Tarihin Ahlul Baiti A



Yüklə 296,5 Kb.
səhifə1/3
tarix17.09.2018
ölçüsü296,5 Kb.
#68718
  1   2   3


Tarihin Ahlul Baiti (A.S)

Daga Cibiyar Ahlul Baiti Da Sahabbai ta Najeriya

كتاب نجي كربلاء للشيخ عبد العزيز العمير بلغة الهوسا

ترجمه محمد المنصور إبراهيم

Mai Rabon Ganin Baxi

Tarihin Zainul Abidina Ali Xan Husaini Xan Ali Xan Abu Xalib (A.S)



Wallafar

Sheikh Abdul Aziz binu Ahmad Al Umair

Alqali a kotun qoli ta shari'ar musulunci

a qaxif ta qasar Saudia

Fassarar

Muhammad Mansur Ibrahim

Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci

Ta Jami'ar Usmanu Xan Fodiyo, Sakkwato

Waxanda suka buga

Mu'assasatu Ahlil Baiti Wassahabah, Najeriya
Bugun Farko 1427H/2006M

Adadin da aka buga: Kwafi 75,000

ISBN 978-2076-68-5

© Haqqen buga wannan littafi na Mu'assasatu Ahlil Baiti Wassahabah, Najeriya ne.

Wanda yake son buga shi saboda Allah ya na iya tuntuvarmu a adireshinmu kamar haka:

97, Ahmadu Bello Way, P.O.Box 2491,

Sokoto, Najeriya.
Ko kuma ya tuntuvi Mai Fassara a

mansursokoto@yahoo.co.uk



ABUBUWAN DA KE CIKI

Gabatarwa.................................................

Muhimmancin Sanin Tarihi:..................

Qa'idodin karanta tarihi:.......................

Qa'ida ta Xaya: Mai karatu ya qudurta koyi da magabata:...................................................

Qa'ida ta Biyu: A kula da ingancin labari ko rashin ingancinsa:.........................................

Qa'ida ta Uku: Sanin cewa, mutum duk xan tara ne:................................................................

Qa'ida ta Huxu: A tsarkake zuciya:.............

Qa'ida ta Biyar: A mutunta Malamai da ladabi wajen ambatonsu..........................................

Qa'ida ta Shida: Hattara da sukar Malammai:

Qa'ida ta Bakwai: Adalci shi ne, auna yawan sawabar mutum tare da yawan kurakuransa.....

Taqaitaccen bayani akan matsayin gidan annabta.................................................

Yadda mutane su ka kasu kashi uku a game da Ahlulbaiti........................................................



Kashi na farko: Su ne waxanda su ke tauye haqqensu..........................................................

Kashi na biyu: Su ne waxanda su ka faifaye a wajen sonsu.......................................................

Kashi na Uku: Su ne waxanda su ka tsakaita, su ka tsaya kan gaskiya...........................................

FASALI NA XAYA:

Wane ne Zainul Abidin?...........................

Sunansa da Haifuwarsa.............................

FASALI NA BIYU:

Jihadinsa Da Yadda Ya Kuvuta A Karbala'..................................................

FASALI NA UKU:

Yabon da Mutane su kayi ma sa.................

FASALI NA HUXU:

Yawan Ibadarsa da qanqan da kansa ga Ubangiji..................................................

Sallarsa da yawan addu'arsa........................

Yadda ya ke tsoron Allah da dogaro ga reshi.........................................................

Karimcinsa da yawan sadaqarsa.....................

FASALI NA BIYAR:

Yawan Ilminsa...................................................



FASALI NA SHIDA:

Kulawarsa da tsarkake zuciya......................

Tawali'unsa:..............................................

Haqurinsa:................................................

Afuwa da Rangwame:.................................

Yarda da qaddarar Allah:............................

Tsentseni:...................................................

FASALI NA BAKWAI:

Wannan Ita ce Aqidarsu.............................

Na xaya: Su na sallah bayan ko wane musulmi...................................................

Na biyu: Sun yarda da Sahabbai..................

FASALI NA TAKWAS:

Wafatinsa.................................................

Kammalawa

Darussa daga abin da ya gabata:

Darasi Na xaya: Tataccen tauhidi shi ne aqidar da Ahlulbaiti su ka rayu akansa............................

Darasi Na biyu: Kyakkyawar alaqar da ke tsakanin Sahabbai da Ahlulbaiti, iyalan gidan Manzon Allah (SAW)..........................................

Darasi na Uku: Irin kyawawan xabi'un wannan bawan Allah........................................................

Darasi na Huxu: Cikakken tsoron Allah shi ne wanda ya ya ke gadar da yin aiki da tsare ibada...................................................................

Darasi na biyar: Qarya ne ace Ahlus Sunnah su na gaba da Ahlulbaiti a da ko a yanzu...................................................................

Daga qarshe......................................................
Bismillahir Rahmanir Rahim

Gabatarwa

Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bude qofofin imani don masu shiga, ya sauqaqe hanyoyin kyautatawa ga masu nema, ya shimfixa rahamarsa ga masu ibada, ya saki labulen suturarsa don gafartawa masu tuba.

Na shaida babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, Shi kaxai. Na shaida cewa, shugabanmu Muhammadu bawansa ne, Manzonsa, wanda aka aiko shi da littafi mafi kyawo, aka qarfafa shi da kyawon bayani da rarrabe zance. Allah ya yi tsira gare shi da dukkan iyalansa da Sahabbai, salati da tsira madawwama zuwa ranar haxuwa da hisabi.

Bayan haka, Lallai sanin matsayin Manzon Allah (SAW) matsayi ne shi kansa babba. Harshe ba zai gaji ba da bayanin darajojinsa ballantana alqalami. Sonsa sharaxi ne na Imani, darajanta shi kuwa shi ne alamar tsoron Allah. Imani bai kammala sai harshe ya furta qaunarsa, zuciya ta qullu akan sonsa da jivintarsa, da darajanta shi da biyar hanyarsa. Ya na daga cikin sharuxxan son Manzon Allah (SAW) a so iyalansa tsarkakakku domin alaqarsu da wannan asali mai daraja na shugaban Manzanni, jagoran masu tsoron Allah.

Son Manzon Allah (SAW) ga 'yarsa Fatimah tabbatacciyar magana ce da dukkan masana sun san da ita, haka kuma 'ya'yanta Al Hassan da Al Hussain waxanda su ne farin cikin Manzon Allah (SAW) da hasken zuciyarsa a duniya. Don haka ne na ga dacewar in ba da kyakkyawan misali daga tsarkakakkar zuri'arta, in rubuta tarihin jikanta na wajen xanta Hussaini kuvutaccen karbala (AS) domin mu samu wani haske daga tarihinsa musamman a wannan zamani da gaskiya ta cakuxa da qarya, mavarnata kuma sun rataya da gaskiya don rufe varnarsu, su na yaudara da sunan son iyalan Manzo (SAW).1

Da sannu mai karatu zai gano irin darajojin wannan taliki, tsarkakakkiyar nasabarsa, zurfin hankalinsa, nisan tunaninsa, tarin ilminsa, kyawon ibadarsa da kuma tsarkin zuciyarsa ba tare da wani qarin gishiri ko zuqi ta mallau ba.

Na yi shimfixa gabanin wannan taqaitaccen tarihi da wasu dokoki da ya wajaba ga mai karatun tarihi ya kiyaye su, na biyo su da wani gajeren bayani akan son iyalan gidan Manzo (SAW) saboda muhimmancinsa. A cikin tarihin wannan bawan Allah kuwa na dogara ga ingantattun ruwayoyi daga littafan magabata, na kuma taqaita sharhi akansu domin sauqin fahimtarsu ga mai karatu. A qarshen littafin na bayyana sakamakon wannan nazari. Idan na yi daidai baiwa ce daga Allah. Idan kuma kuskure ya shiga cikin aikina to, daga wurina ne da wurin shaixan. Fatar da ni ke Allah ya haxa ni da sawaba, kuma ya yafe kurakuraina.

Ya Allah! Ina shedar ma ka qaunata ga iyalan Manzonka, irin qaunar da ni ke fatar samun cetonsa akanta, da kusanci zuwa ga reka a dalilinta. Ya Allah! Ka haxa ni da masoyan nan nawa Muhammad da tsarkakan iyalansa da nagartattun sahabbansa da masu bin sawunsu har zuwa ranar alqiyama a cikin aljannarka maxaukakiya.



Muhimmancin Sanin Tarihi:

Ya na da kyau mu soma magana anan da nazarin faxar Allah Ta'ala in da ya ke cewa,


أُولَئِكَ الَّذِينَ هَدَى اللَّهُ فَبِهُدَاهُمُ اقْتَدِهِ

Ma'ana:

"Waxancan su ne waxanda Allah ya shiryar, to, ka yi koyi da shiriyarsu". An'am 90

Wannan aya ta kan sa ka tuna sunayen manya waxanda ayyukansu su ka dawwamar da ambatonsu, gurabunsu su ka fito da sunayensu, tun daga tarihin Annabawa, waxanda su ka haskaka duniya da hasken shiriyarsu har ya zuwa tarihin Sahabbai waxanda tarihinsu ya ke walqiya a cikin sauran tarihin 'yan adam2, har zuwa ga tarihin malamai da sauran mutanen kirki, shugabanni da talakkawa3. A cikin tarihinsu za ka ga mutanen da su ka sadaukar da rayuwarsu wajen bayanin gaskiya da hukunci da shari'a da yaxa addini, ga kuma yawan ibada da istiqama, abin da zai sa ka yi murna da alfaharin zamanka cikin wannan al'umma wadda ta saba fitar da jarumai masu jagorancin duniya. Anan ne za ka daxa gane haxarin jahiltar da mu ka yi da ilmin tarihi da hasarar da ta cim mana a sakamakon haka.

Karanta tarihin wani bawan Allah ya kan ba ka damar sanin halayyarsa da ilminsa da sauye sauyen da ya samu a matakan rayuwarsa. Daga nan ne za ka xauki darussan da za su taimaka wajen gyara rayuwarka da kauce ma miyagun ayukka waxanda zasu qazamta al'amarinka, ta haka sai a samu musulmi na gari waxanda ke iya xaukar nauyin ci gabantar da al'umma a gaba.

Ga wasu daga cikin maganganun magabata waxanda ke nuna muhimmancin ilmin tarihi:

Imam Abu Hanifa (RH) yace, Na fi sha'awar karanta labarin malamai da kyawawan xabi'unsu fiye da karanta ilmin fiqhu domin wannan shi ke karantar da ladubbansu da halayensu.4

Imam Al Sakhawi yace, Rayuwar na gaba ita ce madubin na baya.

Imam Muhammad binu Yusuf yace, Ban tava ganin abin da ya ke da amfani ba kamar karanta labarin mutanen kirki.5

Babban masani Ibnul Jawzi yace, Ina ba ku shawarar karanta tarihin magabatan kirki da littafansu da labaransu. Wannan zai sa ku zama kamar ku na ganinsu.Kamar yadda wani mai hikima yace,

Na kasa samun ganin gidajensu da idanuna, amma zai yiwu in ga gidajensu da kunnuwana.

Wani kuma yace,

Sun kasance su ne qawar duniya a lokacin rayuwarsu,

Kuma su a bayan mutuwarsu su ke qawata tarihi da littafai.6

Don haka, ya kai xan uwana mai karatu! Kutsa kanka sosai a cikin fadamar tarihi don ka sha ni'ima a cikin inuwar bishiyoyinta, ka ni'imtu da kallon daxaxan furanninta da xanxanar zazzaqan ababen shanta.




Qa'idodin karanta tarihi:

Qa'ida ta Xaya: Mai karatu ya qudurta koyi da magabata:

A yau mu na fama da qarancin aiki tare da tarin ilmi. Duba yawan ayoyin da mu ka sani da hadissai da labaran magabatan kirki waxanda ya kamata ace mu na aiki da su kamar yadda Allah yace:


أُولَئِكَ الَّذِينَ هَدَى اللَّهُ فَبِهُدَاهُمُ اقْتَدِهِ الأنعام 90
Ma'ana:

Waxancan su ne waxanda Allah ya shiryar, To, kayi koyi da shiriyarsu.

Ga wani misali mai muhimmanci game da koyi da Manzon Allah (SAW) a wurin magabata. Bukhari ya fitar da hadisi a cikin ingantaccen littafinsa7 cewa, Abdullahi xan Umar (RA) ya kasance ya na kiyaye wuraren ibadar Manzon Allah (SAW) a hanyoyin Madina, sai a gan shi ya na sallah a wasu wurare waxanda Manzon Allah (SAW) ya yi sallah a cikinsu. Har ma da akwai wata bishiya wadda Manzon Allah (SAW) ya yi sallah a qarqashinta Ibnu Umar ya rinqa kula da ita ya na ba ta ruwa don kada ta mutu.8

Shugaban mabiya Sunnah Ahmad binu Hambali yace, ban tava rubuta wani hadisi ba sai na yi aiki da shi. Watarana sai na cimma hadisin da yace Annabi (SAW) ya yi qaho, ya bai wa wanzamin Abu Xaibah dinari xaya, sai na yi qaho na bai wa wanzami dinari xaya don in yi koyi da shi.9

Ibrahim binu Hani yace, Ahmad xan Hambali ya nemi in samar ma sa wani wuri da zai vuya har kwana uku, sai nace ma sa, ya na da wahala ga reka baban Abdullahi. Sai yace, ba kome, idan ka yi zan saka ma ka. Da na samar ma sa wurin ya qare kwana uku ya fito sai yace min, Manzon Allah (SAW) ya vuya a cikin kogo lokacin da ya yi hijira. Bai kamata mu yi koyi da shi a wurin daxi mu daina koyi da shi a yanayin wahala ba.10

Kamar haka ne mu ke da buqatar gina al'umma wadda ke matuqar kula da aiki irin kulawarta da sanin abin da ta jahilta. Da haka ne mu ke iya samun albarkar karatu, mu ke bin hanyar waxanda Allah ya yi ni'ima akansu, ba waxanda Allah ya yi fushi da su ba, ba kuma vatattu ba.


Qa'ida ta Biyu: A kula da ingancin labari ko rashin ingancinsa:

Da daxewa maqiya su ka kewaye musulmi. Sun shigar da hadissan qarya da labarai marasa tushe a cikin tarihinmu. Sun gurvata wasu daga littafan tarihi da irin miyagun aqidunsu, sun kuma haddasa fitinu a tsakaninmu. Sun sanya savani da rashin jituwa sun yawaita a tsakanin musulmi. Amma duk wannan bai hana malaman musulunci su yi aikin da Allah ya xora ma su ba na tantance gaskiya da qarya. Sun yi wannan ne kuwa ta hanyar bibiyar asalin ko wace magana da in da aka samo ta. Wannan shi ake kira ilmin isnadi.

Imam Ibnul Mubarak yace, Isnadi ya na daga cikin addini. Ba don isnadi ba kuwa da kowa ya faxi abin da ya ke so.11

Shu'ubah yace, Duk hadisin da ba ya da "Haddasana" a cikinsa zulala ne kawai tun da ba a san asalinsa ba.12

Shugabannin Ahlulbaiti da daxewa su ka koka game da yawaita qarya da masu da'awar sonsu suke ma su. Ja'afar Al Sadiq yace, Mu Ahlulbaiti mutane ne masu gaskiya. Amma ba mu rasa maqaryaci da ke zuqa mana qarya don ya shafa mana kashin shanu a idon mutane.13

Don haka ya zama dole mu kula da wannan ilmin na isnadi da Allah ya kevanci wannan al'umma da shi, wanda kuma ya ke buqatar mu san maruwaita mu kuma yi amfani da kaifin basira wajen tantance kalamansu da rarrabe gaskiya daga qarya kamar yadda maqera su ke rarrabewa tsakanin zinariya da sanholama.


Qa'ida ta Uku: Sanin cewa, mutum duk xan tara ne:

Rauni da Jahilci da Kuskure da Mantuwa kaxan ne daga cikin halayen xan adam da Allah ya halicce shi da su. Manyan shugabanni da zavavvu mutanen kirki duk su na cikin faxar Allah Ta'ala da yace,


وَخُلِقَ الْإِنْسَانُ ضَعِيفًا سورة النساء: 28

Ma'ana:

Kuma an halicci xan adam mai rauni.

Haka kuma su na cikin faxar Manzon Allah (SAW) da yace, "Ko wane xan adam mai yin kuskure ne. Kuma mafifitan masu kuskure su ne masu tuba".14

Wannan magana ba ta faku ba daga zukatan bayin Allah mutanen kirki don kuwa sun yawaita faxarta a tsakanin masoyansu da mabiyansu. Misali, Imam Ja'afar binu Muhammad Al Sadiq (AS) yace, Ina sheda ma ku cewa, ni jikan Manzon Allah ne (SAW) amma ba ni da wani tabbacin kuvuta daga wuta sai ga aikina. Idan na bi Allah zai rahamshe ni, idan kuwa na sava ma sa zai yi mana azaba mai tsanani.15

Imam Malik binu Anas shi ma ya na cewa, Ni mutum ne da ke iya yin kuskure kamar yadda ni ke iya yin daidai. Don haka ku duba fatawata duk in da ta dace da Alqur'ani da Sunnah ku yi riqo da ita, in da kuwa ta sava ma su ku bar ta.16

Daga nan zamu fahimci cewa, masu cewa Imamai da Waliyyai ma'asumai ne su na zurfafawa ne kawai a cikin sha'aninsu, su na fitar da su daga 'yan adamtakarsu. Wannan ya fi zama suka a ga resu fiye da yadda ya ke yabo akansu.



Qa'ida ta Huxu: A tsarkake zuciya:

Tsarkin niyya sifa ce ta masu gaskiya. Mutum nawa ne ke maganar adalci amma a aikace za ka ganshi mai biye ma son zuciya, mai kau da kai daga hujjojin Shari'a, Sai ya hukuntar da hankalinsa ya vace ya vatar da mutane? Allah Ta'ala ya yi gaskiya da ya ke cewa,


وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّنَ اتَّبَعَ هَوَاهُ بِغَيْرِ هُدًى مِنَ اللَّهِ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ القصص: 50

Ma'ana:

Wane ne ya kai yawan vata daga wanda ya bi son ransa ba tare da shiriya daga Allah ba? Lalle ne Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai.

Me ya raba irin waxannan da mutanen jahiliyyah waxanda aka san su da hankali da basira amma da manzo ya zo ma su da abin da ya sava ma aikin iyayensu sai su ka buga kai a qasa su ka qi yarda su na masu cewa,
إِنَّا وَجَدْنَا آَبَاءَنَا عَلَى أُمَّةٍ وَإِنَّا عَلَى آَثَارِهِمْ مُقْتَدُونَ الزخرف 23

Ma'ana:

Mu, mun sami ubannenmu a kan wata hanya, kuma lalle ne mu muna tafiya akan sawunsu.

To, ina basirarsu ta ke? Ina gwanintarsu ta je ne?

Mu na buqatar mu tsaya mu lurar da kawunanmu cewa, gaskiya ita ce ta fi cancanta a bi ta akan kome. Kuma duk abinda ya sava ma gaskiya, magana ce ko aiki, aqida ce ko ra'ayi, mu yi watsi da shi. wanda ya zo mana da gaskiya mu karva, wanda ya zo da savaninta mu bar shi da kayansa ko wane ne shi, tare da qaunarsa da girmama shi idan ya cancanci a qaunace shi ko a girmama shi. Mu tuna irin tambayar da za a yi mu na a gaban Allah ranar alqiyama, ita ce;


مَاذَا أَجَبْتُمُ الْمُرْسَلِينَ القصص (65

Ma'ana:

Da me kuka karva kiran manzannina?


Qa'ida ta Biyar: A mutunta Malamai da ladabi wajen ambatonsu

An karvo daga Ubadah binu Samit yace, Manzon Allah (SAW) yace, Duk wanda bai mutunta manyanmu, bai tausaya ma qanananmu, kuma bai san haqqen malamanmu ba, to, wannan ba shi a cikin al'ummata.17

Malam Xawus binu Kaisan yace, Yana daga cikin sunnah a darajanta mutane huxu: Malami, da Tsoho mai furfura, da Sarki, da Mahaifi.18

Don haka, wajibin musulmi ne ya darajanta Malami, ya mutunta shi, ya yi ladabi a wajen faxin sunansa tare da yi ma sa addu'ar samun rahama da gafara, ko malamin ya na raye ne ko bayan mutuwarsa. To, musamman kuma idan malamin ya kasance fitacce ne wajen taimakon gaskiya da yaxa sunnah da tozarta qarya da tarwatsa mutanenta.

Malam Abu Zur'ah Ar Razi yace, Ina tare da Ahmad xan Hambali sai aka ambaci Ibrahim binu Xuhman, xaya daga cikin malamai na Allah, a lokacin Ahmad ba shi da lafiya ya na kwance amma nan take sai ya tashi zaune, yace, bai kamata a ambaci mutanen kirki ba muna kwance.19
Qa'ida ta Shida: Hattara da sukar Malammai:

Musulunci ya haramta musulmi ya soki xan uwansa musulmi ko wane iri ne. Maimakon haka an umurce mu da mu kyautata magana ga junanmu da abin da zai faranta rayukanmu. Wannan wajabcin ya na daxa qarfafa ga haqqen malammai na Allah waxanda ke isar da addininsa su na karantar da mutane yadda za su bi gaskiya.

Kasa kunnenka ka ji wani labari da zai tabbatar maka gaskiyar abinda na ke faxa;

Wasu mutane daga cikin munafikai sunyi izgili da wasu alarammomi daga cikin sahabbai su kace, ba mu tava ganin makwaxaita masu qarya da tsoro kamar makarantan nan namu ba.20 Sai Allah ya saukar da Alqur'ani ya na tona asirinsu da ire irensu in da ya ke cewa,


وَلَئِنْ سَأَلْتَهُمْ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلْعَبُ قُلْ أَبِاللَّهِ وَآَيَاتِهِ وَرَسُولِهِ كُنْتُمْ تَسْتَهْزِئُونَ (65) لَا تَعْتَذِرُوا قَدْ كَفَرْتُمْ بَعْدَ إِيمَانِكُمْ إِنْ نَعْفُ عَنْ طَائِفَةٍ مِنْكُمْ نُعَذِّبْ طَائِفَةً بِأَنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ (66) سورة التوبة

Ma'ana:

Kuma lalle ne idan ka tambaye su zasu ce, mu dai kawai mun kasance muna kutsawa ne muna wasa. Kace, to, da Allah da ayoyinsa da Manzanninsa ne ku ke izgili? Kada ku bada hanzari, tabbas kun kafirta bayan imaninku. Idan mun yafe wa wata qungiya daga cikinku, to, zamu azabta wata qungiya domin sun kasance kangararru.

Kaicon wannan miskini ya na sukar mutanen da su ka qarar da rayuwarsu wajen taimakon addini. Ya za kayi suka ga wanda ya daxe da saukar da kayansa a cikin aljanna?

Malam Ibnu Asakir Ad Dimashqi yace, Lallai naman malamai akwai dafi a cikinsa, abin da Allah ya saba da shi kuwa na tonon asirran masu suka ga resu sananne ne, duk wanda ya saki bakinsa ya na suka ga malamai to, Allah zai jarabce shi da mutuwar zuciyarsa kafin mutuwar gangar jikinsa.


فَلْيَحْذَرِ الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَنْ تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ النور 63
Ma'ana:

To, waxanda ke sava ma umurninsa su yi saunar kada fitina ta auka masu ko azaba mai raxaxi ta cim musu. Suratun Nur, Aya ta 63.



Qa'ida ta Bakwai: Adalci shi ne, auna yawan sawabar mutum tare da yawan kurakuransa.21

Wannan qa'ida ce ta zamantakewa a tsakanin mutane. Mutum duk xan tara ne, amma wani ladarsa ta rinjayi zunubinsa kamar yadda kyautatawarsa ta rinjayi kurakuransa. Wani kuma savanin haka ne zunubinsa ya fi ladarsa, varnarsa kuma ta fi gyaransa. Ba adalci ba ne muyi watsi da mutum don kawai ya yi wasu kurakurai sai mu turbuxe alherinsa.

Malam Sa'id binul Musayyib, xaya daga cikin fitattun malaman tabi'una yace, Ba wani malami ko basarake ko attajiri face ya na da lum'ah. Amma duk wanda alherinsa ya yawaita har ya rufe sharrinsa to, shi ne abin yabo. Wanda ko duk sharrinsa ya yi yawan da ya rufe alherinsa to, shi ne wanda ya kamata ayi suka akansa.22


Taqaitaccen bayani akan matsayin gidan annabta

Akwai ababe da dama da ke nuna son Manzon Allah (SAW) waxanda suka haxa da darajanta iyalansa, da sonsu da jivintarsu da taimakonsu da kariyarsu, tare kuma da faxin matsayinsu da kyawawan ayyukansu, sannan da koyi da su.

An karvo hadisi daga Zaid binu Arqam (RA) yace, Manzon Allah (SAW) yace, "Ina tunayar daku Allah a game da iyalaina, Ina tunayar daku Allah a game da iyalaina, Ina tunayar daku Allah a game da iyalaina".23

Daga Abdullahi xan Abbas (RA) yace, Manzon Allah (SAW) yace, "Ku so iyalaina saboda sona".24

An karvo daga Abdullahi xan Umar (RA) yace, Abubakar Siddiq (RA) yace, ku kiyaye Manzon Allah (SAW) a iyalan gidansa.25

Don haka ne ya sa Sahabbai da Tabi'ai da sauran shugabannin musulmi magabata su ka kasance masu tsananin girmamawa da qauna ga iyalansa. Kamar yadda ya zo a cikin Sahihul Bukhari cewa, Abubakar Siddiq (RA) yace, Na rantse da wanda raina ya ke a hannunsa na fi son in sadar da zumuncin Manzon Allah (SAW) akan nawa.26

A lokacin da Abdullahi binul Hassan jikan Ali bin Abi Xalib ya je neman wata buqata a wurin sarki Umar bin Abdil Aziz, daga cikin sarakuna Banu Umayyah, sai sarkin yace masa, Daga yau ina fatar idan kana da wata buqata a wurina kar kazo da kanka, a maimakon haka ina son ka aiko xan saqo ko ka rubuto min wasiqa, domin ina jin kunyar Allah ya ganka a qofar gidana kana jira na.27

Shehun Malami Abul Walid Al Baji yace, Lokacin da sarki Al Mansur ya nemi Imam Malik ya xauki fansa akan gwamna Ja'afar binu Sulaiman wanda ya sa aka yi masa bulala bisa ga zalunci, sai Malik yace, "Allah ya kiyaye ni. Ai ba wata bulalar da aka xaga a kaina face na faxa a cikin raina cewa, na yafe masa saboda dangantakarsa da Manzon Allah (SAW).28

Shi ma Imamu Ahlis Sunnah, Ahmad binu Hambali lokacin da ya gamu da tasa jarrabawar, aka yi masa duka a zamanin sarki Al Wasiq, sannan daga baya Allah ya xaukaka al'amarinsa (Shi Ahmad), Sai Al Wasiq ya roqe shi ya yafe masa, sai yace, Daman can ni na yafe maka tun da farko saboda matsayin kakanka (SAW).29

Ga wani waqe mai armashi da Di'ibil Al Khuza'i ya yi game da son dangin Mustafa (SAW). A cikinta ya nuna tsananin qaunar da ya ke yi ga Alhulbaiti waxanda yace, ya fi sonsu da nasa dangin, kuma ba ya shiri da kowa idan ba mai qaunarsu ba ko da kuwa ciki xaya su ka fito.30

Wannan shi ne halin musulmi a duk in da aka fito.Amma a yau kam mutane sun kasu kashi a game da Ahlulbaiti kashi uku;



Yüklə 296,5 Kb.

Dostları ilə paylaş:
  1   2   3




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©genderi.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

    Ana səhifə