Karban shawara daga wurin allah "Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya gama su za su ga Allah." Daga



Yüklə 361,5 Kb.
səhifə8/11
tarix17.09.2018
ölçüsü361,5 Kb.
#68717
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11

RASHIN DA’A


Yawancin lokaci ba mu sani cewa rashin da’a tana iya kawo mana bakin ciki ba. Idan mun saba da wata irin hali ta rayuwa, tana da wuya mu amince da cewa akwai wata hali mafi amfani da namu.

Babu wuya in shiga cikin bakin ciki idan ba ni da wata sani game da nufin Allah a cikin rayuwata. A ce ban san ko’ ina hanya ta dama ko hagu ba. Gani nan dai a kan hanya mai kaini zuwa wuri mara suna kuma ina son in yi ta tafiya. Ta zama tilas ne in nemi sanin nufin Allah a kowane rana. Wannan tana da muhimmanci ga masu aikin kansa da kuma marasa ciki ko kuma mata masu aure. Idan Allah ya nada ni in yi wata aiki zan sami kwanciyar rai da kwazo domin yin kowane irin harka wadda ke gabana ko da shi ke aikin ba wata abu ne mai daraja a gabar yan adam ba. Wannan ba cewa sai an yi wata abu ne mai daraja a gabar yan adam ba. Wannan ba cewa sai an yi wata babban addu’a a kullum kafin a yi kome ba. A kasance, idan ina rayuwa cikin biyayya ga Kiristi kuma zuciyata tana dangana a gare shi, yawancin irin tunanin da ke zuwa mani a kai daga wurin Allah ne. Abin koyo a nan ita ne mu zama da nasuwa domin mu ji muryar Allah, domin ka da hayaniya ta jiki ta ja hankalinmu har mu soma bin abubuwa ta ido.

Yawan shakka domin aikata abu na iya kawo bakin ciki. A ce muna da wata muhimmiyar abin da ta na neman ra’ayinmu. Muna kuma daukan makonne masu yawa muna ta tunani sama da kasa game da ita. Sai a karshe bayan a matsa mana, sai mun yi zaben mu, amma ta bayan haka sai mu dauki yan makonne muna tunani ko wannan matakin da muka zoba din nan daidai ne. Domin haka karfinmu da kwazonmu sai ta janye gaba daya. Ko akwai wata hanya fiye da wannan?

Idan ina son in yi wata zaba mai muhimmanci, a farko mataki na ita ce in yi bincike. Sai in karanta kowane irin abu wanda ta shafi wannan zance. Zan kuma nemi shawaran mutane na Allah wanda sun kwaru a wannan hanya, in kuma karbi shawaransu. Bayan na ga cewa duk ababan da na tara sun hadu daidai, sai in kawo duka wannan zuwa gaban Ubangiji. Ta wurin rubuta rahoto, sai in tambaya a gaban Allah in kuma ji shawaran Ruhun Allah a kan wannan. Domin wannan zance ce mai nauyi, zan ba masu ba ni da shawara ta ruhaniya domin. Su tabas wannan zance wanda na ji daga warin Allah, domin sun kuma yi gyara idan akwa. A karshw, idan na tabbata cewa na yi duk abin da Allah ya ke so na yi, sai in dauki mataki in kuma aikata wannan nufinsa. Ba na barin ko shakka kadan ta sha kaina, ko da a ce sakamakon wannan mataki ba kamar yadda nake zato ba. Zan amince da Allah wanda ya na jagoranceni wanda kuma shi ne mai mayar da kome ya zama ta nagarta a gareni ko da a ce na yi kuskure ne.

Wannan ta yi kamar wata babban aiki ne mai cin lokaci. To me za mu ce game da matakin da ke bukatar hanzari? Irin wannan sai in amince da Ruhu wanda ke cikina domin ya ba ni hikima na wannan bukata na yanzu. Akwai lokaci a kullum domin a sa kome ta waje (Jiki) ta zama shiru domin a ji wannan karamin murya ta Allah mai sannu. Ka bi jagorantakarsa a daidai karfin iyawan da ka ke da shi. Kuma, kada ka bar wata hali ta shakka ta ja ka baya. Ko ma da ka yi kuskure, Allahnka yana da iko ya canza wannan domin ta zama cika abin nufinsa domin kawo maka nagara. Ka amince da shi.

RASHIN KULA DA JIKI


Rashin cin abinci mai kyau, da motsa jiki da kuma rashin isasshen barci na iya jawo bakin ciki. Akwai wasu irin abinci wanda ke kawo nauyin jiki da kuma nauyin ruhu. Yawan cin abinici na kawo yawan kiba wanda ke kawo reinnikai wanda na kuma haifar da bakin ciki. Muna bukatar wahayi wanda ke nuna mana kanmu ta wurin cin abinci domin daukaka Allah kurum, da kuma gina jiki mai lafiya yadda Allah ya nufa a garemu tun daga farko.

A wata bincike ta nazari wanda aka yi akan masu fama da bakin ciki an iske cewa idan suna mosta jiki babu wuya su fita doga wannan hali a nan da nan. Ka bincike ka gani kowane irin motsa jiki ne Ubangiji ya shirya maka domin ka sami karfi ta wurinsa. Kamar yadda jikin ka za ta ji dadin samun lafiya daga wasa ta motsa jiki, haka ma ruhun ka da naske ta farin ciki za ta taso cikin duhun nan ta bakin ciki.

Kirista masu yawa su na gani cewa idan ba ka ba kanka barci ba sosai, ai kai ne mutum na ruhaniya sosai. Wato idan kana aikin Allah har zuwa shabiyu ta dare, kuma ka farkawajen karfe hudu na safe domin ka yi addu’a ta awa uku, lalle kai babban tsabtace an Allah ne.Watakila kai daya ne daga cikin irin mutanen nan masu bukatar awa hudu kumim na barci. Da kyau! Amma yawancinmu za mu gaji kacal har mu sona ciku da bakin ciki idan mun ci gaba da irin wannan hali ta rashin barci. Ta na da amfani kwarai idan muna da yanci na ware kanmu domin mu huta. A wasu halin abu ta ruhu wanda za mu iya yi da kannmu ita ne mu hau gado mu yi barci: Idan ka na wata narka wanda ta fi awa 16 na rana, ka bincika babu wuya kana yin ababa fiye da yanda Allah ya shirya maka. Ka nemi nufinsa a gareka, ka kuma dukufa ga wannan a kan wannan kurum. A wasu lokatai ma kana bukatar hutu. Idan ka binciki dokoki ta Isohon Alkawali, za ka isko cewa Allah ya shirya lokatai da yawa domin biki, (na cin abinci). A wannan lokaci na biki, ana bidan kowa ya bar gidansa da ayuka ta kullum domin su je bakonci a Urushalima wurin babban biki. A gaskiya, a wannan taro, akwai ababa ta ruhaniya wanda an umurta a yi a wannan taro, amma yawancin lokacin ana amfani da ita domin cin abinci, shayeshaye, rawa, wasa da kuma ganawa da abokai ne kurum. Ka da ta zama maka abin mamaki idan Ubangiji ya gaya maka cewa kana bukatar hutu a wasu lokatai, kaima.

CIWO DA RAUNI TA JIKI


Wata illa mai tsokano bakin ciki ita ne ciwo da rauni ta jiki. Akwai dalilai da yawa wanda ta sa wannan ta zama haka. Yanayi ta jikinmu tana da iko sosai bisa lafiyar ruhohinmu. Idan ciwo ta jiki ta taba mu, babu wuya mu fadi cikin kasawa ta ruhu ta wurin shakka, tsoro da kuma bakin ciki.

Ciwo ta jiki tana jawo bakin ciki domin babu wuya ta sami shiga ta wurin raguwar karfin mu ta jiki. A wannan lokaci karfinmu ba ta isa mu aikata abin bukata, domin haka babu wuya fidda rai ta sha kanmu. Idan addu’armu ta neman warkasuwa bata sami amsa yadda mu ke zato ba, shakka zata jawo mana fidda rai. Irin wannan hali tana samun shiga sosai idan ciwo tana yawan damun mu a kullum ko kuma idan ciwo ta kwantar da mu na lokaci mai tsawo.

Idan jikinmu ta ki samun daidaitawa daga yadda Allah ya gina ta, wannan za ta jawo bakin ciki. Akwai abin da ya hada ji na ranmu da kuma kayan jikinmu gaba daua. Daya daga cikin dalilan da ya sa wasa ta motsa jiki tana da amfani ta wurin yakan bakin ciki ita ne, motsan jiki tana fitar da wasu ruwa ta jiki mai ba mu jin lafiya ta jiki.Mata masu yawa suna gano wata lokaci a rayuwarsu wanda ke kawo masu duhu mai zuwa da ji iri ta fidda rai. Idan kin iya gane tushen irin wannan rashin daidaitawa ta jiki, kuma kin sani cewa wannan ba abu mai dadewa ba ne, wannan za ta taimakeki ki jimre har zuwa lokacin da za ki ya haske kuma. A irin wadan nan lokaci ki yi da kanki kamar yadda za ki yi da karamin yaro ki dan shakata ki ba na kanki wanka mai ni’ima. Ka da ki karbi wata karin aiki wadda za ta danna maki hutunki. Ki bar mijinki ya kawo maki abinci a wannan lokaci. Kada ki dauki wata mataki da sauri, kuma ki guje musu da tsaguwa idan za ki iya. Karanta wata littafi ki kuma shiga barci da saurci. Babu wuya ta yiwu cewa bayan kin farka sai ki ji cewa wannan nauyi ta bakin ciki ta wuce domin ki sami yin farin ciki a cikin aiki nagarta ta Allah.

Akwai wusu masu shan azaba ta bakin ciki domin irin rashin aiki na wasu ababan jikinsu.. Na yi dan shakka domin ba da wannan dalili, domin wasu na amfani da wannan ta zama hujja a garesu domin kada su furkanci nauyin cutarsu ta ji na jiki. Amma dai idan ka yi bincike ta wurin Ruhu Mai Tsarki a hankali ka kuma ji muryar Allah da wahayinsa, kuma har yanzu bakin ciki na damunka, ka sake bincika ka gano ko akwai wata dalili daga harka ta jikinka mai jawo wannan illa. Ka nemi warkasuwa ta Allah da dukan ranka, idan warkasuwa ta jira, ka karbi taimako daga hannun likita domin maganta wannan kafin Ubangiji ya ba ka cikakken warkasuwansa. Rai madauwami rai ne na farin ciki, kuma Allah yana so kai ka taba dadinsa!




Yüklə 361,5 Kb.

Dostları ilə paylaş:
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©genderi.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

    Ana səhifə