Tarihin Ahlul Baiti A



Yüklə 296,5 Kb.
səhifə2/3
tarix17.09.2018
ölçüsü296,5 Kb.
#68718
1   2   3

Kashi na farko: Su ne waxanda su ke tauye haqqensu, ba su kuma qaunarsu balai girmama su kamar 'yan Ibbadiyyah da su ka kauce ma wasicin Manzon Allah (SAW) akan su. Waxannan ba su da wata alaqa da Ahlus Sunnah sam.

Kashi na biyu: Su ne waxanda su ka faifaye a wajen sonsu har su ka wuce makaxi da rawa, ya kasance sun mayar da su kamar su ma manzanni ne, ko wani lokaci ma su allantar da su. Sai su na ta bada labaran qarya akan su wai don su ja hankalin wawaye da marasa ilmi zuwa ga shirmensu.

Shugabannin Ahlulbaiti kuwa tuni su ka yi Allah waddai da irin wannan so na hauka kamar yadda Ali binul Hussaini Zainul Abidin ya ke cewa, Ya ku mutane! Ku rinqa yi mana so irin na musulunci. A yanzu irin son da ku ke mana ya zama abinkunya akanmu.31



Kashi na Uku: Su ne tsaka tsaki, waxanda su ka tabbatar cewa, su dai Ahlulbaiti bayin Allah ne waxanda su ke kamar sauran mutane ta fuskar wajabcin bin Shari'ah da sauran abin da ya shafi 'yan adam na yanayin halitta, amma kuma Allah ya ba su wata daraja wadda ta samo asali daga kusancinsu da Manzon Allah (SAW). Don haka su kace a basu haqqensu.

Sanin haqqen Ahlulbaiti da ba su waxannan haqqoqin wajibi ne tabbatacce a Shari'ah.32 Don haka, ya kai musulmi, ka nemi sanin waxannan haqqoqi ka tsayar da su ban da wuce iyaka. Ka sani duk wanda ya kauce ma hanyar tsakiya zai halaka.

Allah ya yi muna dace da bin hanya madaidaiciya da tsarin tafiya miqaqqe.
FASALI NA XAYA

Wane ne Zainul Abidin?

Sunansa da Haifuwarsa

Sunansa Ali binul Hussain bin Ali bin Abi Xalib Al Hashimi Al Qurashi wanda aka fi sani da Zainul Abidin. Ana kuma ce da shi Baban Hassan.

Jikan Manzon Allah (SAW) ne ta wajen 'yarsa Fatimah Az Zahra'u (RA). Wannan dangantaka kuwa ta isa wajen xaukaka da daraja.

Mahaifiyarsa ita ce Salamatu, wasu masana kuma sunce sunanta Gazalatu. Amma 'yar Farisa ce ko 'yar qasar sindi ce? Wannan shi ne abin da masana su ka qari junansu sani akansa. Abin da aka tabbatar dai shi ne Ummu walada33 ce ga mahaifinsa.

Ibnu Khillikan ya karkata ga ra'ayin farko, cewa mahaifiyarsa bafarisa ce, har ma yace, ana yi ma sa laqabi da "Ibnul Khairataini", xan mafifita biyu domin an ruwaito cewa, Allah ya na da zavavvu biyu, zavavvunsa a larabawa su ne Quraishawa, a ajamawa kuwa su ne Farisawa. 34

Zamakhshari kuma cewa yayyi, Yazdajrid, Sarkin qarshe na Farisa ya na da 'ya'ya mata da aka kama su a zamanin sarki Umar xan khaxxabi, ta farkon ita ce aka bai wa Abdullahi xan Umar ta haifa masa Salim, ta biyu aka bai wa Muhammad binu Abi bakr ta haifa ma sa Qasim, ta ukun kuwa aka bai wa Hussaini bin Ali sai ta haifa ma sa Zainul Abidin, su ukun (Salim da Qasim da Zainul Abidin) kakansu xaya ne ta wajen iyayensu mata.35

Har wayau game da lokacin da aka kama ta, masana sun yi savani, ko lokacin khalifa Umar ne ko Usman.36 To, ko wanne ne dai ya nuna yadda shugabannin Ahlulbaiti su ka yarda da waxannan khalifofi, su ka amince da ingancin jihadinsu da ganimomin da su ka samo. Ba don haka ba da Ali da 'ya'yansa ba su karvi ganimar har su ka haifar da waxannan 'ya'ya ba.37

Ya'qub binu Sufyan yace, an haifi Ali binul Hussain a shekara ta 33 B.H.38

Amma a cewar Dhahabi ana zaton an haife shi ne a shekarar 38 B.H.39 Wannan ra'ayin kuwa ya fi qarfi domin tarihi ya tabbatar da cewa, a lokacin da aka yi waqi'ar karbala' ya na da shekaru 23 ne.40 Ita kuma waqi'ar karbala' ta faru a shekara ta 61 B.H. ne ba savani.41


FASALI NA BIYU

Jihadinsa Da Yadda Ya Kuvuta A Karbala'

A cikin tarihi ba za ka tava karanta labari mai muni da tashin hankali ba kamar na Karbala'. Labari ne da ke tsage zuciya ya tsima jiki ya sanya ido zubar da hawaye. Ba don kome ba sai don zuri'ar Manzon Allah (SAW) da su ka gamu da ajalinsu a wannan karafkiya. Hussaini da akasarin iyalansa sun rasa rayukansu a wannan rana. Allah ya xaukake su da samun shahada don ya xaukaka darajarsu da matsayinsu a aljanna. Kusan ana iya cewa, ba wanda ya kuvuta daga cikinsu sai xansa Zainul Abidin wanda mu ke ba da tarihinsa a cikin wannan littafi. Shi ma ya yi saura ne a dalilin rashin lafiyarsa.

Malam Ibnu Sa'ad yace, Ali binul Hussaini ya kasance tare da mahaifinsa ya na da shekaru 23, amma a lokacin da aka zo Karbala' shi ba ya da lafiya, ya na kwance akan shimfixarsa. Bayan ma da aka kashe mahaifinsa Hussaini sai da Shamr binu Dhil Jaushan yace a kashe shi, amma wani mutum yace, don me za a kashe shi tun da bai yaqi kowa ba? Da Umar binu Sa'ad yazo sai yace, kar a kashe mata kar kuma a kashe wannan maras lafiya.42

Allah Sarki! Haka dai zamu ga wannan bawan Allah ya fito da cikakken shirinsa na yin yaqi tare da mahaifinsa amma Allah cikin ikonsa da ya ke ya nufi wanzuwar zuri'ar Hussaini sai ya kawo sanadin rashin lafiya wanda ya zama dalilin rashin mutuwarsa. In ban da vangarensa kuwa babu in da Sayyiduna Hussaini ya bar wata zuri'a wadda ta haxa jini da Manzon Allah (SAW) ta gefensa.

Malam Asma'i yace, Hussaini bai bar wata zuri'a ba sai ta wajen Ali binul Hussaini, shi kuma Ali bai bar wata zuri'a ba sai ta wajen matarsa kuma 'yar baffansa Ummu Abdillahi bintul Hassan.43


FASALI NA UKU

Yabon da Mutane su kayi ma sa

Mutane su ne shedun Allah a bayan qasa. Duk musulmin da ka ga jama'a su nai ma sa kyakkyawan ambato da yabawa akansa ka tabbata ya na da rabo a wurin Allah kuma Allah ya na sonsa. A game da wannan bawan Allah kuwa Zainul Abidin shi sha yabo ne a wurin malamai. Wannan ko ita ce bushara ta farko ga mummuni.

Imam Malik ya na cewa, duk a gidan su Zainul abidin babu irinsa.44

Malam Zuhri kuwa, wanda shi ne malamin Malik cewa yayyi, ban tava ganin baquraishen da ya kai tsentseni da daraja irinsa ba.45

Malam Zirru binu Hubaish yace, Na kasance a wurin Ibnu Abbas sai Ali binul Hussaini yazo, Ibnu abbas ya yi ma sa maraba ya na mai cewa, maraba da masoyi xan masoyi.46

A lokacin da Hisham binu Abdil malik ya yi aikin hajji a khalifancin babansa tare da xan uwansa Walid yaje ya yi xawafi sai ya nufaci Hajarul Aswad don ya sumbace shi amma abin bai yiwu ba sai da aka kafa masa wani dandamali wanda ya hau akansa sannan ya sumbaci dutsen saboda cinkoso. Bayan haka ne sai mutanen Sham, hedikwatar mulki ta wannan lokaci su ka kewaye shi su na yi masa fadanci. Ana haka ne sai ya hangi Ali binul Hussaini ya gabato. A lokacin da ya kusanci dutsen sai duk mutane su ka janye ma sa aka ba shi dama ya sumbace shi don girmamawa, ga shi kuwa ya fito a cikin wata siffa mai kwarjini da ban sha'awa. Nan take sai mutanen Sham su ka ce masa, wai wane ne wancan? Sai yace, ban san shi ba, don kar ya jawo hankalinsu zuwa ga reshi. Sai mawaqin nan Firazdaq yace, ai ni na san shi, ku bari in ba ku labarinsa. Anan ne ya yi waqen nan nasa mai ban shawa in da ya wasa Zainul Abidin har sai da yarima Hisham yaji kunya shi da yace ban san shi ba.47

Malam Waqidi yace, Zainul Abidin na daga mafi tsentsenin mutane, mafi ibadarsu, kuma mafi tsoron Allansu.48

Malam Dhahabi kuwa ga abin da yace, Zainul Abidin ya na da kwarjini mai ban mamaki, kuma na rantse shi mai cancanta ne ga reshi. Tabbas ya dace da sarauta domin girmansa da matsayinsa da ilminsa da kammalar hankalinsa.49

A taqaice wannan shi ne matsayin malamai na kirki akan wannan bawan Allah wanda xaya ne daga shugabannin iyalan gidan annabta. Su na sonsa, su na darajanta shi, su na yawaita yabo akansa, uwa uba kuma su na goyon bayansa da koyi da shi. Wannan ita ce aqidarmu Ahlus Sunnah game da duk iyalan Manzon Allah (SAW) wadda mu ke fatar Allah ya rayar da mu akanta, ya karvi rayukanmu akanta.


FASALI NA HUXU

Yawan Ibadarsa da qanqan da kansa ga Ubangiji

Dukkanmu mu na son kasancewa cikin xa'ar Allah, mu na sha'awar mu yawaita bautarsa da nau'oi na bauta da ya ke son a bautata ma sa da su. Amma nan take mun samu cikas da kasala saboda tasirin kwaxayinmu da bin son rayukanmu. Don haka ne mu ke da buqatar hanyoyin da za su taimaka mana wajen dagewa akan xa'a da bautar Allah maxaukakin Sarki. Daga cikin hanyoyin da za mu cimma wannan kuwa har da karanta tarihin magabata daga malaman farko waxanda rayuwarsu ta kasance tutur a cikin ibada kamar Zainul Abidin binul Hussain bin Ali. Ga kaxan daga cikin ababen koyi a rayuwarsa;


Sallarsa da yawan addu'arsa

Imam Malik yace, Na samu labarin cewa, Zainul Abidin ya na sallah raka'a dubu a tsakanin kowane dare da wuni har Allah ya karvi ransa.50 Yace, a dalilin yawan ibadarsa ne ma ake ma sa wannan suna Zainul Abidin, qawar masu bauta.51

Ja'afar binu Muhammad ya karvo daga babansa cewa, Ali binul Hussaini ya kasance ba ya barin qiyamul laili a tafiya ya ke ko a zaman gida.52

Shi ma Umar bin Ali abin da yace shi ne, Ali binul Hussaini ya kasance idan ya samu fargaba akan wani abu ya kan yawaita du'ai.53

Malam Xawus shi kuma cewa yayyi, Na ga Ali binul Hussaini ya na sujada a cikin Hijr, sai nace, wannan wani bawan Allah ne daga cikin iyalan tsarkakakken gida don haka bari inji abin da ya ke faxi. Sai na kusance shi naji ya na cewa, Ya Allah! Ga xan bawanka nan a bakin qofa, Ya Allah almajirinka ne a bakin qofa, Ya Allah talakanka ne a bakin qofa, Ya Allah! Miskininka ne a bakin qofa. Tun daga lokacin ni kuma na rinqa faxin irin hakan idan na shiga wani hali na qunci sai Allah ya kuranye min.54

Ko ka lura da yadda Ahlulbaiti su ke qanqan da kansu ga maxaukakin sarki? Su ba Allah ne ba, ba su iya amfanar da wani ko su cutar da shi. Su ma ta kansu su ke yi. Koma ga Allah ka huta da yaye yaye.


Yadda ya ke tsoron Allah da dogaro ga reshi

Duk wanda ya fahimci qasqantar duniya, ya gane girman alqiyama ba zai mayar da hankalinsa ga duniyar ba. Idan mutum ya daxa zurfafawa a wannan tunani ko abokin zama ba shi buqata. Wane irin daxi mutum zai ji idan ya tuna qabari ne makomarsa, kuma mala'ikan mutuwa na jiransa? Idan mutum ya na tuna ni'imar aljanna da azabar wuta wane daxin duniya ya ke buqata? Irin wannan shi ne tunanin Zainul Abidin a game da duniya. Duk abin da ke cikinta abin lura ne a gurinsa, ko wane shiru ko motsi wa'azi ne a ga reshi.

Abu Nuh Al Ansari ya faxi cewa, an yi gobara a wani gida da Ali binul Hussaini ya ke a cikinsa ya na sallah, aka yi dai dai kuwa ya na sujada, sai su ka rinqa cewa, Ya kai jikan Manzon Allah hattara da wuta! Amma bai xaga kansa ba har in da aka kashe wutar. Daga baya sai aka tambaye shi, yace, wutar da fi ta ce ta xauke hankalinsa, ya na nufin wutar jahannama. Allah ya kiyaye mu.55

Abdullahi binu Ja'afar Al Qurashi yace, idan Ali binul Hussaini ya yi alwalla fuskarsa ta kan canza, in aka tambaye shi sai ya kan ce, kun san ko a gaban waye zan tsaya?56

A ruwayar Sufyan binu Uyainah Ali binul Hussaini ya yi aikin hajji sai da ya yi harama ya hau dabbarsa sai yanayinsa ya canza, jikinsa ya rinqa vari ya na makarkata har ya kasa yin Labbaika. Anan ne mutane su ka tambaye shi me ya same ka? Sai yace, ina tsoron ince "Labbaika", na karva kiranka ya Allah, ace min "La Labbaika" ba a karvi kiranka ba. Sai aka ce masa, to, ai dole ne kace hakanan. A yayin da ya faxi hakan sai suma ya kama shi har ya faxo daga kan taguwarsa. Daga nan aka rinqa ganinsa a cikin wani yanayi har in da ya qare hajjinsa.57

Karimcinsa da yawan sadaqarsa

Abu Hamzah As Sumali ya bada labarin cewa, Ali binul Hussaini ya kan xauki gurasa akansa ya zagaya ya na raba ta a gidajen matalauta cikin duhun dare. Ya kance, ina yin haka ne domin sadaka a cikin duhun dare ta na bice fushin ubangiji.58

Xansa Abu Ja'afar ya faxi cewa, sau biyu baban nasa ya na raba dukiyarsa biyu ya yi sadaka da kashi xaya.59

Kuma idan zai bai wa miskini sadaka sai ya sumbace shi, ya nuna masa qauna sannan ya ba shi kamar yadda Abul Minhal Ax Xa'i ya ruwaito.60

An karvo daga Ja'afar binu Muhammad daga babansa cewa, Ali binul Hussaini ya kasance idan almajiri yazo masa ya kan yi maraba da shi ya na cewa, na yi murnar zuwan wanda zai xauki guzurina zuwa lahira.61

Wannan shi ne kai matuqa ga karimci. Mutum ya na sadaka kuma ya na ganin wanda zai karvi sadakar ya taimake shi? Irin waxannan mutane a yau sai dai mu karanta labarinsu a littafi, in ko har an gansu to, ba su wuce waxanda za a qirga ba. Muna roqon Allah ya yi muna dace.

Shaibah binu Nu'amah yace, mutane da yawa sun xauki Ali binul Hussaini marowaci ne, sai da ya rasu aka sami sama da gidaje xari waxanda ya ke xaukar nauyinsu.62

Malam Dhahabi yace, an xauki ya na rowa ne saboda ba ya yin sadaka a fili, a asirce yake yi sai a xauka shi marowaci ne tara kuxin yake yi.63

Muhammad binu Ishaq yace, Wasu mutane a Madina sun kasance su na rayuwa ba su san ta in da abincinsu yake zo mu su ba. A lokacin da Ali binul Hussaini ya cika sai su ka rasa abincin da ya ke zo mu su da dare. Masu yi ma sa wanka kuwa sai su ka ganshi da wasu alamomi a kafaxunsa da kuma akan bayansa saboda xaukar buhunan abinci da ya ke yi a cikin dare zuwa gidajen talakawa.64

Sufyan ya ba da labarin cewa, lokacin da Ali binul Hussaini ya nufi aikin hajji ko kuma Umrah, qanwarsa Sukainah bintul Hussaini ta aika ma sa da wata jaka mai xauke da kuxi kusan Dirhami 1000. A lokacin da ya kai wajen da ake kira Harrah sai ya yi umurni duk aka raba kuxin a tsakanin talakawa.65

Amru binu Dinar shi kuma ya ruwaito cewa, Ali binul Hussaini ya kai ziyara wurin Muhammad binu Usamah a lokacin rashin lafiyarsa, sai Muhammad ya rinqa kuka. Ali ya tambaye shi, me ka ke ma kuka? Sai yace, bashi ake bi na. Yace, har nawa ne hala? Yace, sama da Dinari 10,000 ne. Sai yace, to, ni zan biya.66
FASALI NA BIYAR

Tarin Ilminsa

Abdur Rahman binu Adrak yace, Ali binul Hussaini ya kasance ya kan shiga masallaci sai ya keta sahu don yaje wurin karatun Zaid binu Aslam. Sai Nafi'u binu Jubair yace masa, Allah ya taimake ka! Me ya sa kake ratsa jama'a don kaje wurin wannan bawa kayi karatu ga shi kuwa kai babban mutum ne a cikin mutane? Ali binul Hussaini sai yace, ai shi ilmi duk in da ya ke nemansa ake kuma can ake samunsa.67

Malam Zuhri yace, Na faxa Ali binul Hussaini wani hadisi, a lokacin da na qare faxa masa sai yace, ma sha Allahu! Ka kyautata, haka ne mu ma aka bamu labarinsa. Sai nace, to, ai ba wani abu ba ne face na faxa maka hadisin da ka fi ni saninsa. Sai yace, af! Ai duk karatun da ba a sani ba ba ilmi ba ne. Ilmi shi ne karatun da aka sani, harsunan malamai su ka yi ta bita akansa.68

To, ina masu ganin sun kevanta da wani sani koma bayan jama'a?

Ina 'ya'yan malam masu qaryar sani su na cika mutane da surrutu da labaran qarya don ace su ma malamai ne?

Ina masu qishirwar wa'azi waxanda duk in da suka zauna sai sun fesa qarya akan Manzon Allah (SAW) wai su suna kawo hadissansa? Sai su na tsinto ababen tausayi da ban mamaki daga cikin hadissan qarya don su burge mutane!

Duk waxannan sai su ji tsoron Allah. Ga maganar Zainul Abidin nan don su gane me nene ilmi? Ilmi shi ne karatun da aka sani, harsunan malamai su ka yi ta bita akansa.

Zainul Abidin dai masanin hadisi ne. Ya karanci hadisi a wurin malamansa daga cikin sahabbai kamar mahaifinsa Al Hussaini da baffansa kuma surukinsa Al Hassan, da iyayen mummunai Nana Safiyyah, Nana A'ishah, da Nana Ummu Salmah. Haka ma ya yi karatu wurin Abu Hurairah da Abu Rafi' dukkansu daga cikin almajiran Manzon Allah (SAW).69

Ko kana ganin malaman nasa ba na kirki ne ba? Sake nazari dai ka gani.

FASALI NA SHIDA

Kulawarsa da tsarkake zuciya

Lafiyar zuciya ita ce lafiyar sauran jiki kamar yadda cutarta ita ce rashin lafiyar jikin shi kansa. Don haka ne ma maxaukakin sarki ya keve ta ambato a tsakanin sauran gavvai in da ya ke cewa,


يَوْمَ لَا يَنْفَعُ مَالٌ وَلَا بَنُونَ (88) إِلَّا مَنْ أَتَى اللَّهَ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ (89) الشعراء: 88-89
Ma'ana:

Ranar da dukiya ba ta amfani, haka ma 'ya'ya (Ba su amfani). Sai dai wanda yazo da zuciya lafiyayya.

Lafiyayyar zuciya ita ce wadda ba son bidi'a ko savon Allah a cikinta. Ita ce wadda ba da cuta ko aibi a tare da ita kamar qyashi ko hassada ko taurin kai ko makamantansu. Don haka ne magabata su ka yawaita mayar da hankulansu ga ayyukan zukata domin su kyautata alaqarsu da mahalicci mai girmama da xaukaka. Ga wasu 'yan misalai daga rayuwar wannan bawan Allah;

Tawali'unsa:

An karvo daga Abdullahi binu Abi Sulaiman yace, Ali binul Hussaini ya kasance idan ya na tafiya ba ya taqama, hannayensa ma ba su wuce cinyarsa.70

Ja'afar binu Muhammad shi kuma yace, Ali binul Hussaini ya kasance idan ya na tafiya a kan alfadarinsa cikin qananan hanyoyin Madina bai ce ma mutane gafara dai, ya na ganin hanya ta kowa ce, dole ne abar kowa ya tafi yadda ya ke so.71

Xansa Ja'afar binu Muhammad ya gamu da wasu baqi sai su ka rinqa wasa shi su na yaba masa, sai yace, ai idan mun kasance cikin na kirki ma ya ishe mu.72

Wannan ita ce hanya mafi kyau wajen karya girman kai, mutum ya nisantar da kansa daga qaunar a yabe shi, kamar yadda magabatan farko su keyi su na qyamar a yaba ma su don gudun Allah ya yi fushi da su ko ya qyamace su idan ba hakanan su ke ba a wurinsa. Allah Ta'ala kuwa ya sifaita masu rabo a lahira da cewa,
تِلْكَ الدَّارُ الْآَخِرَةُ نَجْعَلُهَا لِلَّذِينَ لَا يُرِيدُونَ عُلُوًّا فِي الْأَرْضِ وَلَا فَسَادًا وَالْعَاقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ (83) القصص: 83

Ma'ana:

Waccan ita ce gidan lahira, muna sanya ta ga waxanda ba su son xaukaka a cikin qasa, hakanan (Basu son) varna. Qarshen qwarai ya na ga masu tsoron Allah.

Ka'ab binu Malik (RA) yace, Manzon Allah (SAW) yace, Kerkeci biyu idan aka sake su a garken awaki ba za suyi varnar da kwaxayin mutum akan dukiya da girman duniya ke yi masa a addininsa ba.
Haqurinsa:

Wani mutum ya zagi Zainul Abidin sai ya fita batunsa kamar ma bai ji shi ba. Sai yace, da kai ni ke fa! Zainu yace masa, ni kuma ba ka dame ni ba.73

Abdul Gaffar binul Qasim yace, Ali binul Hussaini ya kasance ya na wajen masallaci sai wani mutum ya zage shi. Nan take bayi da yara su kayi ciri a cikinsa. Sai Ali yace masu, ku rabu da shi mana! Sannan ya fuskance shi ya na cewa, abin da ka faxi kaxan ne ka sani. Kana da wata buqata ne a biya ma ka? Wannan mutum sai ya rasa abin da zai ce ma sa saboda jin kunya. Sai Ali ya xauko wata riga ya ba shi, sannan yace a ba shi Dirhami 1000. Daga ranar duk su ka haxu sai yace da shi, na shaida kai jikan Manzon Allah ne (SAW).74
Afuwa da Rangwame:

Malam Ibnu Abid Dunya ya ruwaito cewa, wani saurayi da ya ke aiki a gidan Ali binul Hussaini yaje zai yanka nama sai wuqa ta faxi akan xan mai gidan. Kafin kace kwabo kuwa yaron ya mutu. Hankalinsa ya tashi ainun, amma shi dai Zainul Abidin ba abin da yace ma sa face, na sani ba da gangan ba ne. Sannan yaje zuwa janaizar xansa.75

Abu ya'qub Al Madani yace, an samu rashin jituwa a tsakanin Hassan binul Hassan da xan baffansa Ali binul Hussaini, sai Hassan yazo da jama'arsa a cikin masallaci su na gaya ma sa munanan maganganu, shi kuma Ali bai ce komai ba. Sai da dare ya yi sai Ali ya same har gida ya sallama ma sa, da ya fito sai yace da shi, ya xan uwana! Duk abin da ka faxi a game da ni idan gaskiya ne ina roqon Allah ya yafe min. Idan kuma qarya ne ina roqon Allah ya yafe ma ka. Sannan sai ya juya ya tafiyarsa. Wannan abin kuwa sai ya ba xan uwansa mamaki, ya bi shi ya rungume shi ya na ba shi haquri har ya na kuka ya na cewa, wallahi ba zan qara yin haka ba. Shi kuma Ali yace, to, in haka ne ai ni tuni ma na yafe ma ka.76

Abdur Razzaq yace, wata kuyanga daga cikin bayin Ali Zainul Abidin ta yi tuntuve a lokacin da ta kawo ma sa ruwan alwalla, sai shantali ya kife a fuskarsa har ya yi ma sa rauni. Da ya xaga kansa sai tace ma sa, ka yi haquri, ka san Allah yace,


وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ..
Ma'ana;

"Da waxanda su ke haxiye fushi (Su ne masu tsoron Allah)".

Sai yace ma ta, na haxiye.

Sai ta ci gaba da karanta ma sa,


وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ..
Ma'ana:

"Da masu yafe wa mutane",

Yace ai na yafe ma ki.

Sai ta qarasa ayar


وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ سورة آل عمران: 134
Ma'ana:

"Allah ya na son masu kyautatawa".

Sai yace, ki tafiyarki na xiyauta ki.77

Wa zai iya wannan in ba babban mutum ba? Haxa yafewa da kyautatawa shi ne kamala ta masu tsoron Allah. Shugabannin Ahlulbaiti kuwa sun cancanta su ba mu misali irin wannan da Zainul Abidin ya ba mu. Ko wanensu zuciyarsa fara ce swal, ba ya qyashi ko jin haushin kowa, ba ya kuma riqo idan aka munana ma sa. Kowannensu kamar yadda wani mawaqi yace ne,

Na xora wa kaina yin afuwa ga duk mai laifi

Kome girman kurakuransa.

Domin mutane iri uku ne,

Wanda ya fi ni ko wanda na fi shi ko wanda mu ke kunnen doki.

Wanda ya fi ni na san girmansa,

Zan bi gaskiya in ba shi haqqin girmansa.

Wanda na fi shi ba na raina kaina wajen faxa da shi,

Wanda kuwa mu ke kunnen doki,

Ni kan riga shi wajen yin afuwa domin ita ce halin girma.78
Yarda da qaddarar Allah:

Xabarani ya ruwaito cewa, watarana Zainul Abidin ya na zaune tare da wasu mutane sai ya ji ana kiransa daga cikin gidansa. Nan take ya tashi ya shiga a ciki. Da ya dawo bai ce ma kowa qala ba, sai daga baya aka gane ashe rasuwa aka yi a cikin gidan nasa. Mutane su kayi ta mamakin haqurinsa har sai da aka yi ma sa magana akan haka, sai yace, mu a gidanmu an koya ma na idan abin murna ya samu mu bi Allah, idan na damuwa ya samu kuma mu gode ma sa.79

Wannan shi ne abin koyi ga dukkan musulmi. Domin qaddarori na Allah akwai alheri mai yawa a tattare da su, idan ka yi haquri za ka same su. Raki da kuka da dukan jiki ba su canza hukuncin Allah. Don haka, xan uwa haqurtar da kanka, ka kore damuwa, ka daina raki. Ka nemi taimakon Allah akan haquri idan musiba tazo ma ka. Ka sani mahaqurci shi ne mawadaci.

Allah Ta'ala yace,


إِنَّمَا يُوَفَّى الصَّابِرُونَ أَجْرَهُمْ بِغَيْرِ حِسَابٍ سورة الزمر: 10
Ma'ana:

Lalle ne ana ba masu haquri ne kawai ladarsu ba tare da lisafawa ba.


Tsentseni:

Malam Juwairiyah binu Asma'u yace, Ali binul Hussaini bai tava cin ko taro albarkacin zumuntarsa da Manzon Allah (SAW) ba.80

Haka ne. Wannan ita ce cikakkiyar kariya ga zumuntar Manzon Allah (SAW). Ba daidai ba ne a xauke ta a matsayin hanyar neman duniya. Wannan zumunci daraja ce da Allah ya ba su, ya xora ma su kare haqqenta ta fuskar tsayar da Shari'ah da kyautata ma al'umma da kariyar addini.
FASALI NA BAKWAI

Wannan Ita ce Aqidarsu

Na xaya: Su na sallah bayan ko wane musulmi

An karvo daga Muhammad binul Furat Al Tamimi yace, na zauna kusa da Ali binul Hussaini a masallacin juma'a sai wasu mutane su ka rinqa magana akan limanci. Sai ya tambaye ni me suke cewa? Sai nace masa, 'yan Shi'arku ne, wai su na cewa, ba ya halalta ayi sallah a bayan Banu Umayyah. Sai yace, wannan wallahi bidi'a ce. Duk wanda ya karanta Alqur'ani, ya fuskanci alqibla kuyi sallah bayansa, idan na kirki ne don kansa, in ba haka ba kuma kansa.81

Daga Abu Ja'afar yace, mu na sallah a bayansu – Banu Umayyah – ba don taqiyyah ba. Kuma na sheda cewa, Ali binul Hussaini ya na sallah bayansu ba don taqiyyah ba.82

Haka ne ya kamata masoyan Ahlulbaiti da masu neman haxin kai su fahimci musulunci fahimta ingattacciya. Domin a yau wasu sun daina sallar jam'i sun daina ta jum'ah, sun haramta wa kansu lada mai tarin yawa da alheri mai girma wai don babu shugaba ma'asumi wanda zai jagorance su.

Ya kai xan uwa musulmi! Yi nazarin waxannan hadissai guda biyu:


  1. Manzon Allah (SAW) yace. "... Su na yi muku sallah, idan sun yi daidai za ku samu lada tare. Idan kuwa sun kauce su ne za su cutu, ku kuma ladarku ta na nan".83

  2. Manzon Allah (SAW) yace, "Sallolin farillah wajibai ne akan ko wane musulmi ya yisu a bayan limami musulmi, na kirki ne ko ba na kirki ba ko da ya na aikata manyan zunubbai.84


Yüklə 296,5 Kb.

Dostları ilə paylaş:
1   2   3




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©genderi.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

    Ana səhifə