DW, Ji Ka Ƙaru. Jahilci: Wata yarinya ’yar makaranta. Kashi na biyar: Nasara ko rashinsa.
1/10
DEUTSCHE WELLE
JI KA ƘARU
Jahilci: Wata yarinya ’yar makaranta
Kashi na biyar: Nasara ko rashinsa
Wanda ya rubuta:
Frédéric Gakpara
Wanda ya tace:
Yann Durand
Wanda ya fassara:
Anne Thomas
’Yan wasa:
Laɗifa:
’yar shekara 15
Zakiyya:
’yar shekara 20
Malamin makaranta: ɗan shekara 36
Namadi:
ɗan shekara 18
DW, Ji Ka Ƙaru. Jahilci: Wata yarinya ’yar makaranta. Kashi na biyar: Nasara ko rashinsa.
2/10
Mai gabatarwa:
Masu sauraronmu, barkanmu da sake kasancewa da ku a cikin wani sabon
shirinmu na “Ji Ka Ƙaru” wanda zai kasance kashi na biyar a yau a kan labarin
nan na “Wata yarinya ’yar makaranta”.
Tun lokacin da Laɗifa ta koma makaranta, sai yanayin rayuwa a gidan Baba
Wali ya ƙara tsananta. Sai Laɗifa ta zama kamar saniyar ware. Kasa biyan
bashin da babarta take yi wanda ta karɓa daga bankin talakawa, sai ya ƙara
dagula al’amura. Tun da al’amuran suka zama haka ba wuya Maimuna ta
hasala, shi kuma Baba Wali sai ya rage zama a gida. Ran nan, bayan an tashi
daga makaranta, sai malamin su Laɗifa ya ce ta dakata, don yana so su ɗan
tattauna. Jama’a ku ba mu aron kunnuwanku don ku ji yadda za ta kasance a
cikin kashi na biyar mai suna “Nasara ko rashinsa”.
Fitowa ta 1: A makarantar Laɗifa
Laɗifa, Malamin makaranta
Malam:
Shin me yake faruwa ne, Laɗifa? Na ga ba kya ƙoƙari kwanan
nan. ... Ba ki ce kome ba. Sauran malamai ma sun faɗa min
cewa ko yaushe ba kya mai da hankali a aji, ni ma kuma ina
ganin hakan duk lokacin da na shiga ajinku. Lalle akwai
wani abu da yake faruwa! Ko kin fara soyayya da wani yaro
ne?
Laɗifa:
A’a Malam!
Malam:
To, mene ne dalili?
Laɗifa:
Ban sani ba, Malam. Ba na samun nutsuwa ne idan ina yin
karatu a gida.
Malam:
Me yake hana ki samun nutsuwar?
DW, Ji Ka Ƙaru. Jahilci: Wata yarinya ’yar makaranta. Kashi na biyar: Nasara ko rashinsa.
3/10
Laɗifa:
Yanayin gidan namu ne a birkice, Malam. Iyayena da ƙyar
suke magana da ni. Ina jin na yi kuskure da na ƙi yarda da
shawarar da iyayena suka yanke tun farko ta cire ni daga
makaranta.
Malam:
Anya kuwa kin yi kuskure? To yaya za ki yi da kin yarda da
shawarar tasu?
Laɗifa:
A lokacin iyayena na fama da matsalar kuɗi, Malam, ni kuma
duk idona ya rufe a kan karatuna. A gaskiya ban kyauta ba.
Malam:
Laɗifa! Ai ba haka ne rashin kyautawa ba. Wannan abin da
kika yi shi ya fi dacewa.
Laɗifa:
In da ban nuna son kaina ba, ai da na ba wa Baba kuɗin ko
ya samu ya toshe wata kafar.
Malam:
Ai karatunki na ɗaya daga cikin matsalolinsa, mafi girma ma
kuwa.
Laɗifa:
To, me ya sa ya daina kula ni? Ba ka gani ba fa, Malam! Gani
suke yi duk matsalolin nan namu na gida ni na jawo su.
Malam:
Laɗifa, ina tabbatar miki da cewa ba ke ba ce. Gaskiyar
magana ita ce, ko dai babanku yana nadamar matakin da ya
ɗauka na cire ki daga makaranta, ko kuma duk matsaloli
sun sha masa kai har ba ya iya tafiyar da harkokin sana’arsa
kamar yadda ya kamata. Amma ko ma dai mene ne, ba ki da
laifi.
Laɗifa:
E to, ko ma dai ba ni da laifi, ba zan fita ba!
DW, Ji Ka Ƙaru. Jahilci: Wata yarinya ’yar makaranta. Kashi na biyar: Nasara ko rashinsa.
4/10
Malam:
Laɗifa, matsalolin babanku wata rana za su iya zama tarihi,
amma in kika yi sakaci da al’amarin karatunki yanzu, to fa
kin rasa ke nan.
Laɗifa:
Amma ba yadda za a yi na sami nutsuwa a gidan da sai ka
ce mutuwa aka yi. Ba kuma ranar da babarmu ba za ta ci
mutuncin babbar ƙawata ba, wadda a haƙiƙanin gaskiya ma
ta biya min kuɗin makaranta!
Malam:
Dole ne ki san dabarar da za ki yi ki faranta wa kanki. Ko da
kuwa kowa zai dinga yin fuskar shanu, to ke, sai ki dinga
murmushi. In kika yi karatu, kina da zaɓi har biyu Laɗifa, ko
dai ki yi sa’a ki sami aiki a wani babban kamfani, ko kuma ki
sami miji na gari. In kuwa ba haka ba, to ba mamaki ki zama
abar tausayi, kin ga kuwa wannan babbar asara ce. Shi ilimi
zai taimaka miki ki sami damar cuɗanya da mutanen kirki,
ki ma zama mace ta gari, sannan ki sami nutsuwa. Ko a ce
ba ki mallaki kome ba, to kuwa za ki sami nutsuwa a kan
abubuwa da dama. Ina fatan kina fahimtar bayanina?
Laɗifa:
E, Malam!
Malam:
A matsayinki na ’ya mace Laɗifa, ilimi ya fi dacewa da ke. A
zamanin nan na yau, kyau ba wani kayan gabas ba ne ga ’ya
mace. Ya kamata ki nutsu. Saura wata ɗaya kacal a fara
jarrabawa, don haka, ɗan kuskure kaɗan da wannan ɗari-
ɗarin da kike yi na iya jawo miki matsala. Kin gane ko?
Laɗifa:
Na gane Malam!
Malam:
To, ki mai da hankali, ina so ki ƙara kula Laɗifa!
DW, Ji Ka Ƙaru. Jahilci: Wata yarinya ’yar makaranta. Kashi na biyar: Nasara ko rashinsa.
5/10
Laɗifa:
To, Malam, ba zan ba ka kunya ba!
Malam:
Madalla! To, a gai da gida!
Laɗifa:
Kai ma haka, Malam. Sai gobe!
Malam:
To, masha’allahu! Na gode ƙwarai, Laɗifa. Sai goben!
Mai ba da labari:
To a halin yanzu an ƙarfafa wa wannan yarinya gwiwa, kuma a shirye take ta
sake fuskantar karatunta. Kashegari ƙawar Laɗifa wato Zakiyya ta gayyaci
Namadi, yaron Baba Wali, don su ci abinci tare da nufin gano yadda karatun
yaƙi da jahilcinsa yake tafiya. Kusan sati uku ke nan yana zuwa.
Fitowa ta 2: A gidan abinci
Zakiyya, Namadi
Zakiyya:
Namadi ke nan. To kana dai jin daɗin karatu, ko?
Namadi:
Ƙwarai Zakiyya, ina jin daɗi sosai. A hankali ake yi mana.
Kuma suna yi mana bayani dalla-dalla, kuma a nutse. Abin
kam alhamdu lillahi.
Zakiyya:
To wane abu ka koya da kake jin yana da amfani sosai?
Namadi:
E to, yanzu na iya rubuta sunana.
Zakiyya:
Allah? Da kyau, Namadi!
Namadi:
Na kuma iya sa hannu.
DW, Ji Ka Ƙaru. Jahilci: Wata yarinya ’yar makaranta. Kashi na biyar: Nasara ko rashinsa.
6/10
Zakiyya:
Da ba ka iya ba?
Namadi:
Am…ban iya ba, babbar yaya, sai dai dangwale.
Zakiyya:
Wannan, ai ba abin kunya ba ne, Namadi
.
Ba ga shi yanzu ka
nutsu kuma kana koya ba!
Namadi:
Na gode, babbar yaya. Ba don ke ba da ban sami wannan
babbar damar ba.
Zakiyya:
Ai Mr Hendrik da matarsa za ka gode wa. Wannan aikinsu
ne. Ni na kai su wurare ne kawai, kuma aikina ne wannan.
Yaya Baba Wali, yana lafiya?
Namadi:
Lafiya lau, yayata.
Zakiyya:
Har yanzu bai haƙura a kan shigarka makaranta ba ko?
Namadi:
Wa? Wannan maigidan nawa? Ai ba ya jin shawara. Kuɗi ne
kawai a gabansa.
Zakiyya:
To yanzu yana amfani da injin da cibiyar su Mr Hendrik ta ba
shi ba?
Namadi:
A to, ya ajiye shi a kwaba. Har gadara yake wai yau sama da
shekaru 30 ke nan yana aikin walda ba tare da kariya ba,
kuma wai ba abin da zai same shi.
Zakiyya:
Kai, Malam, zo ka karɓi kuɗinka! … Wallahi, Namadi,
mutumin nan lalle bai san abin da yake yi ba! Ka ga fa na kai
su Mr Hendrik wajen aikinku ne don na taimaka masa ko ya
samu ya warware matsalolinsa.
DW, Ji Ka Ƙaru. Jahilci: Wata yarinya ’yar makaranta. Kashi na biyar: Nasara ko rashinsa.
7/10
Namadi:
A to. Ni dai, babbar yaya, ba abin da ba na sawa! Kama daga
safar hannu, da tabarau, da rigar aiki, kome ma!
Zakiyya:
Da kyau, Namadi! Za ka sami nutsuwa in dai ka ci gaba da
yin hakan, kuma ba da daɗewa ba!
Namadi:
Na gode, babbar yaya! Ba zan ba ki kunya ba.
Zakiyya:
Yauwa, Namadi. Tun da na karɓi canjina, mu tafi. Akwai aiki
jibge a gabana!
Namadi:
Na gode, babbar yaya.
Zakiyya:
Ba wani abu, Namadi! Sai an jima!
Namadi:
To sai an jima!
Mai ba da labari:
Ba abin da Zakiyya take ta faman yi a ’yan kwanakin nan ban da ƙarfafa wa
babbar ƙawarta gwiwa kafin jarrabawarsu ta zo. Ta kuma sake kai su Mr
Hendrik shagon Baba Wali don su sayi kujerun ƙarfen nan da aka kwaikwaya,
duk don ta taimaka masa ya sake farfaɗo da harkarsa ko ya ɗan sakar wa
Laɗifa fuska. To, ga shi ma har an yi jarrabawar ta ma fito, kuma Ladifa ta
sami kyakkyawan sakamako. Ga su can ma suna
party a gidan Zakiyya!
Fitowa ta 3: A ɗakin Zakiyya
Zakiyya, Laɗifa
Laɗifa:
Kai! Zakiyya! Abin ya sa kaina yana juyawa!
DW, Ji Ka Ƙaru. Jahilci: Wata yarinya ’yar makaranta. Kashi na biyar: Nasara ko rashinsa.
8/10
Zakiyya:
Me fa, Laɗifa?
Lemo ko kiɗan?
Laɗifa:
Wane lemo? Ai ba sinadarin giya a ciki! Ina jin dai kiɗan ne!
Zakiyya:
Me zai hana mu leƙa gidan rawa?
Laɗifa:
Allah? Ban taɓa zuwa ba!
Zakiyya:
Na san ba ki taɓa zuwa ba. To mu je mana yau da daddare!
Ya kamata mu shaƙata saboda murnar cin jarrabawar da
kika yi. Lalle ne ki samu ki sarara, don kuwa kin ji jiki,
saboda kin yi watanni kina fama da karatun jarrabawa, ko ba
haka ba, ƙawata?
Laɗifa:
Haka ne, amma abin zai yi min yawa. Mu yi rawarmu a nan
mana.
Zakiyya:
Ke, ai abin ba ɗaya ba ne, ƙawata!
Laɗifa:
To, ba sai mu lallaɓa haka ba, Zakiyya! Shekarunki fa 20
kuma kin fara aiki. Ga shi kuma ke iyayenki sun sakar miki
mara. Ni kuwa sam ba haka nake ba!
Zakiyya:
Kada wannan ya dame ki, ƙawata!
Laɗifa:
Ya isa haka, na gode Zakiyya!
Zakiyya:
Gaskiya na yi farin cikin cin jarrabawar nan da kika yi.
Laɗifa:
Amma fa da wuya sosai!
DW, Ji Ka Ƙaru. Jahilci: Wata yarinya ’yar makaranta. Kashi na biyar: Nasara ko rashinsa.
9/10
Zakiyya:
Na sani, to ai shi ya sa abin yake da muhimmanci. To mana
Laɗifa, mu ci gaba da sha’ani.
Mun ci jarrabawa!
Laɗifa:
Mun ci jarrabawa!
Zakiyya:
Ina jin yayanki ne ya bugo waya! Shi ne ma ne. Alo, Abba? …
Wa ya ba ka wannan lambar? … Me ka ce? … Kada ka
kuskura ka sake bugo wannan lambar! Ba za ni ko’ina da kai
ba yau. Goben ma haka sam. Ka daina yi min wata barazana
ko na kira maka ’yan sanda! … Mts! Abin haushi kawai!
Laɗifa:
Ke Zakiyya! Wane ne kuma haka?
Zakiyya:
Wani mahaukaci ne wallahi! Haka wannan mutumin yake ta
yi min barazana in na taso daga wajen aiki. Kin ko san abin
da yake cewa in na ƙi kula shi? “Ai ba Turawa ne kaɗai suke
da kuɗi ba.”
Laɗifa:
To?! Wato don yana ganinki da baƙi ’yan yawon buɗe ido.
Zakiyya:
Haka ne! Haka ’yan mazan nan suke ɗaukata. Tunaninsu shi
ne, ni ma ina aiki a nan ne don na jawo hankalin ’yan yawon
buɗe ido.
Laɗifa:
Wannan shi ne abin da ya sa ba na sha’awar aikinki sam!
Zakiyya:
Haka abin yake fa, Laɗifa, a ko’ina. Su maza da sun ga mace
ta taka wani tudun dafawa, sai su ɗauka mutuncinta ta
sayar. Ba na so na dogara da wani ɗa namiji. Ina so na tsaya
da ƙafafuna, kuma zan ci gaba da yin kwasa-kwasai don na
dinga samun ci gaba a aikina.
DW, Ji Ka Ƙaru. Jahilci: Wata yarinya ’yar makaranta. Kashi na biyar: Nasara ko rashinsa.
10/10
Laɗifa:
Gaskiyarki, Zakiyya! Dole ne mu yi karatu mu nema wa
kanmu ’yanci. Ke kawai mu manta da wannan! Bai kamata
mu bari wannan ya shiga rayuwarmu ba! Mu tashi mu ɗan
taka mana!
Mai gabatarwa:
Haka dai waɗannan ƙawayen suka dinga tiƙar rawa har dare ya raba. Wani
abin mamaki shi ne Baba Wali da Maimuna ba su damu da irin daren da
’yarsu ta yi ba ta dawo gida ba ranar. Hasali ma dai Maimuna sai da ta ce da
Zakiyya, Allah ba mu alheri, lokacin da ta kawo Laɗifa gida. Saboda haka, sai
abin ya kasance wa Laɗifa da Zakiyya kamar ba-zata. To amma wannan shirin
zai ɗore ke nan? Sai a tare mu a shiri na gaba. Kuna iya ziyartarmu a
adireshinmu na yanar gizo domin sake sauraron wannan shirin ko aiko da
tsokaci, wato www.dw-world.de/lbe.
Dostları ilə paylaş: |