Karban shawara daga wurin allah "Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya gama su za su ga Allah." Daga


NASARA TA WURIN MUTUWA DA TASHIWAN



Yüklə 361,5 Kb.
səhifə10/11
tarix17.09.2018
ölçüsü361,5 Kb.
#68717
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11

NASARA TA WURIN

MUTUWA DA TASHIWAN

MATATTU

Akwai wata farne ta rayuwarka wanda zunubi ta sha kawo maka hari wanda kuma har yanzu ba ka sami nasara cikakke ba? Kana jin alhaki idan an yi magana akan, “mika kai,” “tsarki,” da kuma “kin kai” a zucaiyarka? Ko ka taba mika kanka ga Alla domin ka zama hadaya mai rai amma. ka kasa? Ko kana ji kamar wannan zance ta samun yanc daga zunub wanda ake fada a bishara banza ce? Ko zuciyarka na maimaita wannan zance ta manzo Bulus mai cewa, “Kaitona, ga ni mutum, abin tausai! Wanene za ya tsamo ni daga chikin jikin nan na mutuwa? (Romawa 7: 24)?”

“Na gode wa Allah ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu ! (Romawa 7: 25).” Akwai hanya to kubuta ! Alkawali ta kalmar Allah ta na da gaskiua a kulium. Yanci daga zunubi da rayuwa ta tsarki ta na nan a yalwace domin kowane da na Allah. Amma akwai hanya daya tal domin samunsa. A tsaye a tsakiyar dukan zance ta Bishara, bisa kowane irin koyasuwa da bangaskiyia, akwai gicije. Mutuwan Yesu, mai tsarki, Dan Allah mara aibi, A kan giciye,ta biya dukan bashi ta alhakin zunubi har ta kuma kubutar da mu daga mutuwa ta har abada. Wannan ita ne hanye daya kadai.

Muna nan tare da shi a wannan ranar. An giciye mu tare da Kristi (Galantiyawa 2 : 20). Mun mutu kuma ranmu tana nan a boye cikin Kristi a cikin Allah kuma (Kolossiyawa 3 : 3). Da muka sa Yesu ya zama Ubangijin rayukanmu, a takaice dai, an Karfafa ra’ ayinmu kena. Agaban Allah dai an rigaya an yi an gama Amma har wa you dai akwai wannan yaki cikin jikinmu. “Gama nagarta da ni ke so in yi, ba na aikawa ba: amma mugunta da ba na so ba, ita ni ke aikawa (Romawa 7 : 19).” Idan na nutu da gaskiy, to me za ta sa ina yin abu kamar mai rai?

Akwai wata giciye na kanmu wadde dole ne mu dauka a kowace rana (Luka 9 : 23). Dole ne mu koyi cewa mu mum mutu ga zunubi, amma a cikii Kristi Yesu muna nan da rai ga Allah (Romawa 6 : 11). Wannan abu ne mai muhimmanaci kwarai, ko da shi ke mutuwa a kan gicije ga dukan kwadayi ta ranmu tana da muhimmanci kwarai, amma ba wannan ce karshen bidanmu ba. Mutuwa kofa ce kurum, hanga ce zuma wurin da mu ke nufa. Babban mnufan Kristanci ita ne mu yi rayuwa irin ta tashiwan matattu, daga yanzu har zuwa rai ta har abada. Muna da wannan bege mai daukaka ta tashiwan matattu wanda jikin mu za ta yi, domin wannan bege ba za mu ji tsoron mutuwa ba ko cikin makoki da kuma cikin bacin rai. A ta haka ma, muna da bege ta tashiwan jiki daga matattu domin ta karfafamu cikin mutuwan tsohon ranmu, wato jiki ta zunubi (Romawa 6 : 6).

“Amma idan muka mutu tare da Kristi, mun bada gaskiya za mu kuma rayu tare da shi ….. Gama mutuwa da ya mutu, ya mutu ga zunubi so daya : amma rai da ya ke rayuwa, yana rayuwa ga Allah. Hakanan ku kuma ku maida kanku matattu ne ga zunubi, amma rayayyu ga Allah chikin Kristi Yesu. Kada Zunubi fa ya yi mulki chikin jikik mai – mutuwa, da za ku biue ma sha’awoyinsa: Kuma kada ku bada gababuwa naku ga zunubi alatun aikin rashin adilchi: amma ku mika kanku ga Allah, watau masu – rai daga chikin matattu, gababuwa naku kuma alatun adilchi zuwa ga Allah (Romawa 6: 8-13).

Mutuwa tawa da Kristi abu ce ta ainihi sosai. Aiki na a wannan mutuwa ta kullum ita ne in riga tuna da wannan gaskiya, in kuma yarda cewa haka ta ke, in kuma kira wannan ta tsiro cikin harkar rayuwata. Idan na dubi Maganar Allah, ba na sake ganin Doka tana yi mani Sharia. A maimakon haka, ina ganin Yesu yana cika umurnin Doka a rayuwarsa na duniya da kuma ta hannuna. Ba na kokari in aikata umurnin Doka ta wurin giciue kaina (jikina), amma ina imani da cewa an rigaya an giciye ko. Ba na tashiwa domin in yi yaki da kwadayi ta jiki mai jarabce ni domin in yi zunubi. Amma sai in juya idanuna daga wurin kwadayi ta jiki zuwa ga gaskuya wanda ta bayana mani cewa ina raue da tufa ta Kristi, dukan yalwatar rayuwarsa tana nan a cikina, kuma zunubi ba ta da iko a kaina yanzu kuma ina da yanci in yi rayuwa ta tsarki. Kuma kamar yadda, “..Mu dukanmu, da fuska ba lulubi muna juya darajar Ubangiji kamar madubi, muna sakuwa zuwa chikin wannan sura daga daraja zuwa darja, kamar dai daga wurin Ruhun, watau Ubangiji (Korinthiyawa 2, 3 : 18). Idan na sa rai na ga irin jikina ta zunubi da kuma irin ikon da zunubi ta ke da shi a yanzu a kan raina, babu wuya in fidda rai.Amma, idan na kafa ido ga Ruhu da kuma ikonsa na tashiwan matattu wanda ke aiki a cikina, mai ba ni karfi in ci nasara ga magabci, babu wuya sai in sami rai da kuma salama (Romawa 8 : 6).

Ta yaya ne zan aikata wadan nan darasai din a rayuwata ta yau da kullum? Idan jaraba ta abko mani, ta yaya zan gane cewa ni na mutu ga zunubi kuma ina nan da rai ga Kristi? A misali a ce, wani abokina wanda na yarda da shi sosai ya ci amana ta. Abin yi ta farko ita ne in ji zafi, kuma in nuna wannan ta wurin fushi da kuma neman hanya in rama . kuma neman hanya in rama. Wannan tsohon jikina ne na aikinsa. Duk wannaba ta kai zunubi ba tukuna, jaraba ce ta abko mani da karfi. A wannan lokaci, ba zan bude baki ko in yi wani abu ba, domin idan na yi, zan aikata zunubi domin ina barain jikina ta yi magana. A maimakon wannan zan juya hankalina zuwa ciki, zuwa ga Kristi wanda ke rayuwa a cikina. Zan tuna wa kaina cewa na mutu zuwa ga aikata abu na son raina. Ko da shi ke suna jarabta na, amma ba su da iko su tilasata ni in yi biyayya a garesu. Zan zura wa Kristi ido, wanda shi ne raina, da wannan addu’a “ Ubangiji, ina jin zafi, bacin rai da kuma fushi. Ba ni da iko in gafarta. Amma kai Ubangiji, kai ne kauna. Mai zuba a yawalce na rai madawwami a cikina. Ka yi cikin gafara a cikin mugun zafi da konar zuciya. Ka zama dukan abin da na ke bukata. Cika ni da kaunarka, aikin gafaranka, ganewarka da kuma tausayinka. Ka cinyeda alherinka duk wadanda za su tashi domin yin gaba da ni.” Wasu lokaci a hankali, ko kuma a nan da nan, za ka ji saki daga wannan kunar rai da fushi, wanda ke tasowa daga wurin Ruhu na Kristi. Bayan dukan amsa ta jiki ta kwanta a gaban Yesu, sai in ba abokina amsa irin wanda ta gamshi hal na Kristi. Zan iya zama manzo na sulhu da kuma mai kawo sako ta salama.

Zam iya maimaita wannan a cikin rabin miniti, ko mintuna, ko awanne ko kuma watanne ko ma cikin shekaru. Amma idan na so in manne wa ciwon rai nawa in kuma lallashe su, to lalle zan bi harka ta jiki kenan. Idan kuma na zura ido ga jaraba da irin ikon da ta ke da shi a bisa kai na yanzu, kuma ina yakan jaraba ta hannun nama da jini to, lalle zan kasa sosai. Amma kuwa idan na yi tsit a gaban Allah, na kuma furta masa bukatuna da kuna kasawate, kuma na ba shi dama ya amsa mani da kalmarse ta alheri da kuma wahayinsa na nasara, nan da nan zan yi nasara. Nawa amsa ga yan - ayi ta rayuwa ita ne in bi ta hanyar mutuwa zuwa tashin matattu. Nawa sa rai ita ne in yi amfani da wannan mataki ta karshe, wato in tsaya cikin salama a yayin da Yesu yana aiki ta wurin rayuwata.

Akwai sashi har gida uku wanda ni Krista zan iya aiki da ita. Zan iya sa ido ga sonkai,wadda ke da rai, wannan tana nan kamar rayuwa ta mara – bi kenan. Idan jaraba ta kawo mani hari, sai in yarda mata ba tare da wata wata ba. Watakila in bada gaskiya ga karya game da zunubi, wai idan na fara bin so na jiki, na yi zunubi kenan, domin haka, tun da na rigaya na fadi bari in karasa sauran cikin kurunm. Amma kuma, zunubi ba ta farawa sai dai idan na aikata abin nema na kaina. Idan na ci gaba da wannan irin tunani zan yi rayuwata cikin kokari ta kaina, na kunar zurciya, de fushi, da ramako da kuma son bin ra’ayi ta kaina. Zan ciku da hali ta jiran sammani, da tsoro da kuma rashin sa hankali guri daya.

Na biyu kuma, ita ne in zura ido ga kaina, wanda ta mutu. Zan yi kokari in tura duk harka ta zunubi daga rayuwata ta wurin kokarina. Zan zama kamar doli na addini, mai sha’ ani ba daga kaina ba ko kuma ta wurin Kristi. Zan zama mara auki, mai yawan gajiya don rashin aiki da kuma mai yawan nace wa harka ta addini: Ba za a gan ni da lafiyar hali ta mutuntaka ba, kuma ba zan sami fili domin nishadi ba, balle ma na jin dadin halitar Allah ko kuma farinciki. Rayuwata za ta kafu kan abu daya kurum, wata harka ta aikin addini.

A sarari dai, ba zan goyi bayan ka yi aiki da wadannan hanyoyi biyun nan ba. A maimakon wannan zan yi amfani da wata hanya dabam, wato hanya ta barin Krist ya yi rayuwarsa a cikina. Ko da shi ke na rigaya na bada gaskiya cewa an giciye ni kuma kaina na da ta mutu, amma ina kuma da sane cewa an tada ni daga matattu tare da Kristi domin wannan ina nan da rai ta wurin iko na tadawar matattu. Idan na ga wata harka ta duhu a rayuwata, sai in kore ta ta wurin haska haske na Kristi, ta wurin kawo fuska nasa zuwa aikin zancen. Domin haka sai rayuwa irin ta Yesu za ta soma bayyana a nawa rayuwa. Sai in zama mutum mai nuna kauna, da kula, cike kuma da bangaskiya, mai nagarta, mai hikima da kuma yanci. Domin na sami warkasuwa na raunukana, ni za a iya mora domin kawa wa wasu warkasuwa a cikin wehalarsu. Hali ta Kristi za ta bullo a rayuwata ta wurin ‘ya’ ya na Ruhu Mai Tsaki. Iko ta Kristi za ta fito ta wurin baiwa ta Ruhu Mai Tsaki.

Giciye kwadayi ta jiki ba abu mai sauki ba ne, ba kuma harka ta nishadi ba. Kada kowa ya yi sammani cewa hidima ta mika kai da tsarki abu ne wanda za a iya daukanta a cikin sannu. Akwai zafi da kuma wahala. Amma idan za mu jimre wa giciye, za mu sami farin ciki da kuma kubuta daga dauri na zunubi a yadda ba mu taba yin zato ba.

Asalin dalilin zuwan Yesu a nan duniya ita ne domin ya mutu a kan giciye. Kafin ya fara aikinsa, ya yi azumi na kwana 40 ya kuma sami karfi domin ya ci nasara bisa ga jaraba wanda ke so ya sa shi neman hanya na sauki a wurin aikata wannan aika ta Allah. A lokacin aikinsa a duniya, an yaba masa akan wai shi ne Mahadi da kuma Sarki har aka kuma nuna masa wata hanya na aikata sarautarsa ta wurin kauce wa giciye. Kowace jaraba ana shan karfinta dai da dai ne, Yesu kuma ya nace a kullum cewa, “Ubangiji, Kada in yi nawa nufi amma sai dai naka”. A karshe, a wannan dare kafin mutuwarsa, wata loto to kokuwa mai tsanani ta abko masa. Ya hangi abu ta gaba. Ya sani cewa dole a biya wonnan basli. A cikin gonar Jathsaimani, Yesu ya yi addu’a a cikin azabar rai har sa’anda Ruhu ta ci nasara ga so na jiki, sai kuma ya saka nanatawa cewa, “Amma dai, ba nawa mufi za a bi ba, sai naka.”

Yesu bai jira har sai an Kai shi kan giciye kafin ya yi nasa zabe ba. Bai kuma jira sai an kafa kaya a kansa kafin ya yi zabe tu nufinsa ba. Ya ci nasarar yakin nan tun daga Jathsaimani. Domin ya ci nasara a cikin addu’a, domin haka ya iya jemrewa ga giciye.
Dole mu ma mu zo Jathsaimani. Ko da shi ke mun rigaya mun yarda za mu bi shi tun farko, dole mu maimaita wannan. Kai bisa kai za mu ci gaba da bin Allah cikin addu’a har sai ruhunmu ta sha karfin jini da nama domi mu iya cewa, “Ba nawa nufi za a bi ba, sai naka.” Bayan haka, idan mun fuskanci giciye kuma muka kashe so na jiki, za mu iske cewa mun rigaya mun ci nasara.

Me ta faru a Jathsaimani? A nan muna samun gani daga makanta ta da da kuma samun sabon wurin zuba ido. Yawancin lokatai muna zuwa wurin Allah cikin addu’a da son mu yi masa biyayya a sausai, amma so na jiki tana rufe mana ido. A yayin da wadannan kwadayi ta jiki ta ke mamaye hankulanmu, sai duka zub da ido na mu tana kowa garesu da kuma abubuwan da an hana mu yi. Ko kuma za mu sa hankali kurum a kan wahalar da aka sa a gaban mu domin mu sami yanci. Babu kuma wuya mu sa hankali ga giciyi har mu kasa ganin tashiwa ta matattu wanda Allah ya sa bayan mun gama shan wahalar. A Jathsaimani, Ruhu za ya juya mu a sannu domin mu ga abubuwa daga waje da mu. Za ya nuna mana rayuwa ta tsarki mai zuba daga iko to tashiwan matattu wanda za ta zama namu. Za ya ba mu iko mu iya zama kamar Yesu, “Wanda ya jimre da gichiye domin farinzuchiya da aka sa gabansa (Ibraniyawa 12:1).” Domin Jathsaimani, za mu iya hangar gaba da giciye zuwa tashiwan matattu.




Yüklə 361,5 Kb.

Dostları ilə paylaş:
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©genderi.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

    Ana səhifə