Karban shawara daga wurin allah "Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya gama su za su ga Allah." Daga



Yüklə 361,5 Kb.
səhifə3/11
tarix17.09.2018
ölçüsü361,5 Kb.
#68717
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11

Babi Na 3



MAI KARA DA MAI LALLASA
Ko ka taba neman ka mika kanka ga Yesu a dukan farnen rayuwarka, domin ka sami kwanciyar rai, da iko, da natsuwa, amma sai ka iske wata tunani a cikinka na zarganka, da sharantaka har ka rasa abin yi? Idan haka ne, ka yi wauta domin ka na sauraran shaitan wanda shi ne a ke kira mai kawo karan yan uwa masu bi.

Yesu shi ne mai ba mu shawara mai alfarma, wanda shi kadai ne ke warkar da duk damuwarmu ta ruhu. A kullun gyara da warkasuwa na zuwa ta hannun wahayi ta nufin Allah, wato iya ganin mulkin kauna ta Allah a rayuwarmu da yanayinmu. Dole ne mu iya ganin wahayi na Allah tare da jin muryarsa a zukatanmu idan muna so mu ci gaba cikin nufin Allah.

Yanzu dai mun gane cewa ma’amala da duniya ta ruhu tana aukuwa ne gare mu a ta hanyar tunani ta sa’a sa’a ko kuma wahayi masu saukowa a zukatanmu ko tunaninmu. Mun koyi yadda za mu yi shiru mu san Allah. da kanmu domin Mun koyi yadda kuma shirya za mu shirya zukatanmu domin mu kama kalmoni da wahayi daga Ruhu Mai Tsarki.

Har ma mun soma rubuta rahoton ganawarmu da Allah, muna yantas da tunaninmu domin mu karba a cikin bangaskiya, da cikakken sani cewa za mu gwada duk abin da muka rubuta zuwa nan gaba.

Da na ci gaba da ganawa da duniya ta ruhaniya, sai na soma ganewa cewa ba dukan tunani ta sa’a sa’a ne ta ke zuwa daga wurin tunani ta irin hali na Kristi ba. Shine, ko akwai wasu masu zama a wannan duniya wadanda ba na Ruhu Mai Tsarki ba, kuma suna neman su cika mani tunani? To me zan yi da su? Wasu domin wannan suna tunami su ja da baya. Idan muna ji daga gurin shaitan kamar yadda mmuna ji daga wurin Allah, ba za ta fi sauki ba idan mun daina ji gaba ki daya domin kada mu fadi a hannun yaudara ba? Ni ban zabi irin wannan amsar ba. Na sha azaba sosai kafin na soma jin muryar Allah, domin haka ba zan bar shaitan ya saci wannan albarka daga wurina a sauke haka ba. Na nace yanzu in zama da ilimi, wadda za ta sa in gane muryar Ruhu Mai Tsarki daga muryar Iblis, domin in yaki duk muryar da ba na Ruhu Mai Tsarki wanda ke zama a zucijata ba.
“Bulus ya ba da gargadi kamar haka: “Gama makaman yakinmu ba na jiki ba ne, amma masu-iko ne gaban Allah da za su rushe wurare masu-karfi; muna rushe zache-zache da kowane madaukakin abu wanda aka daukaka domin gaba da samin Allah, muna komo da kowane tunani chikin bauta ga biyayyar Kristi (Korinthiyawa ta 2,10:4,5).”


Wannan ta nuna a sarari cewa Bulus ya gane tushe ta ruhaniya wanda ke kawo wadannan tunani ta zukatanmu. Ya sani cewa akwai yaki wadda ta kamata ya yaka, da kuma abokangaba wanda ya kamata mu hallakar, da kuma firsinoni wanda ya kamata mu dauka mu karfafa namu irin tunanin. Domin wasu tunani wanda ba na tsarki ba suna nan, ba ta nuna cewa sai mu ki yin tunani ba gaba ki daya. Domin kurum wata wahayi mai aibi ta abko ma zuciyarmu sai mu rufe idanunmu ta ruhaniya? A’a ba haka ba. Maimakon haka sai mu tashi cikin iko ta sunan Yesu Kristi! Ka da ka yarda a ka da kai ba tare da ka yi fada ba. Ka hallakar da ikon iblis domin ka rungumi iko ta Kristi!.

Mataki ta fari domin gane muryoyin da ke zuwa mani, ita ne, gane dalla dalla irin halin mutanen da ke magana da ni. Maganar da mu ke yi na ba da launin irin halinmu. A kabilar Yahuda da kuma koyasuwa ta Bibul, sunan mutum tana dunkule da ma’anar irin halinsa. Idan ka san sunan wani nan da nan za ka san abu masu yawa a kansa. Idan Allah ya canza halin wani a lokatai masu yawa yana canza masu sunansu. Misali su ne Yakubu zuwa Israila, Siman zuwa Bbitrus, shawulu zuwa Bulus. Domin in sami cikakken ganewa a kan halin wadannan masu magana da ni, sai na yi nazari a kan sunan da aka ba wa shaitan da kuma Ruha Mai Tsarki a cikin Bibul. Wannan ta canza rayuwata ba kadan ba tun daga lokacin.


Sunaye da Halayen Shaitan Mai kawo Kara

Asalin halin shaidan shi ne yawan kawo kara. Tushen sunansa a harshen Helleniyawa ita ne “diablos,” wadda aka juya ta a Turance, “devil” wato shaitan manufarta ita ne “mai kawo kara” ko kuma “mai tsegumi” Tushen aikin shaitan shi ne ya origa kowa kawo dare da rana.

A Ru’ya ta Yohanna an rubuta cewa, “Na ji babbar murya kuma cikin sama, ta che, Yanzu cheto, da iko, da mulkin Allahnmu ya zo, da sarautar Kristinsa kuma gama an jefasda mai-saran yan-uwannmu, shi wanda ya ke nasara dare da rana a gaban Allahnmu. Suka yi masara da shi sabili da jinin Dan rago, sabada maganar shaidassu kuma; ba su kamnachi ransu kuma har mutuwa ba (Ru’ya ta Yohanna 12:10,11)”. Ka lura da cewa, ceto, da iko, da mulkin Allah da kuma ikon Kristi na aukuwa a rayuwanmu idan mun ci nasara da kuma hambare wannan mai saranmi.

Idan asalin shaitan shi ne ya kawo kara da sara, a kan wa ya ke kawo wannan kara ko sara? A nan yadda muka karanta yana kawo sara a gaban Allah a kan masu bi. A Littafin Ayuba 1:9 mun ga shaitan ya na kawo sara a gaban Allah game da Ayinba: “A banza na Ayuba ya ke tsoron Allah?” abin nufi a nan ita ne,” Ai gaskiya ne Ayuba na tsoronka, ya Allah. Duba irin albarkun da ka jibga masa. Yana bautarka domin irin wannan halin da ka ke nuna masa ne kurum. Ba ya kaunarka ko kadan, kaunarsa na kan irin abin da ka ke ba shi ne kurum.”

Sara a kan masu bi bai tsaya a gaban Allah kurumba. Kowane irin shawara ta kyeta, da sharanta juna domin makirci, da kuma kowane irin sara a cikin tunaninmu a kan dau’uwanmu tana fitowa daga magabci mai sara wato shaitan. Idan muna yin zumunci da irin wannan harka muna kuma furta irin wannan sara game da yau’uwa masu bi, harshenmu “kwa daga Jahannama a ke kunna shi “(Yakub 3:6). Idan zukatanmu suna cike da kishi, da tsaguwa, da kowane irin mugun al’amari, to a nan ne lalle mugunta ke samun wurin zama Mai lafiya (Yakubu 3:15,16).

Shaitan yana zuwa ya faskancemu da sara, da tsokana, da kuma sharantamu a zuciyarmu. A yayin da Ruhu Mai Tsarki ya kai Yesu zuwa cikin jeji, sai Iblis ya gamu da ga ce masa, “Idan kai Dan Allah ne...” (Luka 4:3).” Ko ka dago irin saran da ke cikin wannan zance? Wato shaitan na nufin cewa “Idan kai ne na ainihi a yadda ka fada...” Haka yana yi mana sara zai ce “Idan kai dan Allah na ainihi ne, me zai sa za ka aikata irin wannan abu? Idan kai na ruhaniya ne me zai sa ba za ka yi addu’a sosai ba? Ai Dakta Cho yana yin addu’a na awa shida kowace rana. Don me ba ka yin irin wannan addu’a idan kana kira kanka mai bi na ainahi? Idan kai mai bi na kirki ne, ai za ka kara lokacin binciken Littafi Mai Tsarki. Ba za ka cika fushi a kullum ba. Ba za ka aikata wannan ko wancan abu ba.” Haka irin wannan sara tana cin gaba a zukatanmu har za ta kai loton da za mu yarda da ita har mu ba da kanmu ga wannan yaudara.

Shaitan ma yana saran Allah a gabanmu. Idan zaka iya tuna, a gonar adinin, shaitan (macijin nan) ya gaya wa macen nan, cewa, “Ashe, ko Allah ya che, Ba za ku chi daga dukan itatuwa na gona ba?... gama Allah ya sani ran da kuka chi daga chiki ran nan idanunku za su bude, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta’ (Farawa 3:1,5).” Ka ga yadda shaitan na tsokanan nufin Allah, har da sara cewa Allah na so ya yi masu rowa game da wata abu mai kyau wadda shi yana da shi? Idan muna cikin damuwa da jin tausayin kanmu, irin wannan harbi ta bakan iblis tana iya shiga zukatanmu ba da wuya ba.” Allah ya taba sanar maka da kaunarsa? Idan Allah yana sonka ai ba zai taba barin irin wannan mugun hali ta same ka ba. Idan Allah ya ga dama ai zai iya hana duk wadannan tsegumi wanda a ke yi a kanka. Idan Allah yana son ka kamar yadda yana son sauran mutane, ai zai ba ka aiki mai kyau, da gida mai daraja da kuma aure mai kwanciyar hankali. Allah dai baya kaunarka ko kadan.” Idan mun yarda da wadannan sara, ba tare da neman samin tushen su ba, mun dukufa ga tafiya bisa hanyar mutuwa da hallaka ke nan kamar irin na Hauwa’u.
Uban Karya

“Sa’anda ya ke yin karya, da kansa ya ke yi. Gama makaryachi ne shi, da uban karya kuma (Yohanna 8:44).” Shaitan shi ne tushen sara wadda ke zuwa gare mu a kullum, kuma saransa a garemu tana hade da gaskiya da kuma karya.


Ka dubi wannan misali, a cikin Ayuba (Ayuba 1:9,10,11).

“Magabchi fa ya amsa ma Ubangiji ya ce, A banza ne Ayuba ya ke tsoron Allah? Ba ka kewaye shi da shimge ba, da shi da gidansa, da dukan abin da yake da shi, a kowane sassa? Ka albakarchi aikin hannuwansa, dabbobinsa sun karu a kasa. Mika hannunka kadai yanzu, ka tabba dukan abin da ya ke da shi, za ya la’anta ka a fuskarka!”

Akwai dan gaskiya a wannan zance na iblis. Allah ya kewaye Ayuba da wata shimge da duk dukiyarsa. Allah kuma ya yi masa albarka sosai wadda ta sa shi ya zama mai albarka fiye da kowa. A nan dai shaitan yana fadin gaskiya. Idan ba mu yi hankali ba daga wannan dan gaskiyar, ba za mu gane cewa kalmominsa na gaba da wannan karya ba ce. Allah ya ba shaitan izini domin ya tabba duk abin da Ayuba ya ke da shi, amma Ayuba bai la’anta Allah ba. Ko da shi ko dai Ayuba ya damu sosai. Har ya la’anta ranar da aka haife shi. Amma dai bai la’anta Allah ba. Wannan kalma ta shaitan karya ce.

Ka lura da irin nufin da shaitan ya ke da shi a nan, wato yana so ne ya kawo shakka a kan irin tunanin da ke zuciyar Ayuba. Ka yi hankali idan ka na sharanta da makirci abin da wani ke yi. Ba za ka taba sanin ko me yake motsa wani ya yi abin da ya ke yi ba. Ba za ka iya sharanta nufin zuciyar wani ba. Wannan farne harka ce wadda Allah kadai ya ke da iko da ilimi a kan ta. Ka da ka bar shaitan ya mai da ke juji na zubar da sharan sararsa.

Ka kuma tuna cewa yawancin abubuwan da shaitan zai fada gaskiya ne. Shaitan ba wawa ba ne, ya san cewa idan ya yi maka karya zalla za ka gane yana hada karya da gaskiya domin ka badagaskiya da ita. Ga wata yar shawara domin gane yaudara ta shaidan.





85 Bisa Dari ta Gaskiya + 15 Bisa Dari ta

Karya + Markirci = Sara ta Shaitan

Bincike kowane irin karya a zuciyarka. Yawancin lokaci suna zuwa ne a barkatai cikin siffar al’amura ta kasawa: “Ni ba na iya yin komai daidai.” “Ba zan taba iya cin nasara ba.” “Allah ba ya kaunata domin irin abubuwan da na yi.” “Kowa ya ki jinina.” “Dukan mutane makaryata ne.” Ka dago nanda nan cewa shaitan yana neman ya cika zuciyarka da karya ke nan (Ayukan Manzanni 5:3) Kada ka ba irin wannan tunani ta makirci da hallaka fili a zuciyarka.


Magabci da mai gaba

“Makiyin da ya shibka su kuma shaitan ne (Matta 13:39)” “Ku yi hankali shimfide, ku yi zaman tsaro: magabchinku shaitan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya chinye ku tsaya masa fa, kuna tabbatawa chikin bangaskiyarku...(Bitrus I 5:8,9).”

“Shi mai kisankai ne tun daga farko (Yohanna 8:44).”

Babu shakka ko kadan, shaitan magabcinka ne. Yana neman ya hallaka ne har abada. Kowane harka na hallaka, da sara, da mai kawo tsoro, da na zargi, da alhaki, da tunani ta makirci tana sirowa ne daga wurinsa. Kada ka ba wata tunani mai kada kai kasa wuri a rayuwarka, nan da nan ka cika zuciyarka da tunani mai zuwa daga gurin Allah.


Mala’ika Mai Haske”

Wata mai munar hali ta shaitan a cikin sararsa ita ne irin iyawa nasa ta canza kansa kamar mala’ika mai haske (Korinthiyawa II, 11:14). Shaitan yana kunna maka tunani a zuciyarka domin ya kawo maka hallaka, amma zai yi kamar wadannan tunani suna zuwa daga wurin Allah ne. Domin haka zai saka ka dauka alhakin da ba naka ba, ya sa ka yi tunani cewa ka saba wa Allah, amma dai duk wannan shaitan ne ya ke kokari ya hallaka ka.

Ta yaya wannan za ta faru? Ta yaya zamu amince da kalma ta iblis kamar ta fito daga hannun Ubangiji Mai Tsarki? Magabcinmu yana da wayo sosai, yana iya amfani da sunan adilci domin cikata nasa makirci. Misalin irin wannan ita ne amfani da ya ke yi da kalmar Allah domin ya yaki mu masu bi. Yana sa mu mu kafa hankalinmu a kan dokokin Allah domin ya tuna mana da kasawarmu ta wurin aikatata, domin dai kada mu sa hankalinmu ga iko ta rai wanda Yesu Kristi ya ba duk masu bi domin su ci nasara. Yana zuga mu mu yi amfani da kalmar Allah domin mu ci mutuncin juna Kirista a maimakon mu karfafa juna a cikin hanyar rai (Romawa 15:4). Babu wuya mu sami kanmu muna amfani da Bibul ta zama kulki ta hambare wasu a maimakon amfani da ita ta wurin tsarkake juna.

Shaitan yana iya sa mu kasa gane babanci tsakanin jan kunne da sharantawa, wannan tana hana samun daman kin iblis ko kuma karban tsarkakewa daga hannun Ruhu Mai ta wurin irin dabatunsa. Za me iya koyon sanin banbancincsa, mu kuma hambare aikin mai sarannan, mu kuma kawo ceto, iko da mulkin Allah a rayuwarmu.

Sharantawa ta ibblis tana kawo mana tunani a birtice ta rasanawa. Wannan halice ta jujayi ta dankan alhakin zunubanmu da rashin iyawawmu. Ruhu Mai Tsarki kuwa yana taba mu game da zunubi wanda muka yi mai ganuwa ne. Zai muna mana laifin ne a sarani domin mu gane wurin da damuwar dake.

Muryar Sherantawa ta shaidan tana zuga ka zuwa hallaka. Zai mamaye hankalinka har ka badegaskiya cewa abin yi game da kasawarka shine ka rusar da bangaskiyarka ga Allah, ga sauran mutane, ga kai kanka, da kuma dukan al’amuran rayuwarka. Amma shi Ruhun Allah zai kawo ka zuwa ga tuba ne. I, an yarda ka yi zunubi, amma akwai wankewa da sabon Rai ta wunin jinin Yesu Kristi. Baba shakka Ubangiji mai adilci ne kuma za ya gafarta maka.

A karshe, shaitan zai gaya make cewa baba wata hanya ta tsira. Zai ce, ai kai la’ananne ne kuma baka da bege babu kuma abin da zo ka iya yi dominsamin sira. Rayuwarka ta iko bakin hallaka. Kasawarka ta kai intaha, babu alamar ceto. Amma Ruhu Mai Tsarki yana zuwa maka ne da irin hikimar abin da ta kamata ka yi. “Mai-yin sata kada shi kara yin sata: amma gwamma shi yi aiki, da hannuwansa yana aika abin da ya ke da kyau, domin shi kasance da abin da ya ke da kyau, domin shi kasance da abin da za shi diba shi bayas ga wanda ya rasa (Afisawa 4:28).” “Amma yanzu sai kuma ku kawasda dukan wadannan; fushi, basala, keta, tsegunnim alfasha daga chikin bakinku… ku zama masu-godiya (Dubi Kolossiyawa 3:5-17).” “Domin wannan fa sai ku fadi gaskiya kowane game da dan-uwansa, kuna kawasda karya, gama mu gababuwa ne na junanmu (Afisawa 4:25).”

Kada mu taba Ruhu Mai Tsarki yo ke nuna mana a kan zunubanmu. Shi ba za ya ta amsa musu ba. Idan mun ci gaba da musu, kunnen zuciyarmu za ta kullu ta kuma kurmance daga jin muryarsa. Amma a kullum ya kamata mu ki dukan sharantawa ta shaitan, mu ki dukan sharantawa ta shaitan, mu muna masa kuma duk aikin da jinin Dan Ragon nan ya yi domin mu, mu kuma furta kalmnin shaida na mu.

Barawo.

“Barawo ba ya kan zo ba sai domin sata, da kisa, da hallaka: ni na zo domin su sami rai, su same shi a yalwache kuma (Yohanna 10:10).”



Shaitan shi ne mai sara kuma shi ne tushen dukan kow are irin sora ta mugunta. Shi makaryaci ne kuma shi ne uban kanya duka, yana hada karya da gaskiya ya yandare mu domin bangaskiyarmu ga Allah da mutane har da akanmu ta rushe. Shi kuma kisa ne wadda a kowane hanya shi magabci ne a garemu. Yana mayar da kansa kamar malaika ta haske, domin ye yandare mu daga gane shi, domin ya yandare mu daga gane shi, domin ya hana mu yaki da irin hari wadda ya ke yi mana. Shi kuma barawo ne wanda yake neman ya yi sata da kisa da kuma hallaka a kullum duk abubuwan adilci loton da muko iske ana neman a gire bangaskiyarmu, mun san wanda ya ke aikata wannan hali: wato shaitan! Amma bai kamata mu ba zhi izni ya aikata irin wannan halinsa mugunta ba. Za mu iya yakansa. Za mu kuma iya cin nasara bisa kansa. Za mu uja kuma yar da shi zuwa kasa ta wurin iko da karfi ta Yesu Kristi wanda ke mulki da zama a cikinmu.


Yüklə 361,5 Kb.

Dostları ilə paylaş:
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©genderi.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

    Ana səhifə