FEDERAL MINISTRY OF HEALTH, NIGERIA
SHIRI NA MUSAMMAN GA MAI KALLO
TAKARDAN BAYANI
TAKAITACEN PASSARA
(MINTI 15)
TAMOWA: ANNOBAR DA TA
ADDABI NIGERIA A BOYE
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE
1
Gudanarwa za ta fara da bakin bango
► Slide 1: Click Forward (a yi shiru yayin da hoto ya fito na tsawon dakika biyar)
► Slide 2: Click Forward (a jira har sai hoton ya dauke)
► Slide 3: Click Forward
Idan muka duba shekarun baya, a Najeriya mun samu ci gaba da dama.
► Slide 4: Click Forward (music starts)
Mutuwar yara yan kasa da shekara biyar ya ragu da kashi ashirin da biyu cikin dari, a alif dari
tara da tamanin, zuwa kashi goma sha uku cikin dari a shekarar dubu biyu da goma sha uku.
Tattalin arzikinmu ya karu ga kowane mutum daya, daga naira dubu dari da hamsin, zuwa
naira dubu dari uku da hamsin, a shekarar dubu biyu da goma sha daya.
Yawan yara mata dake gama karamar makarantar firamare, sun karu da kashi saba’in cikin
dari a shekaru ashirin da suka wuce.
Sannan kuma mun wadata da hanyar sadarwa……. Domin kusan mutane miliyan dari da
goma sha biyar ne suke amfani da wayar salula.
Kasarmu…. na
matukar ci gaba!
Sai dai kuma, akwai wata matsala
daya da ta ke mai da mu baya…….
► Slide 5: Click Forward
….
TAMOWA, wato rashin ingantaccen abinci ga mata da yara qanana na jawowa kasarmu
asara, duk da cewar akwai hanyoyi da dama na warwaresu.
► Slide 6: Click Forward
A yau, tamowa na sanadin macewar yara sama da rabin miliyan ‘yan kasa da shekaru
biyar a
kowace shekara a cikin kasar Nigeria……………. Wato kowane daya daga cikin
mutuwa buyu na tamowa ne.
► Slide 7: Click Forward
Sai mu duba mu gani, wadanne irin darusa ne muka koya a kan tamowa a ‘yan shekarun
nan?
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI
NIGERIA A BOYE
TAKAITACEN PASSARA: MINTI 15
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE
2
► Slide 8: Click Forward
Taimakon na farawa ne tun daga kwanaki dubu daya na farko, wato sanda uwa ke rainon ciki
zuwa yaye…..wannan kwanaki ne ya dace jariri ko jaririya su samu kulawa ta musamman
kafin wani cikin ko haihuwar.
Bari mu duba da kyau don muga mahimmancin wannan lokacin.
► Slide 9: Click Forward
Tun daga mahaifa, dan tayi na cikin hatsari idan har mai cikin bata samu abinci mai gina jiki
ba, ko abinci mai bada kuzari, wanda sune zasu taimakawa ginin kwakwalwa da kashi da
sassan jiki.Rashin isashen abincin yana kawo karancin jini tare da matsala wurin haihuwa
Da zaran an haifi jariri….daga haihuwa zuwa wata shidan farko, a shayar da jariri nonon uwa
zalla, ba tare da bashi wani abinci ba don tabbatar da lafiyar yaro.
Bayan wata shidan farko, karin ingartaccen abinci ga yaro ya zama dole, don tabbatar da
lafiyar jariri yadda ya kamata domin kuwa ciwuka a
wannan tsakanin suke shiga.
► Slide 10: Click Forward
(A dakata sai karan ganga ya wuce)
………….BA GUDU BA JA DA BAYA………
Barnar rashin cimaka mai kyau a kwanakin dubun farko (daga haihuwa zuwa yaye) ba ta
gyaruwa…….
► Slide 11: Click Forward
• Domin tana lalata kwakwalwa, ta mai da yara dakikai, masu raunin fahimta
• Sannan tana hana su girma yadda ya kamata…….
• Bugu da kari, tana haifar musu da munanan cututtuka har zuwa girman su.
► Slide 12: Click Forward
Kamar munanan ciwawuka irin su ciwon siga, hawan jini, da ciwon zuciya, wadanda ke
wahalar da jiki matukar ana raye.
► Slide 13: Click Forward
Wata babban matsalar shine, mafi yawan jama’a basu gane cewa tamowa ga yara na
faruwa har tsawon shekaru
ba tare da an gane ta ba.
Misalin wadannan yaran daga kauye daya suke…..ko za ka iya kwatanta shekarun su?
Duk fa shekarun su daya…….shekarun su takwas-takwas…….amma ka ga akwai banbancia
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE
3
giman jikinsu.
Yaron da ke hagu tsumburarre ne, wanda ke nuna jikinsa bai daidai da shekarunsa ba,
saboda karancin abinci mai kyau. Wannan yaron da wuya ya kamo sauran sa’annin sa
kamar abokin wasan sa da ke dama.
► Slide 14: Click Forward
Cutar tamowa na haifar da salo daban daban da ake gani daga zamani zuwa zamani…….
Misalin illar tamowa daga zamani zuwa zamani…
► Slide 15: Click Forward
…..yana iya farawa daga matar da bata samu cikaken abinci mai gina jiki ba, to tana cikin
hatsari matuka daga lokacin da zata dauki ciki, zuwa yaye. Ga kuma hatsarin haihuwar da
mara kwari.
► Slide 16: Click Forward
…….Kamar wannan yarinyar, wacce ta ke cikin halin rai kwa-kwai mutu kwa-kwai, tare da
hadarin kamuwa da karancin ci gaba da rashin fasaha.
► Slide 17: Click Forward
……..Za ta iya samin nakasu a wajen girmanta da tunanin ta……..wanda…
► Slide 18: Click Forward
…….Kasancewan haka kuwa sai
budurcin ta ya tawaya, domin a wannan locacin ne
kashi hamsin daga cikin dari na kasusuwan jikinta ke girma.
► Slide 19: Click Forward
Kasancewar tamowa da ke jikinta……… kuma, zata dawo kamar wannan matar da ke cikin
taswira.
► Slide 20: Click Forward
Kun ga tamowa ke nan na bibiyar ta tun tsawan zamani zuwa zamani.
► Slide 21: Click Forward
Idan muka duba taswirar kasar Najeriya, zamu fara leka cikin babban birnin Abuja, mu ga
yadda hidimomin su suke. Nan ga babban filin wasan kwallo na gabashin Abuja.
Shigar mu cikin garin, za mu ga akwai ci gaba sosai a cikin ta, wanda har zamu ga cewa
a
nan, samuwar tamowa zai yi wuya saboda Abuja ita ce karfin kasar…… amma a binciken
kwanannan ya nuna cewa a kowane yaro guda daya a cikin yara biyar tsamurarre ne.
TELEPORT
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE
4
Yanzu mu juya zuwa jahar Lagos, mu maida hankalin mu akan unguwar Mushin, wanda take
da tarin jamaa sama da dubu dari biyar. Sun kasance a cakude da junan su, kuma ba tare
da wadata ba…... Tamowa na kusan kowane gida saboda kashi daya bisa uku na yaran
unguwar suna dawke da tamowa.
Duk da talauci na kara yawan tamowa, ba talaka
kadai ke dauke da tamowa ba.
TELEPORT
In muka matsa unguwar Ikoyi, wato unguwar da masu arzikin jihar Legas ke zaune, suna da
manyan gidaje da wadata. Ba wuya mu dauka cewar tamowa ba za ta shiga gidajen su ba
saboda karfin arzikinsu. Ya za a yi a sami Tamowa a irin
wannan wurin. To amma duk da
haka, kashi goma sha uku bisa dari na yaran masu
arziki a wannan unguwan suna dauke
da cutar tamowa.
TELEPORT
A ci gaba da tafiyar mu, mun fahimci cewa ba wani bangare a cikin kasar nan da Tamowa
bata shafa ba.
TELEPORT
Gamu a jihar Niger Delta, jiha mai arzikin man fetur….. Sana’ar su ita ce kamun kifi da
noma don su sama wa kansu abinci mai gina jiki. Amma wannan bai sa jihar ta wadatu da
ingantaccen abinci ba.
Cutar tamowa babbar matsala ce ga yaran Jihar Delta, saboda kowane yaro daya daga
cikin yara biyar na dauke da ita.
TELEPORT
A karshe kuma, mun gano cewa cutar tamowa tana nan a wuraren da noma itace sana’ar
da suka dogara da ita.
Kaman a nan, arewacin najeriya, kusan noma ita ce babar sana’ar su, a dalilin hakan, suna
samun wadatacen abinci na tsawon shekara, har su bawa makotan su ba tare da gazawa
ba. Haka zalika abinci mai gina jiki baya yanke musu. Amma duk da haka, sai da tamowa ta
sami wajen zama a yakin.
(A dakata)
Abin takaici ne yanda tun shekarun baya, har izuwa yanzu, ba a samu cikakiyar ci gaba, don
hana yaduwar cutar tamowa ba.
► Slide 22: Click Forward
Ka duba ka gani tun shekaru goma da suka wuce……….
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE
5
► Slide 23: Click Forward
…….Bincike ya nuna cewa ba a samu kwakkwaran ci gaba ba a harkar yaki da cutar tamowa
ba. Amma binciken shekara dubu biyu da goma sha uku ya nuna an
dan sami cigaba kadan
da ba a rasa ba…
► Slide 24: Click Forward
….Duk da haka dai, sama da kashi daya bisa uku na yaran kasar nan tsumburarru ne.
► Slide 25: Click Forward (MAP)
Kamar yanda muka gani a cikin taswira, wadda ta nuna mana misalin yaduwar tamowa a
cikin kasar mu, babban bangaren ma da ake ganin bata da yawa sosai, a kowane yara biyar
zakaga akwai guda daya wanda ke dauke da ita,wato a kudu maso kudu da kuma kudu
maso yamma. A arewa maso gabas kuwa, kusan
RABIN yaran suna da matsananciyar
tamowa.
► Slide 26: Click forward
Hukumar samar da lafiya ta majalisar dinkin duniya ta jaddada mahimmancin ba wa jarirai
abinci mai nauyi mai gina jiki bayan wata shidan farko don samun cikakkiyar kariya daga
cututtuka………
► Slide 27: Click Forward
Amma bincike ya nuna cewa jarirai biyu cikin uku ba sa samun cin abincin daya dace.
19
Mafi
yawa suna samun abinci ne mai danko ne, irin su rogo da shinkafa a maimakon ‘ya’yan
marmari irin su ganyaye da nama da kifi da kwai -wanda zai gina musu jiki.
► Slide 28: Click Forward (TRENDALYZER)
Don mu ga masu samun cikakken nonon uwa a Najeriya, muna iya kwatanta Najeriyya da
kasar Ghana.
► Slide 29: Click Forward
A ta bangaren hagu, muna da lissafin jarirai yan kasa da wata shida masu samun nonon uwa
zalla. Wanda kason ya taso daga sifili zuwa kashi tamanin bisa dari.
► Slide 30: Click Forward
A bangaren kasa kuwa, akwai lissafin lokaci, daga Alif dubu daya da dari tara da casa’in da
hudu zuwa shekarar dubu biyu da goma sha uku.
► Slide 31: Click Forward
Mu lura cewa a shekarar Alif dubu daya da dari tara da casa’in da hudu a Nigeria da Ghana
suna da kashi bakwai bakwai cikin dari na yawan jarirai masu samun nonon uwa zalla.
In mu kai ta tafiya, mu duba abin da ya faru tsawon lokaci a kowace kasa….zamu ga
cewa…..kason…
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE
6
► Slide 32: Click Forward
…..jariran da ke samun nonon uwa zalla a kasar Ghana kullum habaka ya ke…… yana
sama….yana kara sama…
► Slide 33: Click Forward
…..Har sai da ya kai ga cewa, kashi sittin da uku na jarirai, ko kusan kasha biyu cikin uku na
jariran da ke Ghana, na samun cikakken nonon uwa a shekarar dubu biyu da goma sha uku.
► Slide 34: Click Forward
…..Sabanin a Najeriya, wanda kashi goma sha bakwai ne kawai (wato kowane daya daga
cikin shida) ke samun cikakken nonon uwa.
(A dakata)
Ko me kasar Ghana tayi data samiwannan ci gabar?
To…tun farkon shekarar dubu daya da dari tara da casa’in, suka kirkiri dokoki, tare da
hadin kan mutanen gari, da karin kayan aiki don a shayar da yara nonon uwa zalla.
In da Najeriya zata kara fadin shirin ta, ta fadada dokokin ta da tsarin ta, kuma ta fifita
shayar da yara nonon uwa zalla,
muma da mun sami ci gaba a kasarmu.
(A dakata)
Mun san za mu iya hakan saboda…….
► Slide 35: Click Forward
Mun
san abubuwan da zasu iya kawo mana canji!
Idan aka jarraba abubuwa hudun nan, za su iya zama kariya ga uwaye da jarirai…………Na
farko shine……..
► Slide 36: Click Forward
Bada nonon uwa cikin minti talatin daga lokacin da aka haifi jariri, sannan a cigaba da bada
nonon uwa zalla har na tsawon wata shida
ba tare da ba jariri ko digon ruwa daya ba.
(A dakata)
► Slide 37: Click Forward
……Na biyu kuwa shine za a tabbatar da bawa jariri nau’in abinci mai gina jiki bayan wata
shidan farko, tare da ci gaba da bashi nonon uwa har tsawon shekaru biyu.
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE
7
► Slide 38: Click Forward
Na uku shine, a tabbatar da cewa uwa da jaririnta na samun isasshen abinci, wanda zai
wadace su……….
► Slide 39: Click Forward
…….. abinci ingantacce ……sannan iri daban-daban.
► Slide 40: Click Forward
Domin iyali su kasance suna samin wadataccen abinci mai gina jiki, a ko da yaushe.
► Slide 41: Click Forward
A takaice dai yana da kyau iyaye mata da sauran ma su kulada jarirai su ringa samun bayanai
akan yadda za su shayar da jarirai dan samun cikakkiyar lafiya.
(A dakata)
► Slide 42: Click Forward
Bincike ya nuna mana cewar cimaka mai kyau “tafi kowace sana’a sayuwa” a harkakokin
kasarmu……..saboda sana’ar cimaka mai kyaw mai da kudi gida ne.
► Slide 43: Click Forward
Cimaka mai gina jiki a kwana dubun farko na haihuwa takan samar da amfani mai yawan
gaske ga iyali da kasa baki daya. [Kamar wannan nagartacen dan wasan kwallon!!]
► Slide 44: Click Forward
Lafiyayyun yara sukan fi gama makaranta da kyakkyawan sakamako, domin haka yawan
samin su yakan ninka da kashi goma cikin dari fiye da wadan da ba a kula dasu ba.
► Slide 45: Click Forward
Tunda lafiyayyan abinci a kwana dubu na haihuwa ya na kara kwazon yara a makarantu,
yaron da aka lura da shi har ya girma yakan zama fitacce…….hakan na iya samun cigaban
tattalin arzikin kasa har ninki goma sha daya cikin dari a kowace shekara.
► Slide 46: Click Forward
Ko nawa aka ware don samar da abinci mai gina jiki ga al’umar kasa bai yi tsada ba- don
amfanin da ke cikin ta zai ba da kyakkyawan sakamako.-wato a sa jari a harkokin samar da
cimaka yakan ninninka riba har ta fi uwar kudin da aka zuba da kashi
ashirin da biyar.
► Slide 47: Click Forward
Kun ga ke nan kowace naira dubu dari da aka ware wajen samar da abinci mai gina
jiki………….
► Slide 48: Click Forward
……Zata ba da ribar kwatankwacin Naira maliyan biyu da rabi wajen bunkasa tattalin arzikin
kasa.
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE
8
► Slide 49: Click Forward
Tamowa Annobar kasa ce gaba daya………..
…………………………….saboda haka, samo mafitar ta ma, sai an hada hannu gaba daya.
(A dakata)
► Slide 50: Click Forward
Mu na da hujjoji………….. na irin abubuwan da zasu iya kawo mana canji.
► Slide 51: Click Forward
Muna neman ku magantu da yin kira wajen rage cutar tamowa
……sannan ku ja hankalin al’umma da gaggawa da su dunfari abinci mai gina jiki musamman
mata ma su ciki da yara kanana….. sannan muna kira da ku sa ido a kan iyaye mata don
tabbatar da shayar da jarirai nonon uwa har iya tsawon lokacin da ya dace.
► Slide 52: Click Forward
Muna dada rokon al’umma da su tashi tsaye wajen tabbatar da cewa an habbaka cinikin
cimaka mai gina jiki a kowane bangare na maaikatunkasan nan da ma su zaman kansu,
kamar ma’aikatar kudi,da ta tsare-tsare,da ta gona,da ta ilimi,da ta harkokin mata, da ta
muhalli dama ta ruwa.
► Slide 53: Click Forward
Muna dada rokon hukumomi su kara hada hannu dan tsai da mafita a kan abinci mai gina
jiki a maaikatu…….musamman maaikatun kudi, da na tsare tsare, da na noma, da na ilimi,
da na harkokin mata, da na mahalli, da na ruwa.
► Slide 54: Click Forward
A karshe mu na dada rokon da a agaza mana da karin tallafi....wato,
zai yi kyau a sami
kasafin kudi na MUSAMMAN a asusun maaikatar lafiya, da na gona, da kuma asusun
jihohi gaba daya, domin biya wa bukatar kawar da wannan annoba ta tamowa.
Ba zai yiwu mu rasa
duk wadannan damarmakin da mu ke da su ba.
► Slide 55: Click Forward
In da za mu saka jari akan cimaka mai gina jiki….
► Slide 56: Click Forward
• Za mu iya tabbatar da cewa yaran mu sun yi kwari sun kai gaci…….
• Mu kuma rage yaduwar cututt ikin mu ya habaka a gaba.
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE
9
► Slide 57: Click Forward
Inda zamu taru mu hada karfi da karfe……..
(A dakata har sai wasu jerin kalmomi sun fito)
…. Zamu iya
cimma burinmu nan gaba akan ayyukan mu na baya
(A dakata har sai wani jerin kalmomi sun fito)
Zamu iya
tsayar da annobar tamowar da ta mamaye mu……
Zamu agazawa masu bukatar taimako…...
(A dakata har sai wani jerin kalmomi sun fito)
Za mu iya
kawar da annobar tamowa daga doron Nigeria baki daya.
► Slide 58: Click Forward
(A tsaya shiru)
TAMOWA: ANNOBAR DA TA ADDABI NIGERIA A BOYE
10
REFERENCES
1 World Bank, “Data Bank,” accessed at http://data.worldbank.
org/indicator/SH.DYN.MORT?page=6, on Nov. 10, 2014;
and National Population Commission of Nigeria and ICF
International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013
(Abuja, Nigeria, and Rockville, MD: and ICF International, 2014).
2 Index Mundi, “Nigeria: GNI per Capita,” accessed at: www.
indexmundi.com/facts/nigeria/gni-per-capita, on Nov. 10, 2014.
The latest value for GNI per capita, PPP (current international $)
in Nigeria was 2,290.00 as of 2011.
3 Nigeria Communications Commission, “Subscriber
Database,” for year 2012/2013: 113,195,951 active users;
accessed at: www.ncc.gov.ng/index.php?option=com_
content&view=article&id=125:art-statistics-subscriber-
data&catid=65:cat-web-statistics&Itemid=73, on Nov. 10, 2014.
4 Population Reference Bureau calculation based on birth data
from: United Nations, World Population Prospects: The 2012
Revision (New York: UN, 2013); and on the under-5 mortality
rate from the National Population Commission of Nigeria and
ICF International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013.
5 1,000 Days Partnership, “Why 1000 Days” (2013), accessed at
www.thousanddays.org/about/, on March 10, 2014.
6 Cesar G. Victoria et al., “Maternal and Child Undernutrition:
Consequences for Adult Health and Human Capital,” Lancet
371, no. 9609 (2008): 340-57.
7 United Nations Standing Committee on Nutrition (UNSCN), 6th
Report on the World Nutrition Situation: Progress in Nutrition
(Geneva: UNSCN Secretariat, 2010).
8 Bonnie A. Spear, “Adolescent Growth and Development,”
Journal of the American Dietetic Association 201, no 3,
supplement (2002): S23-29; Alan D. Rogol, Pamela A. Clark,
and James N. Roemmich, “Growth and Pubertal Development
in Children and Adolescents: Effects of Diet and Physical
Activity,” The American Journal of Clinical Nutrition 72, no. 2
(2000): 521S-28S; and FAO/WHO/UNU, Energy and Protein
Requirements: Report of a Joint FAO/WHO/UNU Expert
Consultation (Geneva, WHO, 2001).
9 National Population Commission of Nigeria and ICF
International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013.
10 R.O. Abidoye and N.N. Ihebuzor, “Assessment of Nutritional
Status Using Anthropometric Methods on 1-4 Year Old
Children in an Urban Ghetto in Lagos, Nigeria,” Nutrition and
Health 15, no.1 (2001): 29-39.
11 Nigeria National Bureau of Statistics, United Nations Children’s
Fund, and United Nations Population Fund, Nigeria Multiple
Indicator Cluster Survey 2011 (Geneva: Unicef, 2013).
12 National Population Commission of Nigeria and ICF
International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013.
13 National Population Commission of Nigeria and ORC Macro,
Nigeria Demographic and Health Survey, 2003 (Calverton,
MD: ORC Macro, 2004); National Population Commission
of Nigeria and ICF Macro, Nigeria Demographic and Health
Survey 2008 (Calverton, MD: ICF Macro, 2009); and National
Population Commission of Nigeria and ICF International, Nigeria
Demographic and Health Survey 2013.
14 National Population Commission of Nigeria and ICF
International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013.
15 National Population Commission of Nigeria and ICF
International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013.
16 World Health Organization, “Essential Nutrition Actions, 2013,”
accessed at www.who.int/elena/titles/complementary_feeding/
en/, on Nov. 10, 2014.
17 National Population Commission of Nigeria and ICF Macro,
Nigeria Demographic and Health Survey 2008.
18 Ghana Statistical Service, Ghana Health Service, and ICF
Macro, Ghana Demographic and Health Survey 2008
(Calverton, MD: ICF Macro, 2009).
19 National Population Commission of Nigeria and ICF
International, Nigeria Demographic and Health Survey 2013.
20 Scaling Up Nutrition, A Framework for Action (Washington, DC:
BMGF, the Government of Japan, and the World Bank, 2010),
accessed at www.unscn.org/files/Announcements/Scaling_Up_
Nutrition-A_Framework_for_Action.pdf, on May 10, 2014.
21 World Bank, Repositioning Nutrition as Central to Development:
A Strategy for Large-Scale Action (Washington, DC: World
Bank, 2006).
22 Sue Horton and Richard H. Steckel, “Malnutrition: Global
Economic Losses Attributable to Malnutrition 1900-2000 and
Projections to 2050,” in How Much Have Global Problems Cost
the World? A Scorecard from 1900 to 2050, ed. Bjorn Lomborg
(Cambridge, UK: Cambridge University Press, 2013).
23 John Hoddinott et al., “The Economic Rationale for Investing
in Stunting Reduction,” Maternal & Child Nutrition 9, no. S2
(2013): 69-82.
Dostları ilə paylaş: |