Jss week topic: sarkakkiyar jimla (goyon jimla)



Yüklə 34,5 Kb.
tarix17.09.2018
ölçüsü34,5 Kb.
#68719

JSS 3 WEEK 3

TOPIC: SARKAKKIYAR JIMLA (GOYON JIMLA)

Akan sami sarkakkiyar jimla ne kamar yadda akan sami hardaddiya, watau ta hanyar hada jimloli fiye da daya. Bambacia a nan shi ne a cikin sarkakkiya jimla ana yin goy one. Wannan kuwa shi ne a dauki wata jimla a saka ko a tsunduma a cikin wata, to an yi goyon jimla ken an.




Menene goyon jimla?

Goyon jimla shi ne a dauki wata jimla sukutum a saka ta a cikin wata domin ta rika aiki a matsayin wani bangare na jimlar da aka sat a a ciki. Alal misali ana iya daukar jimla daya sukutum a saka ta a wata jimla a makwafin karbau ko cikamako kamar yadda za a same shi a sassaukar jimla.


Misali

1. a) Sassaukar jimla

Audu ya san gida


A wannan jimla gida she ne matsayin karbau ko cikamako.

b) Jimla mai goyo/sarkakkiyar jimla

audu ya san Bello ya tafi kano
Isan an lura kamar yadda kalmar gida ta biyo bayan san (watau aikatau) domin ta zama cikamako, haka jimla Bello ya tafi kano ta biyo bayan san ita ta zama cikamako. Ga wani misali.
2. a) Sansaukar jimla

Magajiya ta hana yara su shiga gidanta

A nan kamar yadda kalmar kudi ta kasance a matsayin cikamako haka jimlar “Yara su shiga gidanta”.
IRE-IREN SARKAKKIYAR JIMLA

Sarkakkiyar jimla iri uku ce:

1. Mai cikon cewa

2. Mai cikon makasudi

3. Mai wakikin suna dogarau
Sarkakkiyar jimla mai cikon cewa

1. Audu ya san cewa Bello ya makara.

2. Matane suna tsammanin cewa Asabe bat a da hankali.

3. Kwamishinoni sun tuna cewa jama’a suke yi wa aiki.


Sarkakkiyar jimla mai cikon makasudi

Misali:


1. Gwamnati tana so a ba kowa hakkinsa.

2. Jama’a suna suka ce kada kowa ya kara yawon dare.


AIKIN GIDA

1. Me ake nufi da sarkakkiyar jimla?



2. Rubuta jimloli masu dauki da sarkakkiyar jimla mai cewa guda uku (3) mai makasudi guda uku.
Yüklə 34,5 Kb.

Dostları ilə paylaş:




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©genderi.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

    Ana səhifə