Na biyu: Sun yarda da Sahabbai
An karvo daga Abu Hazim yace, wani mutum yazo wurin Ali binul Hussaini sai yace, me nene matsayin Abubakar da Umar a wurin Manzon Allah (SAW)? Ali binul Hussaini yace masa, irin matsayinsu a yanzu. Ya nuna qaburburansu. Ya na nufin yadda su ke a kwance yanzu kusa da juna haka kusancinsu ya ke a lokacin rayuwarsu, haka kuma ya ke a aljanna.85
Daga Ja'afar binu Muhammad daga babansa yace, wani mutum yazo wurin babana, yana nufin Zainul Abidin Ali binul Hussaini, yace, Ba ni labarin Abubakar. Sai yace, Siddiq ka ke nufi? Sai mutumin yace masa, kai ma ka na kiransa haka? Sai yace, kai ar! Ba ka waxanda su kayi masa wannan suna ba? Waxanda su kayi masa wannan suna ai sun fi ni. Manzon Allah ne (SAW) da Muhajirai da Ansarai. Wanda ko duk bai kira shi "Siddiq" mai cikakkiyar gaskatawa ba, to kada Allah ya gaskata maganarsa. Ni ina ba ka shawarar kaje ka so Abubakar da Umar, ka qaunace su, in hakan laifi ne na xauke maka.86
Muhammad binu Haxib yace, wasu mutane sunzo ma Ali binul Hussaini daga Iraqi, sai suka rinqa aukawa a cikin mutuncin Abubakar da Umar da Usman (R.A). To, a lokacin da suka qare kalamansu sai Imam yace da su: Ku ba ni labari su wane ne ku? Shin ku ne Muhajirai na farko da Allah Ya ce:
﴿ لِلْفُقَرَاءِ الْمُهَاجِرِينَ الَّذِينَ أُخْرِجُوا مِنْ دِيارِهِمْ وَأَمْوَالِهِمْ يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِنَ اللَّهِ وَرِضْوَانًا وَيَنْصُرُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ أُولَئِكَ هُمُ الصَّادِقُونَ (8)﴾
Ma'ana:
(Ku yi mamaki) ga matalauta masu hijira waxanda aka fitar daga gidajensu da dukiyoyinsu, suna neman falala daga Allah da kuma yarda, kuma suna taimakon Allah da manzonSa! Waxannan su ne masu gaskiya.
Suratul Hashri, Aya ta 8.
Sai su ka ce, A`a. Ya ce: to, ku ne:
﴿وَالَّذِينَ تَبَوَّءُوا الدَّارَ وَالْإِيمَانَ مِنْ قَبْلِهِمْ يُحِبُّونَ مَنْ هَاجَرَ إِلَيْهِمْ وَلَا يَجِدُونَ فِي صُدُورِهِمْ حَاجَةً مِمَّا أُوتُوا وَيُؤْثِرُونَ عَلَى أَنْفُسِهِمْ وَلَوْ كَانَ بِهِمْ خَصَاصَةٌ وَمَنْ يُوقَ شُحَّ نَفْسِهِ فَأُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ (9)﴾
Ma'ana:
Da waxanda suka zaunar da gidajensu (ga musulunci) kuma (suka zavi) imani, a gabanin zuwansu, suna son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma ba su tunanin wata buqata a cikin qirazansu daga abin da aka bai wa muhajirai, kuma suna fifita waxansu a kan kawunansu, kuma ko da suna da wata larura. Kuma wanda aka kiyaye shi daga rowar ransa to, waxannan su ne marabauta.
Suratul Hashri, Aya ta 9.
Sai su ka ce, A`a. Ya ce: To, ga shi ku kun sheda ba ku cikin waxannan biyun. Ni kuma na shaida ba ku cikin na ukkun su ne:
﴿وَالَّذِينَ جَاءُوا مِنْ بَعْدِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَانِنَا الَّذِينَ سَبَقُونَا بِالْإِيمَانِ وَلَا تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلًّا لِلَّذِينَ آَمَنُوا رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوفٌ رَحِيمٌ (10)﴾
Ma'ana:
Kuma waxanda suka zo bayansu, suna cewa, "Ya Ubangijinmu! Ka yi gafara a gare mu, kuma ga 'yan uwanmu, waxanda suka riga mu yin imani, kada Ka sanya wani qulli a cikin zukatanmu ga waxanda suka yi imani. Ya Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi, Mai jinqai. Suratul Hashri, Aya ta 10.
Sa`annan ya ce da su: Ku fita ku bani wuri. Allah Yayi mu ku kaza da kaza (ma`ana yayi addu`a maras kyau akansu).87
A wata ruwaya kuma cewa yayyi, Ku tashi ku ba ni wuri! Kada Allah ya kusanta gidajenku domin ku ku na lavawa ne ga musulunci don kuyi varna, amma ku ba musulmi ba ne.88
Akwai mamaki ga waxannan mutane da irin qarfin halinsu wajen sukar Sahabban Manzon Allah (SAW), da yadda ta qoqarin rusa musulunci.
Wa nene ya kawo ma na Alqur'ani?
Wa nene ya cirato mana rayuwar Manzon Allah (SAW) da ayyukansa?
Wa nene ya xauko musuluncin kacokan bayan ya yi jihadi wajen kariyarsa, ya kutsa birni da qauye ya na yaqi, don ya isar da shi zuwa ga remu?
Su wa nene Allah yace, ya yarda da su kuma sun yarda da shi?
Duk waxannan ba su ne Sahabban Manzon Allah (SAW) ba? Ba sune surukansa ba? Sun yi tarayya kuma da shi a wasu jikoki.89
Duk mai sukar su to, addinin ne yake suka. Wanda ya soke su ba sauran Alqur'ani a gurinsa don ba shi da hanyar saninsa.
Wanda ya tuhumce su da sun canza wani abu a cikin littafin Allah kuwa, to, littafin Allah xin ya qaryata shi.
Wanda yace sun canza bayan Manzon Allah (SAW) sun yi ridda bai yarda da abin da Allah yace ba kenan cewa, ya yarda da su. Domin kuwa ya za'a yi wanda Allah ya yarda da shi ya bar shi ya vace har ya kai ga ridda?
FASALI NA TAKWAS
Wafatinsa
An karvo daga Abu Ja'afar cewa, lokacin da mutuwa tazo ma mahaifinsa Ali binul Hussaini ya yi kuka. Sai nace masa baba me ya sa ka kuka alhalin kuwa ni ban tava ganin wanda ya bautata ma Allah kamarka ba?
Sai yace, Ya xana! Idan Alqiyama ta yi ba sauran mai iko. Kowa ya na a qarqashin ikon Allah har Annabawa da Mala'iku. Wanda Allah yaso sai ya kai shi aljanna, wanda yaso kuwa sai a yi wuta da shi.90
Ali binul Hussaini ya rasu a shekara ta 95 B.H. kamar yadda Malam Yahya binu Kasir yace.91
Amma wasu masana sunce, a shekara ta 94 B.H. ya rasu, ya na da shekaru 58 a duniya. Wasu masanan kuwa na da ra'ayin cewa, tun a shekarar 92 ko 93 B.H. ne Allah ya karvi ransa.92
Bayan yi masa sallah an kai shi a maqabartar baqi'ah in da aka yi jana'izarsa.
Anan ne za ka ga qarshe na gaskiya ga wannan rayuwa. Allah mabuwayi yace,
إِنَّكَ مَيِّتٌ وَإِنَّهُمْ مَيِّتُونَ سورة الزمر: 30
Ma'ana:
Lalle ne kai (Manzon Allah) mai mutuwa ne, Kuma lalle ne su ma masu mutuwa ne.
Suratuz Zumar, aya ta 30
وَمَا جَعَلْنَا لِبَشَرٍ مِنْ قَبْلِكَ الْخُلْدَ أَفَإِنْ مِتَّ فَهُمُ الْخَالِدُونَ سورة الأنبياء : 34
Ma'ana:
Ba mu sanya ma wani mutum tabbata ba a gabaninka. To, idan ka mutu su za su dawwama ne?
Suratul Anbiya' aya ta 34
Wannan ita ce rayuwar xan adam. Kome tsawon ranka watarana zaka mutu. Ko wane ne abokinka watarana zaka rabu da shi.
Kaji daxi yadda ka ke so, amma fa tabbas sai ka rabu da shi. Mutuwa kenan! Mai wargaza jin daxi, mai kore farin ciki. Wasu lokuttan mu tuna, a wani yanayin kuma sai mu shimga.
Ali binul Hussaini bai yi kuskure ba da yace a cikin wani waqensa;
Mu kan firgice idan mutuwa ta juyo
Mu na koma wasarmu idan mun ka mance
Misalin namu wanda ya hangi zaki
Idan ya ba da bai ko sai ya mance93
Kammalawa
Ya xan uwa!
Ga mu dai tare da kai mun kammala wannan saqo, bayan mun yawata a cikin tarihin wannan bawan Allah wanda xaya ne daga fitattun 'yan gidan annabta, kuma wanda 'yan sha biyun shi'a ke gadara da jingina kansu zuwa ga reshi.
Daga abin da ya gabata dai ka na iya fahimtar wane ne Zainul Abidin bisa gaskiyar Allah babu za'ida. Mu na iya taqaita darussan wannan xan littafi kamar haka;
Darasi Na xaya
Tataccen tauhidi shi ne aqidar da Ahlulbaiti su ka rayu akansa. Ba su kiran kira kowa don neman biyan buqatunsu sai mahaliccinmu. Ba su kiran Annabi ko Mala'ika ko Waliyyi ko wani zavavve, domin sanin da su kayi cewa, wannan haqqen Allah ne shi kaxai. Ba mai amfanar kansa da kome a duniya sai da yardar Allah ballantan ya amfani wani. Wanda ko Allah ya nufi shi da samun cuta ba mai kuranye ta daga kunsa sai shi Allah mahalicci.
Ga abin da Allah yace ma mushrikai da su ka nemin agajin wani ba shi ba;
إِنَّ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ عِبَادٌ أَمْثَالُكُمْ فَادْعُوهُمْ فَلْيَسْتَجِيبُوا لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ سورة الأعراف: 194
Ma'ana:
Lalle ne duk waxanda ku ke kira koma bayan Allah su bayi ne irinku. To, sai ku kira su, su kuma su karva maku in har kun kasance masu gaskiya (a kiran da ku ke ma su). Suratul A'raf, aya ta 194
Darasi Na biyu;
Kyakkyawar alqar da ke tsakanin Sahabbai da Ahlulbaiti, iyalan gidan Manzon Allah (SAW). Wannan hujja ne akan soyayyar gakiya da qaunar da su ke ma junansu.
Sau tari ne Ahlulbaiti su ka kare martabar almajiran mai gidansu, su na yaba ma su, su na mayar da martani akan mai sukarsu, su na jaddada kira ga qaunarsu da jivintarsu. Wannan kuwa ba zai asali ba da kyakkyawan yabon da Allah ya yi ma su (Sahabban) a cikin tsarkakakken littafinsa, kamar in da ya ke cewa;
لَقَدْ تَابَ اللَّهُ عَلَى النَّبِيِّ وَالْمُهَاجِرِينَ وَالْأَنْصَارِ الَّذِينَ اتَّبَعُوهُ فِي سَاعَةِ الْعُسْرَةِ مِنْ بَعْدِ مَا كَادَ يَزِيغُ قُلُوبُ فَرِيقٍ مِنْهُمْ ثُمَّ تَابَ عَلَيْهِمْ إِنَّهُ بِهِمْ رَءُوفٌ رَحِيمٌ سورة التوبة: 117
Ma'ana:
Darasi na Uku:
Irin kyawawan xabi'un wannan bawan Allah kamar son jama'a da kyautata ma su, da haquri akan cutawarsu, da nisantar abin hannunsu duk su na daga cikin xabi'un annabta da ya gada daga iyaye da kakanninsa.
Darasi na Huxu;
Cikakken tsoron Allah shi ne wanda ya ya ke gadar da yin aiki da tsare ibada. Zainul Abidin kuwa ya dace da wannan suna nasa a wannan fage.
Darasi na biyar;
Qarya ne ace Ahlus Sunnah su na gaba da Ahlulbaiti a da ko a yanzu, domin kuwa babu wanda ya san haqqensu bisa ga adalci kamar Ahlus Sunnah. Mu tuna irin yabon da limaman Sunnah su ka yiwa wannan bawan Allah. Haka su ke da duk sauran ire irensa daga zuri'ar Annabi mai tsarki.
Daga qarshe, Ina 'yan uwana masu qaunar iyalan Manzo, masu jin daxin jingina kansu zuwa ga resu? A daina faxin maganar fatar baki wadda ba ta kai zucci. A koma ma rayuwar waxannan bayin Allah ayi koyi da su a maganganunsu da ayyukansu. Masoyi fa shi ne mai koyi da masoyinsa.
Wannan kiran na fara shi da kaina sannan da sauran 'yan uwana musulmi na ko wace xariqa da ko wace mazhaba. Muzo muyi aiki da kalamai da ayyukan Ahlulbaiti don mu haxa kanmu wuri xaya kamar yadda su ka kasance a tasu rayuwa, wataqila zamu samu haske da zai kai mu wurin Allah mu same shi a cikin yarda da mu ba cikin hushi ba.
Ya Allah! Ga yi gafar ga remu da 'yan uwanmu musulmi da su ka riga mu bada gaskiya, Kada ka sanya damuwa a cikin zukatanmu a game da waxanda su ka yi imani. Lalle ne ya Ubangijinmu Kai ne Mai tausyi, Mai jinqai.
Allah ya yi tsira akan annabinmu Muhammad da iyalansa da Sahabbansa baki xaya.94
Manazarta
Al Bidayah Wan Nihayah, na Ibnu Kathir Ad Dimashqi, Bugun Farko, Dar Ar Rayyan Lit Turath.
Tarikh Madinati Dimashq, na Hafizh Ibnu Assakir As Shafi'i, Dar Al Fikr.
Tahdhib Al Kamal, na Hafizh Ibnu Hajar Al Asqalani, Bugun Farko, Muassasatur Risalah.
Tahdhib At Tahdhib, na Hafizh Ibnu Hajar Al Asqalani, Bugun Farko, Dar Al Ma'rifah.
Al Jami' As Sahih, na Imam Abu Isa At Tirmidhi, Bugun Farko, DAr Ihya' At Turath.
Hilyatul Auliya' Wa Xabaqatul Asfiya', na Hafizh Abu Nu'aim Al Asfahani, Bugun Farko, Dar Al Kutub Al Ilmiyyah.
Dam'atun Ala hubbin Nabiyy, na Abdullahi binu Saleh Al Khudairi, An buga shi a jerin littafan Al Muntadal Islami, Huququn Nabiyy bainal ijlali Wal Ikhlal, Bugun Farko.
Siyar A'lam An Nubala', na Imam Shamsud Din Muhammad binu Ahmad Addhahabi, Bugu na Sha xaya, Muassasatur Risalah.
Sahih Al Bukhari, na Imam Muhammad binu Isma'il Al Bukhari, Dar Al Qalam, Beirut.
Sahih Muslim, na Imam Muslim binul Hajjaj, Dar Ihya' At Turath Al Arabi.
Sifatus Safwah, na Imam Ibnul Jauzi, Bugun Farko, Dar Al Fikr.
Ax Xabaqat Al Kubra, na Imam Ibnu Sa'ad Al Basri, Bugu na biyu, Dar Al Kutub Al Ilmiyyah.
Musnad Al Imam Ahmad, na Imam Ahmad binu Hambal, Dar Al MA'arif.
Littafan Shi'ah:
Bihar Al Anwar, bugun Al Wafa, Beirut, 1403H.
Sharh Ihqaq Al Haqq, na Al Mura'shali, Maktabatu Ayatillil Uzhmah Al Mura'shali, Qum, Iran, 1415H.
Kashful Gummah, na Arbili, Bugun Al Adwa', Beirut.
Dostları ilə paylaş: |