”
AKAWAL & KILI:
“Iyayen gidanmu ne suka ɗaura yaƙi. … Mu kuma muka taya su.”
GADO:
“Kai ku dakata don Allah! Me ya sa kuka cusa kanku a faɗa tsakanin
bil’adama? Ba sai ku rabu da su su kashe kansu ba, tun da ba su da
hankalin da za su yi haƙuri su mori rayuwa! Ku kuma me ya sa kuka
rasa abin yi sai cutar da junanku?”
KILI:
“Wannan gaskiya kika faɗa. Mu dai mun bi umarnin shugabanninmu
ne kawai! Kin san mu ai ba a tata mu.”
DW, Ji Ka Ƙaru. Bari na ba ku labari. Na biyar: Akawal da Kili.
6/7
GADO:
“Wannan ai hauka ne! Za ni ce ta tad da mu je mu! Yanzu in
shugabanninku suka ce ku faɗa wuta sai ku faɗa? Ba kwa tunani ne?
Ai duk da cewa shugabanninku ne, ba kome suka ce ku yi za ku yi
ba! Wannan ai abin kunya ne. Ga ku kyawawa, ba mamaki ma ku
zama abokan juna.
MAI BA DA LABARI:
Daga wannan bayani, sai dawakan nan suka kalli juna suka kuma
sunkuyar da kai, saboda kunyar ganin yadda suka ji wa juna rauni.
Bayan sun ƙura wa juna ido na tsawon lokaci sai Akawal, wanda
idonsa ya yi jaja wur da alamar nadama, ya ce da farin dokin:
AKAWAL:
“Ba kai ne Kili ba?”
KILI:
“Kai kuma ba kai ne Akawal ba?”
MAI BA DA LABARI:
Daga ƙarshe sai suka gane juna! Sai suka girgiza kawunannsu a
ruɗe. Da ka gan su, ka san irin halin da suke ciki na damuwa. Sun
daɗe ba su ga juna ba! Wannan sai ya sa Gado ya ji daɗi, kuma ya ce
a ransa:
GADO:
“Ah, abin ya yi, kamar da wasa! Daga yanzu ya kamata na zama wani
ƙwararren mai ba da shawara fa. Mutane fa sai ka ga sun ƙi gaskiya
da gangan. Wannan al’amari ne babba, mai kuma lada. …
To, da ma kun san juna ashe! Kili! Akawal! Ni zan tafi. Ina da aiki a
gabana. Ina kuma yi muku fatan alheri.”
DW, Ji Ka Ƙaru. Bari na ba ku labari. Na biyar: Akawal da Kili.
7/7
MAI BA DA LABARI:
Akawal ne ya fara magana bayan Gado nan ya tafi:
AKAWAL:
“Kili, idonsu ya rufe! Bai kamata mu tsoma kanmu a wannan
hatsaniyar ba. Ba abin da ya fi yaƙi muni. Dubi halin da muka samu
kanmu a ciki yanzu fa!”
KILI:
“Gaskiyarka, Akawal. Mu tafi. Daga yau, ba abin da zai sake raba
mu.”
MAI BA DA LABARI:
Da wannan, sai Akawal da Kili suka tafi abinsu, suka kuma zauna
tare har mai rabawa ta raba su. Har hazar yau ma, za ka gan su tare!
Hikayar tamu ke nan. Duk wanda bai ji bari ba, ya ji hoho!
MAI GABATARWA:
Ba mamaki ku ma kun taɓa samun kanku a wani yanayin da ake ba ku umarni
ku yi wani abu da bai kamata ku yi ba. Kun taɓa yi kuwa? Idan kun taɓa yi,
kada ku ɓoye, ku magantu! Ku faɗa wa abokanku, ko kuma ku rubuto mana
ta adireshinmu na yanar gizo, wato www.dw–world.de/lbe domin muna so
mu ma mu ji. Ibrahim Ndiaye ya rubuta wannan hikaya.
Dostları ilə paylaş: |