Karban shawara daga wurin allah "Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya gama su za su ga Allah." Daga



Yüklə 361,5 Kb.
səhifə2/11
tarix17.09.2018
ölçüsü361,5 Kb.
#68717
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11

Babi Na 2


GANAWA DA ALLAH
A wannan zamanin da mu ke a ciki, mai halaye ta tunani irin ta asha da kuma tunani irin ta farnen kimiya da boko, babu wuya a yi wa mai jin muryar Allah dariya domin zancen irin wannan bata taso ba a zukatan marasa imani. Yan duniya sun saba da yi wa masu imani da jin muryar Allah ba’a, a bisa wannan kuma wata abin ban haushi ita ne, ikkilissiya ma ta soma goyi bayan irin wannan zama ta rashin imani. Mun kauce wa hanyan Littafi Mai Tsarki, wadda ta nuna mana cewa jin muryar Allah ita ne sanin Allah! Ba mamaki mun kasa gaba daya daga sanin nufin Allah. Domin haka muna bukatar wannan babban Mai-Shawara domin ya kubutar da mu.

Na yi magana cewa idan muna neman tsabtaccen zuciya, domin mu sami shawara daga hannun Allah, dole ne ka iya jin muryar Allah, da ganin wahayi daga wurin Allah da kuma gane nufinsa a game da yanayin da ka ke ciki. Ko da a ce mun yarda da wannan harka, dole mu sani cewa abu mai wuya ne a aikatata. A gaskiya, a cikin rayuwata ta kirista na shekaru goma, ban iya gane muryar Allah a zuciyata ba, ban kuma taba ga wahayi daga wurinsa ko so daya ba. A cikin nazarina ta Littafi daga farawa zuwa Ru’ya ta Yohanna, na iske cewa mutane su na jin muryar Allah. Na yi marimari in zama karmar mutanen nan na littafi, amma duk da kokarina, ban ji wata murya kirikiri a cikin zuciyata ba. Har a karshe na takaita cewa ai watakila na ja da baya ne, sai na yi tuba, da azumi da kara karatun Bibul, amma a ina, ban ji ko wata murya ba. Na karanta littafai iri iri wadanda sun yi koyasuwa a kan wannan zance, har ma da tambaya daga wadanda sun saba jin muryar Allah, na gwada yin duk dabarun da suka gaya mani, amma babu wata murya.

A karshe sai dai Ubangiji ya bude mani ido domin in sami wasu mabudai wadda suka bude mani hani hanya ta ganawa da Ruhu Mai Tsarki wanda ke zuciyata daga nan ne na soma jin muryarsa. Na kuma soma iya ganin wahayi. Cikakken labari na yadda na fara ganawa da Allah suna rubuce a wata littafi mai lakabi Ganawa da Allah. A wannan babi zan ba da dan gusurin irin mabudin da ta taimaki dubban mutane su soma shiga irin wannan ma’amala ta magana sakaninsu da Allahnsu.

Mabudai wadanda na yi amfani da su na samuwa a littafin Habakkuk 2:1,2.

“Zan tsaya wurin tsarona, in tsaya a bisa hasumiya, in duba, in ga abin da za ya fada mani da abin da zan amsa masa a kan karata. Ubangiji ya amsa mani, ya che, ka rubuta ru’yan, ta fita a fili chikin alluna, domin mai-karantawa shi yi a guje (ko kuma, domin a karantata ba da wahala ba”.

Wadannan su ne mabudai hudu wadda na gano, masu matukar amfani ta wurin koyo na ji da gane muryar Allah:



Mabudi ta 1 - Yi shiru da kanka

Mabudi ta 2 - Ka nasu a kowane yanayi

Mabudi ta 3 - Yi amfani da wahayi

Mabudi ta 4 - Rubuta rahoto




Mabudi ta 1 - yi shiru da kanka “Ku yi shuru, ku sani ni ne Allah (Zabura 46:10) Abu ta fari wadda ya kamata in yi kafin in soma jin muryar Allah ita ne in kawas da kunne daga duk wasu muryoyin da ba na Allah ba wadda ke neman su mamaye hankalina.

Habakkuk ya ce, “Zan tsaya wurin tsarona, in tsaya a bisa hasumiya...” wato wannan kalma ta koya mana cewa Habakkuk yana da wani wuri wadda zai iya buya shiru daga tunani da motsi ta jiki, da kuma zirgazirga da damuwa ta rayuwa.

Na sami dabaru dayawa yadda zan yi shiru da kaina, domin haka ba ta yi mani wuya in gani irin yanayi ta motsin Allah. Nuna kauna ga Allah ta raira wakokin bauta ko sujada tana da amfani kwarai ga mutane dayawa. A yayin da an kira Elisha ya ji magana daga wurin Allah domin sarakuna Israila da Yahuda, shi Elisha ya ce masu, “...amma yanzu sai a kawo mani mai-kidin molo. Ya zama fa, sa’anda mai-molo ya zo ya kada, hannun Ubangiji ya sabko a kansa (sarakuna II, 3:15)” sai ya fara yin annabci. A ta haka, wakoki na sujada na taimaka su kawo mana halin sannu a gaban Allah, domin mu gane motsi ta Allah.

Idan wata tunani ta zo mani game da wata abin da na manta na yi, sai in yi maza in rubutata domin kada in manta, bayan haka sai in cire tunanin daga zuciyata. Idan tunanin wata kasawa ta zunubi ta zo mani, nan da nan sai in yi tuba na kwarai, in kuma karbi wankewa ta jinin Dan Ragon Allah, sai in sa rigar adilci in kuma saya ba tsoro a gaban Allah.

Idan na zura wa Yesu ido (Ibraniyawa 12:2) na kuma yi shiru da kaina a gabansa, na kuma furta masa abin da ke zuciyata, nan da nan sai in ga cewa wannan ma’amala da ganawa tsakanin mu ta fara. Tunani na tafiya daga kursiyin Allah zuwa gare ni, a nan sai in iske cewa ina magana da sarkin sarakuna da kansa.

Dole ne mu nasu sosai mu kuma kafa fuskarmu a gareshi idan muna neman samun kalma tsabtace daga wurin Allah. In ba mu nasu ba, za mu ji mu kuma karbi namu tunanen ne kurum. Idan ba mu kafa fuska sosai ga Yesu ba, za mu karbi kalma mara tsabta, domin irin wannan tunani tana zuwa ne kurum ga wurin da hankalinmu ta ke. Idan mun kafa hankalinmu ga wata abin da zuciyarmu ke so, wannan irin tunani ta ruhu za ta zo daidai kamar wannan abin da mu ke so. Domin haka, kafin mu sami tsabtacen tunani, dole ne mu nasu tsit, mu kuma “kafa wa Yesu ido”. Zan sake maimaitawa, wannan tana yiwuwa idan muna yin sujada ga Sarkinmu, a haka zamu karbi maganarsa a cikin nasuwarmu.



Mabudi ta 2 - Ka nasu a Kowane Yanayi


“Ubbangiji ya amsa mani, ya che, ...(Habakkuk 2:2).” mun ga a nan dalladalla cewa kowane lokaci idan Habakkuk ya nasu, yana iya gane muryar Ubangiji. A lokacin da na ke koyon yadda zan ji muryar Allah, ina ta kasa kunne in ji wata murya irin na mutum. Amma na zo na iske cewa ba haka ne Allah ya saba yin magana da ni ba. Muryar Allah na zuwa caraf ne kamar wata tunani wadda ke “bullowa ba tare da sammani ba a cikin zuciyarmu.

Ga wata misali, a ce kana tukin mota a hanya sai nan da nan sunan wani ya bullo maka a tunaninka. Ko ka taba tunani cewa Allah ne ke so ka yi masa addu’a? Ko wannan na bullo maka domin muryar Allah ne domin ka yi masa addu’a? Yawancin mutane za su amsa cewa haka ne. Ni ma na yarda da haka. Wannan aukuwa ta koya mani cewa wasu irin wannan tunani na nan da nan suna zuwa daga wurin Allah ne. Wannan babban bude ido ne a gereni.

Daga gane wannan sai na soma rubuta rahoton duk tunani ta nan da nan, da yadda nake ganin abubuwa, da yadda nake jin abubuwa a jikina da kuma wahayin da nake gani a yayinda nake yin addu’a. Tarin dukan wannan ta ba ni mamaki domin irin zurfin hikima da yalwatan kauna wadda na gani a cikin rahoton nan. Wannan a gaskiye dai ba aikin tunani ba ne!

Littafi Mai Tsarki ta ambata wannan a hanyoyi da yawa. Manufin “paga” a harshen Yahudawa ita ne addu’a ma wasu, wato tushen manufanta ita ne “haduwa ta sa’a ko kuma haduwa wadda ba a shirya ba”. Domin haka idan Allah ya kira mu mu yi wa wasu addu’a yana amafani da “paga” wato “haduwa ta sa’a” a cikin tunaninmu.

Ta abubuwan da na koya da kuma na duban wasu mutane, na iske cewa mutum zai iya nasuwa domin ya kama kan irin wadannan tunani ta sa’a. Idan na nasu a gaban Ubangiji Allah ina addu’a, sai in ji shi yana yi mani magani a hankali cikin zurfin tunanina, da yanayi ta jikina da kuma a cikin wahayi ta ruhu da na jiki.

Mabudi ta 3 - Yi amfani da Wahayi


Na yi dan magana game da wannan a shafin da ta wuce, amma bari mu yi cikakken nazari a kan wannan. Habakkuk ya ce, “zan tsaya wurin tsarona... in ga... Ubangiji ya amsa mani, ya che, ka rubuta ru’yan...” Abin sha’awa ne mu iske cewa a yayin da Habakkuk ya nasu ya yi shiru domin ya ji, ya sa hankali domin ya ga ru’ya ko wahayi daga irin amsar da Ubangiji zai ba shi. Ya bude idanun zuciyarsa domin ya hangi yanayi ta duniya ta ruhaniya domin ya ji abin da Allah ya ke so ya nuna mashi. Wannan wata hikima ce mai ban sha’awa sosai.

Ban taba yin tunanin bude idanun zuciyata domin in ga wahayi ba. A gaskiya ban ma taba tunanin ko wahayi tana da daraja a cikin harkar rayuwar mai bi ta sabon alkawali ba. Amma, a yayin da na ci gaba da tunani akan wannan al’amari sai na iske cewa ai ashe Allah ya ba ni wannan idanu ta ruhaniya domin wannan dalili ce kurum. Ba a banu su domin kwadayi, ko tunanin kasawa, ko kuma fahariya a kan nasara wadda na ke samu ta aikin jikina ba. An bani su ne domin in yi amfani da su in hangi duniya ta ruhaniya domin in gane irin motsi ta Ubangiji Allah Madawami. Akwai wata lafiyayyar duniya ta ruhu wadda ke kewaye da ni. Akwai mala’iku, da aljani, da Ruhu Mai Tsarki, da Ubangiji Allah da kuma Dansa Yesu. Irin al’adu ta tunanin duniya ce ke hana ni ganin kewaye da ni, domin irin shakkar da suka dasa a zuciyata. Nufin Allah har yanzu ita ne in yi amfani da dukan wadannan baiwan domin in kara zaman zumunci namu tare da shi.

Mataki ta farko domin gani a cikin ruhu ita ne mu duba. Daniel na ganin wata wahayi “a zuciyarsa” sai ya ce, “Ina gani... ina na ina dubawa... na gani... (Daniel 7:1,9,13).” Habakkuk ya kafa tsaro domin ya gani (Habakkuk 2:1) a cikin Ruhu ne sai Yohanna ya gani (Ru’ya ta Yohanna 4:1). A kamar haka ne, idan ina cikin addu’a ina neman Yesu wanda ke tare da ni, in kuma ci gaba da kallonsa a yayin da yana yi mani magana game da abubuwan da ke a zuciyarsa. Kirista mafi yawa sun sani cewa idan sun duba za su gani. Ma’anar Immanuel shi ne Yesu, wato Allah na tare da. Yanzu ne idanunmu sun soma gani wasu ababa wanda ke a labe tun da farko. Sai mu soma ganin wahayi ta sa’a sa’a, kamar yadda mu na karban tunani ta sa’a sa’a. Za mu iya ganin Kristi tare da mu domin yana nan tare da mu.

Yawancin lokaci abin tana zuwa ba tare da wahala ba, domin haka muna iya ce ko tunaninmu kurum, har mu rena ma wahayin. Shakka ita ce babban makamin shaidan ga mai bi. Idan ka nace da rubuta wadannan ru’yoyin, ka kuma jaraba su yadda babi ta uku za ta koya mana, dukan shakkarmu za ta narke a gabar bangaskiya a yayin da za a sani cewa Allah mai girma shi kadai ne zai iya haifar da su.

Allah ya bayana kansa ga mutanen alkawalinsa ta wurin mafarki da wahayi daga farawa har zuwa Ru’ya ta Yohanna. Ya yi alkawali cewa idan Ruhunsa ta sauko bisa mutane kamar na Ayukan Manzanni ta 2, wannan irin ma’amala ta wurin mafarki da wahayi za ta ci gaba ga masu bi (Ayukan Manzanni 2:1-4). Yesu, wanda shi ne misalinmu mara aibi, ya nuna mana irin wannan ma’amala da Allah wadda ba tsinkewa. Ya ce shi ba ya yin komai ta yadda ra’ayinsa ke so amma sai dai abin da yana ganin Ubansa ke yi ko fadi (Yohanna 5:19,20,30). Wannan rayuwace mai ban mamaki!.

Za ta iya yiwuwa mu yi rayuwa mai umurni daga hannun Allah kamar irin ta Yesu? Na bada gaskiya za ta yiwu. Daya daga cikin dalilen da ya sa Yesu ya mutu ita ne domin labulen nan ta yage daga sama zuwa kasa domin dukanmu mu sami shiga zuwa gaban fuskar Allah. Ya umurce mu cewa mu matso kusa (Ibraniyawa 10:19-22). Wannan darasin da na ke magana a kai za ta iya zama kamar abin hauka ga al’adunmu na zamanin yau, amma Littafi ta nuna dakidaki cewa wannan koyasuwa da rayuwa irin ta masu bi ne. Lokaci ta yi domin mu kabutar da ikkilisiya daga wannan yaudara wadda ta mamaye ta ta wadannan shekaru.


Mabudi ta 4 - Rubuta Rahoto


Allah ya gaya wa Habakkuk “ka rubuta ru’yan, ta fita a fili cikin alluna... (Habakkuk 2:2)”. Ba ta taba zo mani wai in rubuta dukan addu’ata da kuma amsoshin da Allah ke ba ni kamar na Habakkuk ba. Amma wannan tana cikin tsari ta tarbiyan Littafi Mai Tsarki. Yawancin dukan babin Littafi Mai Tsarki an rubuta su kamar rahoto ne. Misali masu kyau a wannan su ne yawancin Littafin Zabura, da anabcin anabawa da kuma dukan Littafin Ru’ya ta Yohanna. Me ya sa ban taba tunani a kan wannan ba? Me ya sa ban ma taba jin ko wa’azi daya a kan wannan ba?.
Na kira irin wannan rubuta, rubuta rahoto, har na soma amfami da ita domin in gani. Na iske wannan wata shahararriyar makami ce ta gane motsi irin ta Allah, domin a cikin bangaskiya sai in dade ina yin rahoto wadda na yi imani daga wurin Allah ta ke zuwa. Ba na gwada wannan zubi a lokacin da ta ke zuwa, domin na sani idan motsin ta tsaya zan iya tafiya in gwada ta a hankali in gani ko ta yarda da ka’idodin Littafi Mai Tsarki.

Za ka yi mamaki da abin da za ta faru idan ka gwada amfani da rubuta rahoto. Idan shakka ta kawo maka hari a farko, ka yar da shi, ka tuna wa kanka cewa wannan umurni ce daga Littafi, kuma Allah har wa yau yana magana da ‘yayansa. Ka da ka dauke ta da nauyi a fari. Ka yi ta kamar da wasa ce. Idan mun dauki abu da nauyi nauyi babu wuya mu taurara hankalinmu har mu hana motsin Ruhu Mai Tsarki. Ubangiji na samun dama ya yi motsi ne sosai idan mun daina yin namu ciki irin ta jiki mu kuma shiga hutun Allah (Ibraniyawa 4:10). Domin haka kwantar, da hankalinka, ka gyara zama, ka zaro alkalaminka da takarda, ka kuma sa hankalinka ga Allah a cikin yabo da sujada, domin ka sami fuskarsa. Idan ka rubuta tambayoyinka ga Allah ka kuma natsu, ka kuma zura wa Yesu ido wadda ke tare da kai nan da nan za ka ji wata tunani mai kyau tana baka amsar tambayarka. Kada ka yi musu ko kuma shakkarta a wannan lokacin, rubutata a cikin bangaskiya kai da kanka za ka yi mamaki idan ka soma karanta wannan rahoto nan gaba, za ta ba ka mamaki idan ka iske cewa ka na ganawa da Allah.


Kalma ta Gargadi

Ba zan shawarci wani ya yi wadannan matakin idan bai taba karanta dukan sabon Alkawali ko dukan Littafi Mai Tsarki ba. Ya kuma zama abin wajibi ne muna da wuri wanda muna samun shugabanta ta ruhaniya a kullum. Duniya ta ruhaniya ba abin tsoro ba ne, amma ya kamata mu sani cewa ba Ruhu Mai Tsarki ne kadai yana ba mu irin tunani ta sa’a ba. Domin haka duk rahoton da za mu rubuta dole a sake bincika ta. Na daya, dole duk rahoto ta yarda da ruhun kalmar Littafi Mai Tsarki. Babu ko lokaci daya wanda rahoto za ta fi umurni ta Allah a Littafi iko. Kuma duk abin da za ka aikata daga rahoton ka, ta zama wadanda sun zama shigabannenka cikin hanyar Ubangiji sun yarda da ita tukun.


Takaitawa

Za ka iya jin muryar Allah ka kuma ga wahayinsa! Ko da kai wane irin mutum ne, idan ka ba da kanka domin jagora ta ruhu wanda ke cikin masu bi na jikin Kristi, rayuwa mai aikin da ma’amala da Allah za ta iya zama taka.



Amsa

Me za ta hana ka aikata wannan ka’idodin da ka koya? Ka rubuta wa Yesu wasika, ka nuna kaunarka a gareshi, ka kawo kukanka da tambayoyi na zuciyarka da duk addu’ar da ka ke so ka mika masa. Bayan ka gama fadin duk abin da ka ke so ka fada, sai ka yi shiru da kanka, ka zura wa Yesu ido ka kuma fara rubuta duk tunanin da ke tasowa daga cikin zuciyarka. Yabo ta tabbata ga Allah, kai ma za ka iya ganawa da Allah.



Yüklə 361,5 Kb.

Dostları ilə paylaş:
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©genderi.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

    Ana səhifə