Karban shawara daga wurin allah "Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya gama su za su ga Allah." Daga



Yüklə 361,5 Kb.
səhifə6/11
tarix17.09.2018
ölçüsü361,5 Kb.
#68717
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11

Babi Na 4



Tunani Akan Kristi Kadai
Ko ka taba haduwa da wata yanayi wadda kana cikin murna, kana jin dadin rayuwa, da kuma cike da yabon Allah domin rai wadda ya ba ka sai nan da nan kawai a cikin wasu yan mintoci, wata fushi ko bacin rai ta bazu a cikin zuciyarka ta kuma mamaye duka farin cikinka? Ta yaya ne irin wannan canji ta ruhaniyar mutum ke faruwa? Akwai abin da za mu iya yi domin mu maganta wannan kokuma mu canza sakamakonsa? Da na soma gane kalmonin mai sara da mai lallasa a zuciyata sai na soma ganin yawan irin wadannan “canza canza” a rayuwata, wannan kuma ta dameni sosai na nemi nufin Allah game da wannan domin ya ba ni wahayi wanda za ta sa ni in gane tushen wannan al’amura da kuma yadda zan sami yani daga ita. Sai watarana, a wata ranar lahadi, ina cikin majami’a wadda nake yin aikin fasto ina durkushe cikin addu’a a gaban bagadi, domin Allah ya ba ni koyaswa na wasu babban anabara biyu na wannan zamaninmu, wato Dakta Paul biyu Cho da kuma Kenneth Hagin, wannan koyaswa ta gaskiya ta juya yanayin rayurata da na almajiraina.
A nan ne na sami wayewa game da cewa ruhohinmu suna da farne biyar ta sunsuna abubuwa, kamar yadda jikinmu take. Idan kuwa muna da kwazo domin ciyar da wadan nan farnonin biyar da tunani a kan Allah a kullum, wannan aya ta Filibbiyawa 4:8 cata zama gaskiya a rayuwarmu:

“A karewa, yan-uwa, iyakar abin da ke mai-gaskiya, iyakar abin da ya isa bangirma, iyakar abin da ke mai-adilchi, iyakar abin da ke mai-tsabta, iyakar abin da ke jawo kamna, iyakar abin da ke da kyakkayawan ambato idan akwai kirki, idan akwai yabo, ku maida hankali ga wadannan.”


A nan ne dukan yanci, da farin cciki daa kuma rai mai yalwata wadda an yi wa ‘ya’yan Allah alkawali akai ta ke zama!.
Mene ne wadannan farnoni na sunsuna guda biyar na ruhohinmu? Mun rigaya mun yi magana game da guda biyu wato kunne da kuma ido na zuciyarmu. A hade da wannan ruhunmu tana da rai na ciki da nufi da kuma ji na jiki Watakila ka taba jin wannan koyaswa yaddan nima na gane cewa, ranmu na da, rai nata, da nufinta da kuma ji na jiki nata. Bayan na yi nazari sosai daga Littafi Mai Tsarki, na iske cewa, duk da shi ke rai tana da irin wandannan farnonin amma na ga cewa akwai irin su a farnoni na ruhu wadda ta fi na jiki da narai zurfi.
Wadannan farnoni na sunsuna su ne kan gaba na ba mutum hikima domin kikkiro sabobin dabaru. Daga wurinsu ne abubuwa na ruhaniya suna samun shigowa ko kuma zama abubuwa na duniyar jiki. Wadannan farnonin suna aiki a kullum domin su haifar da wata al’amura daga ruhaniya zuwa duniya ta jiki. shaian yana iya cika su da hallaka da razana ko kuma Ruhu Mai Tsarki ya cika su da rai da bege.

Kamar yadda akwai mataki uku kafin haihuwa ta auku haka ma akwai mataki uku a wannan bangare to ruhu:
Yin Ciki

Wannan na aukuwa idan kunne mai zurfi na ruhu ta ji kalma daga wurin shaitan ko kuma Ruhu Mai Tsarki, da kuma.


Ido mai zurfi ta ruhaniya ta ga wahayi daga shaitan ko kuma Ruhu Mai Tsarki.
Rikon Ciki

Rai mai zurfi tana zurfin tunani game da kalma ko kuma wahayi kenan,


Wato nufi mai zurfi ta nace kuma muna soma magana daga ababan da sun cika zuciyarmu, da kuma.
Ji na ruhu mai zurfi suna tasowa domin su sa mu aikata abin da kalma da wahayi ke nuna mana.
Haihuwa

A karshe, al’amura ta ruhaniya ta zama ta jiki kenan.


Ta yaya ne wannan ke faruwa a rayuwarmu na yau da kullum? A ce ka shigo majami’a ranar Lahadi da safiya, kana nan cikin kauna da farin ciki a cikin Ubangiji sai ka hango wani idon sani a zaune can karshen gefen majami’ar. Ka kuma yi mata gaisuwa da hannu har da murmushi a fuskarka, amma bata amsa maka ba! Ta kuma daure maka fuskarta ta kuma kau maka da fuska Nan da nan mai saran nan ya fara aikinsa a zuciyarka yana. cewa, “Wai me ke damun wannan yar’uwa Susie ne ni kam? Hankalinta dai yau na cikin bakin ciki. A gaskiya dai abin kamar hankalinta ta sake gaba ki daya a makonin nan. Ba ta murmushi kamar na da. Watakila tana juyayi ne domin zunubanta. I, kuwa haka ne, babu shakka. I kuwa, watakila wannan damuwan nan da ta taba gaya mani kwanakin baya, na tabbata ta fadi cikin wannan hali na zunubi ke nan. Watakila ma ta ja da baya kenan! Ai ma ba taba daukan ta kamar wani Kirista na gaskiya ba. Ban ma taba daraja abokantakarta ba, ba ta ma isa irin nawa daraja ta girma cikin ruhaniya ba”.


A yayin da ana cikin wa’azi, sai kai kuwa hakalinka na ta jin irin sara na iblis kana kuma ganin irin rayuwa ta zunubin yar’uwanka, har ma kana tunanin yadda za ka raba abokantaka da ita. Ka bar zuciyarka a bude domin shaitan ya cika ta da duk karyar da ya iya hadawa. A karshen jawabin Fasto, zuciyaaka ta rigaya ta ciku da karya kana kuma marimarin ka bide baki ka yi magana ne kurum. Daga nan kuwa sai ka juya ka yi magana da wanda ke kusa da kai (cikin juyayi ta tausayi irin na Allah mai zurfi) cewa, “Kai, ko ka lura da yar’uwa susie a wannan watannen nan kuwa? Ni a gani na ta rigaya ta kauce daga hanyar Ubangiji Tana ware kanta daga zumunci da sauran mata a cikin Kristi, kuma ka san irin hasarin da wannan ke kawowa. Na tabbata tana cikin zunubi sosai...” A yayin da wannan irin dafi tana fitowa daga bikinka kuma zuciyarka na kunawa domin ka aikata tunaninka. A yayinda za ka fito ke nan sai kana kokarin ka fita ta kofa ta gefe, domin dai kada ku hadu, nan sai ka bi ta wata hanya wanda za ka bi domin ka hadu da Fasto ku kuma sha hannu.
Amma a ce in da ka maganta wannan karya daga bakin shaitan wanda ya harba wa zuciyarka, ka kuma ki karbanta, ka la’anta wannan sara nasa, ka kuma juya ga Kristi domin jin murya ta gaskiya, to, da me za ta faru? Watakila Ruhu mai Ta’aziya din nan zai ce maka, “yar’uwanka tana cikin tsanani sosai a yanzu. A wannan lokaci na tsanani da gwaji tana ganin kamar na guje ta gaba daya. Ba ta iya sunsuna kaunata domin tana ganin cewa na ware kaina da ita, tana ji kamar ba ta isa karban kaunata ba. Tana bukatar kuunarka a yau fiye da dukan komai da komai. Ina so ka zama hannayena zuwa a gareta a yau. Ina so ka rungume ta ka kuma nuna mata irin matukar kaunar da nake da shi a gareta”.
A dukan lokacin da jawabi ke tafiya, hankalina na nasuwa da irin wannan kalma wanda Ruhu ya gaya maka da kuma wahayin da ka karba daga wurinsa. Amma, a yanzu tana kawo maka tunani ta kauna da rai a ruhunka. Ana bakin gama sujada ke nan, sai ka ruga zuwa wurin Susie domin ka furta irin zancen da ta cika zuciyarka. Bayan ka yi mata wannan magana ta kauna da jinkai, cewa, “Allah yana matukar kaunarki, kuma ni ma in kaunarki,” nan da nan hawaye ta warkasuwa za ta zuba, kuma abokantaka za ta komo kamar yadda da take, bangaskiya kuma za ta sami karin kafuwa.
Yanzu ta rage na mu. Wa za mu ji? Kalmar wa za mu yi tunani a kai? Umurnin wane ne za ta motsa mu har mu yi magana da kuma aiki? Za mu zama masu kayaswa ne ko kuma masu sulhu? za mu kawo cuta da azaba ne ko kuma warkasuwa ga wadanda muka taba?
Bari in kara ba da wata misali! A ce, maigidanka na ofis ya kara maka girma wurin aiki. Wannan tana bukatar kara daukan nauyi, wadda kuma tana bukatar karin ilimi da koyo. Nan da nan magabci ya yi maka magana a kunne cewa, “Ai ba irin wannan aiki ka ke so ba! Ai ba ka bukatar irin wannan wahala. Ai komai na tafiya daidai a da. Ka da ka jawo wa kanka wata illa. Idan ka dauki wannan matsayi ai mutane da yana za su riga dangana a kanka. Idan kuma ka yi kuskuri kowa da koma zai sani ya kuma ba ka laifi. Kuma ka sani cewa dole ne ka yi kuskure. Ai yanzu ma ka fi karfin ka koyi sabobin abubuwa domin ka rigaya ka yi tsufa. Wannnan harka tana da wuya. Ba za ka dai iya yin wannan ba.”
A yayin da kana yin wannan zancen da matanka da dare, zuciyarka na ta cikuwa da karin irin kasawarka ne kurum. Ba ma wai zaka kawo wa kamfaninka damuwa kurum ba, ga shi ma za su yi rashin kudi domin rashin iyawarka. Wannan kuma za ta kawo asara ga wurin aikinka har a ma rufe kamfanin, a kuma koreka daga aikin ka kuma rasa daraja a gaban abokanka, domin dukan su sun sani cewa kai ne ka jawo dukan wannan bala’i. Domin wannan firgita sai kashi gari ka gaya wa maigidanka a ofis cewa, “Na gode da wannan karin da ka ba ni, amma wurin da nake ta ishe ni.”


To, amma me za ta faru, idan ka ki muryar wannan makaryaci a nan da nan daga zuciyarka? Me Ruhu za ya fada game da wannan? Watakila zai ce maka, “Yau ga abu mai kyau ta faru, ga hanya an ba ka domin ka yi girma ta wurin koyon sabobin abubuwa! Kana nan cike da hikima da kuma karfi, domin haka za ka ciku da ilimi a wannan sabon nauyin aikin. Idan ka sa bangaskiyanka a gare ni, ka kuma cika ranka da maganata, zan sa ka ci nasara a dukan aikinka. Za ka iya yin kamai domin karfina ta cika dukan rayuwarka.” Nan da nan sai wahayi ta nasara ta mamaye ranka, a yayin da kana tunani game da kalmoni na rai. Daga nan sai ka nace a zuciyarka cewa za ka yi iyakacin kokarinka ta wurin Kristi domin haka sai ka karbi wannan sabon matsayi.
Ina fata ka soma gane irin gurbin da wannan irin aukuwa ke daukawa a ruhohinmu. Ko mun sani ko kuma ba mu sani ba, zukatannu suna aiki a kullum domin su kirkiro abubuwa daga duniya ta ruhu zuwa duniya ta jiki. Domin haka wajibi ne mu zura wa Kristi idanunmu da kunnuwanmu domin mu ciku da shi kurum, domin iri na adilci ta sami girma da haihuwa ta wurinmu.
Yesu ya ce, “Fitillar jinkinka idonka ne: kadan idonka sosai ne, duka jinkinka kuma chike da haske ya ke, amma kadan mugu ne, jikinka kuma chike da dufu ya ke (Luka 11:34-36).” Idanunmu ta ruhaniya su ne kayan aiki mafi karfi domin aikata kirki ko mugunta wanda Allah ya kira a aikin mu. Na bada gaskiya cewa, iya hada setin idanunmu na ruhaniya ita ce abu mafi karfi a dukan al’amura ta rayuwannu. An gaya mana cewa, mu “zuba ido ga Yesu shugaban bangaskiyarmu da mai-chikanta... (Ibraniyawa 12:2).” Ta wurin zura wa Yesu ido ne kadai za mu iya samun gani ta sarari domin dukan jikinmu ta ciku da haske. Idan ba mu mika su ga Kristi domin su sami cikakken haske ta Allah ba, nan da nan, shaitan zai kawo duhu da kwadayi, da tsoro, da kasawa, da kuma rashin iyawa ga dukan jikinmu.
Idan mun ji magana ko mun karbi wahayi daga gurin Allah, ya kamata mu shuka ta cikin zuciyarmu ta ruhu, domin ranmu ta ruhu da ra’ayinmu ta ruhu da ji ta jikinmu ta ruhuniya ta jiku sosai da kalmar. Ta haka ne za mu dauki ciki na cika nufin Allah mu kuma zama masu daukan ikonsa mai daraja duka a cikin wannan daukan ikonsa mai daraja duka a cikin wannan duniya. Ranmu tana kuma tunani ne kurum game da irin al’amura ta Allah, dukan shakka da jan baya na shaitan kuma ba ta samun wuri a cikinta. Muna kuma amfani da ra’ayinmu na ruhu domin furta zance a cikin bangaskiya bisa duk abin da Allah ya fada. Kuma idan jikinmu ta ruhu ta kunnu da hasken wahayin Allah, wannan tana sa mu mu tashi mu aikata abubuwua cikin bangaskiya bisa alkawarin da Allah ya ba mu, mu kuma sa bege domin ganin al’ajibansa. A cikin lokacinsa, ba dai namu ba, zai cikata alkawarinsa a garemu, domin sunansa shi sami daukaka. Zai jira sai ya ga cewa, mun daina kokarin mu cika alkawarinsa da kanmu. A yayin da kowa ya ga cewa wannan kalmansa a garemu ba za ta yiwu ba a karfinmu ta jiki, shi za ya aikatata a irin nasa hanya ta ruhaniya.
Ibrahim, Uban Bangaskiya

Ibrahim shi ne ainihin misalin irin wannan aukuwa. A Farawa 12:2, Allah ya yi masa magana fuska da fuska cikin zuciyarsa cewa, “Daga wurinka zan yi al’umma mai-girma.” Ga alkawali mai daraja! Ga kuma kalma mai jawo cin gaba, mai ginawa, da kuma kawo farin ciki! Idan kana rubuta rahoton abubuwan da Allah ke fada, kai ma za kz iske cewa kalmomi Allah kalmiomin ne masu daraja, da kawo cin gaba, da ginawa da kuma kawo farin ciki. Shi ma zai yi alkawalin ya aikata ababa masu daraja ya wurin hannunka. Amma magabci zai yi kokarin ya sata wadannan alkawalin daga wurin ka, cewa, “Ai Allah ba za ya tabba amfani da kai ba. Ka dubi yadda kai ka ke mana.” Amma a irin wannan yanayi ta kayaswa wanda ke zuciyarmu, sai Ruhun Allah ya busa mana nufinsa a zuciyarmu cewa, “Zan yi amfani da kai. Ka dube Ni da yadda NA KE!”.


Bayan shekaru guda goma sha daya, Ubangiji ya sake ziyartar Abram. A wannan lokaci. Allah ya nuna masa taurari na sama da kuma yashi na teku a cikin wahayi. “Haka zuriyarka za ta zama” Ubangiji ya gaya masa. Abram kuwa gashi nan dai, shekarunsa tamanin da shida, tsoho mara da. Ta yaya za ya amusa wa irin wannan alkawali? “Sai ya bada gaskiya ga Ubangiji...” Abram ya badagaskiya ga kalmar da Allah ba shi fuska da furka na shekarun da suka shige, domin irin aikinsa ta nuna cewa yayi biyayya da wannan zance. Amma wannan bangaskiya wadda ta zo a sakamakon wannan wahayi ta yi zurfi da kuma karfi sosai shi ya sa aka yi magana a kanta cikin Littafi Mai Tsarki. Irin wannan ne ikon da ke cikin wahayi. Ta na karfafa alkawali, tana kuma bada siffa ga ababan da ba za a iya gani da ido ta jiki ba.
Bayan ya karbi wannan kalma da kuma wahayi, Ibrahim ya cika ransa na ruhu da tunani ta bangaskiya ne kurum.
Shi wannan bisa ga kafa bage ya bada gaskiya sikija sabain tsammani... Ba ya kwa bar bangaskiya ta yi rauni ba, ko da ya lura da jiki nasa daidai kamar matache ne... Garin kafa ido bisa alkawalin Allah, ba ya raurawa ta wurin rashin bangaskiya ba, amma ya karfafa ta wurin bangaskiya... Yana kwa sakankanchewa sarai, yana da iko ya chika abin da ya alkawarta... (Romawa 4:17-22).”
Ko da yake shekaru masu yawa sun wuce ba tare da ya ga alamar cikawar alkawalin Allah ba, Ibrahim bai motsa daga bangaskiyarsa ba amma ya cika ransa da kalma da kuma wahayin da Ubangiji ya ba shi.
Shekaru guda goma sha uku suka wuce ba tare da da ba. A karshe, Allah ya ziyarce Abram da wani umurni cewa, “... Ibrahim ne sunanka gamma uban jama’ar al’ummai na maishe ka (Farawa 17:5).” Wato wannan sabon sunan na tuna masa kalmar Allah a kowane lokacin da ya kirata. “Barka, ni ne uban al’ummai.” “Kana da yaya nawa ne?” “Babu ko daya tukuna, amma Allah ya yi mani alkawali!”


Ya kamata mu lura da lokacin da wannan umurni ta furta (jan ayar Allah) ta zo masa. Ibrahim yana tunani cikin zuciyarsa game da wannan kalma da wahayi daga wurin Allah na wajen shekaru ashirin da hudu. Ya rigaya ya dauki cikin wannan kalmar, yana da cikin wannan alkawali ta Allah! Idan mun ja ayar Allah a cikin bangaskiya, mutanen duniya suna ganin mu kamar wawaye ne kurum, har ma domin wannan suna yi mana ba’a da sara sosai. Idan irin wannan ba’a ta faru da mu yayin da iri tana nan dan karami tukuna, kuma bamu sami kafuwa da karfi ba tukuna, babu wuya a zubar da cikin wannan wahayi da kalma. Amma idan tsanani ta zo a daidai kusa da loton da za mu haihu, muna iya jimrewa mu ce, “I, na san cewa wannan gaskiya ne. Wannan kalma tana ta girma a cikina kuma ga shi ta yi kusan ta bullo wa duniya. Babu abin da za ta hana ni furta bangaskiyata!”. Furta aya tana da muhimmanci a wurin halittan abubuwa sosai amma biyayya da Allah game da loton da ta kamata a soma furta maganarsa de furta maganar duk suna da muhimmanci.
Allah kuma ya ba Ibrahim umurni game da kaciya a daidai yana da shekaru tasa’in da tara (Farawa 17:10-24). Har zuwa wannan lokaci ba wanda ya yi wani magana game da sharadin wannan alkawali. Amma kunnuwan Ibrahim na cikin zuciyarsa tana nan a farke domin ya yi biyayya ga Ruhu a nan da nan. “A chikin wannan rana fa aka yi ma Ibrahim kachiya... (Farawa 17:26).” Ka lura da cewa Ubangiji ya ci gaba da ba Ibrahim umurni game da ababan da ya kamata ya yi a lokacin jiran wannan cikawar alkawalinsa. A duniya ta jiki, mace mai ciki tana yin abubuwa masu yawa domin shirin loton da haihuwa za ta auku. Tana samun taimako daga hannun likita, tana cin abinci masu gina jiki, tana kuma hadiye manya manyan kwayoyin vitamin, da kuma horon jiki, domin ta shirya zuciyarta da jikinta domin ranar haihuwa, har ma da shirya dan karamin daki domin jaririn da ke zuwa. Ta haka ya kamata muma mu shirya wasu abubuwa domin haihuwan wahayin da Allah ya ba mu. Allah za ya gaya mana abin da za mu yi har ma da lokacin da za mu yi ta. Dole mu yi biyayya nan da nan ga umurnin kalmarsa. Ba ta isa ba idan mun ce kawai “Ai, Allah ya yi mani wannan alkawali tun shekaru ashirin wanda suka shige” Dole ka lura domin ka san ko me yake fadi game da wannan alkawali a yau.


A karshe, bayan jira ta shekaru ashirin da biyar, sai ga aikin al’ajibi na Allah ta wurin haifuwar Ishaku. Wannan dai ba karshen tarihin ba. A lokacin wannan jira Ibrahim ya yi kuskuri guda daya. “Abram kwa ya ji maganar Saraya (Farawa 16:2).” I kuwa, lokaci mai yawa ta wuce, ba ko alamar cikar wannan alkawali. Watakila Allah na jiransu su yi wani abu dabam. Watakila wannan ita ce lokaci ta kafa komiti domin su duba usannan al’amura domin a yi taro a ga yadda za a taimaki Allah domin a cika nufinsa. Don wannan Ibrahim ya manta da muryar Allah na dan lokaci kadan domin ya ji hikima irin ta duniya. Sai bayan Allah ya sake ziyartarsa domin ya yi masa magana, sai Ibrahim ya nuna ma Allah sakamakon kokarinsa yana cewa, Da dai ka yarda Ismailu ya kasanche a gabanka! Ka ga irin aikin da muka yi, ya Ubangiji? Mun yi da yadda ka ce za ka yi. Wannan ba ta cancanta ba ne? Wannan ba ita ne cikawar alkawarinka ba?” Amma Allah ya ce, “A’a...” (Farawa 17:18,19).” Kokarinmu ba za ta taba iya cika nufin Allah ba. Idan dai mun ci gaba da kofarin mu aikata nufin Allah da kanmu, kokarinmu za ta zama abin hana cikan wannan wahayi, kuma haka wahayin za ta ci gaba da zama a wofi. Sai dai bayan mun gama duk kokarinmu har dukan karfinmu ta jiki ta kare kaf tukuna na ikonsa ta ruhaniya za ta motsa ta cika nufinsa domin shi karbi ya danki daukaka.

Takaitawa


A karshen wannan babi za ka ga wata jeri wanda ta takaita dukan ababan da aka tattauna a nan. Wannan jerin ba abu mai canzawa ba ne: Zaban wanda za mu ji muryarsa da wahayinsa tana a hannunmu, mu ne za mu zabi wanda kalmarsa ko wahayinsa za ta yi girma ta kuma sami haihuwa a cikinmu.

Amsa


Ya kamata ka ba Allah dama ya yi amfani da wandannan darasai na gaskiya domin su yi amfani a rayuwarka. Idan ka na neman shawara daga murin Allah, dole ka hadu da shi, ka yi magana da shi ka kuma kasa kunne domin ka ji daga wurinsa. Ka dauki littafin rubuta rahotonka ka nemi wuri mai shiru kai kadai domin shi ya bayyana maka. Wace irin mafarki ne ya nuna maka? Ko ka cire begenka daga mafarkin da aka ba ka? Ko kana cin gaba da tunani akansu a rayuwanka? Kana furta su da bakinka kamar yadda Allah ya umurce ka? Kana kasa kunne domin ka yi biyayya ga dukan abin da Ubangiji ke gaya maka, domin ya slirya manya ta cika maganarsa? Kana hutu daga cikinka domin ka bba Allah damaya yi aikinsa ta wurinka?
Tunani A kan Kristi Kadai

Ta wurin cika dukan farnen ji ta zuciya guda biyar da shi




ABIN SUNSUNA


YADDA AKE AMFANI DA SHI


MISALI DAGA BIBUL


MATAKI

1

Kunne Mai Zurfi (Yoh. 5:30)


Karban kalma ta Allah


Farawa 12:1-3


Yin Ciki

2

Ido Mai Zurfi (Rwuya ta Yoh. 4:1)


Karban Wahayi ta Allah


Farawa 15:5,6




3

Rai Mai Zurfi (Luka 2:19)

Yin Tunani Akan Maganar


Romawa 4:20,21


Rikon Ciki


4

Ra’ayi Mai Zurfi (Ayuka Man 19:21)

Yin magana cikan kalmar


Farawa 17:5




5

Ii taRuhu Mai (Sarakuwa J, 2:5)

Aikata Maganar Allah Da Wahayi


Farawa23





SAKAMAKO

Rasuwar Wahayi “Ni” ba zan iya aikata wannan abin ba

Farawa 16:2 Farawa 17:18,19


HAIHUWA





Tasowa daga matattu ta wahayi (ikan Allah) “A cikin lokacinsa ALLAH zai cikata alkawarinsa.”


Farawa 21:1,2


Galantiyaira 4:4a



“Muna zubba ido ga Yesu Shugban bbangaskiyarmu da mai-chikanta.” (Ibraniyawa 12:2)
“Nine Alpha da Omega, na fire da na baya, farko karshe.” (Ru’ya Ta Yohanna).

BABI NA 5

GANIN ALLAH A KWANAKIN BAYA

"Masu-albarka ne masu-tsabtan zuchiya: gama su za su ga Allah." To, me zan ce a lokacin da ba na ganin Allah? Me kuma zan ce game da irin munayen lokaci da aukuwa wadda suka jijjiga rayuwata a da, wadda har yanzu suna siffanta hali na a yau? Da irin lokacin nan masu aukuwa ta duhu, wanda dai na sani cewa Allah ba ya nan tare da ni? Ta yaya ne zuciyata za ta sami warkasuwa daga raunuka wanda na ji tun kafin in karbi Kristi?


Wannan Mai-Shawara mai Al'ajibi ne kadai wanda daukakarsa ta fi na lokaci, shi ne wanda za shi aza zama da mu a yanayi ta da da kuma yanzu a lokaci daya. Kristi ne "NI NE", na har abada. Shi ba "NI na da" ba balle ma "Ni wanda wanda zan zama nan gaba", ba amma shi "NI NE", na har abada a cikin loto ta yanzu. Rayuwarsa ta wuce karfin lokaci; ba ta uma da izini domin ta yi mulki da shi. Abu daya ne a gare shi ya bayana a lokaci na da ko kuma ya bayana a lokaci ta yanzu. A gaskiya, shi yana nan a zamaninka ta da da kuma ta yanzu da kuma zamaninka mai zuwa. Yana nan a koina kuma yana nan a nan a kullum. Shi ne Allah na nan da kuma yanzu, kowane lokaci a wurinsa a kullum ita ce nan da kuma yanzu. Wannan gaskiya tana da wuyan mu gane a cikin zukatanmu amma kuma gaskiya ce tuktur.
Domin wannan gaskiya ne, kuma Kristi yana nan a kowane irin lokaci, da da yanzu, da kuma gobe, kuma yana rayuwa a mulkin da ba ta da gurgunta na lokaci, shi yana iya yi mana taimako domin samun warkasuwa daga duka raunukan da mun taba ji a da. Mutane ne kiran irin wannan aukuwa da sunaye dabam dabam kamar: Warkasuwa ta ciki, warkasuwa ta tunanin ababan da, warkasuwa mai zurfi, ko kuma warkasuwa ta rai. Wadannan sunaye ba su da wata muhimmanci illa dai su nanata wasu darasi ta gaskiya daga Littafin Allah. A gaskiya, raunuka ta da masu zurfi na samun warkuwa ne ta wurin gafartawa da kuma barin Kristi ya yi aikinsa a ranmu da irin nasa warkasuwa ta Kauna.

Akwai ababa masu yawa wanda ba warkasuwa ta ciki ba. (1) Ba tattauna raunuka ta da domin samun warkasuwa ba. Ba kuma haka da debo duk faruwa ta da wanda ta yaki cin gaban mu ba. Amma Kristi ne mai tuna mana dukan irin wadannan aukuwa cikin sannu domin ya nuna mana wurin da za ya so ya warkar mana. (2) Warkasuwa ta ciki ba kai ne da kanka kana kaga wata aukuwa dabam da irin ta da ba. Wata sabon addini mai suna "New Age" wato Sabon Zamani, tana koyawa cewa a yi amfani da tunani ta kauna da aikin kirki domin ta mamaye irin aukuwa ta rauni wanda ta faru a da. Irin wannan gyara ta ababan da sun ji mana rauni a rayukanmu, ba na Ruhu Mai Tsarki ba ne, domin karya ne kurum, mun san kuma cewa Ruhun Allah ba za shi yi karya ba. Warkasuwa ta gaskiya tana faruwa ne idan mun ga Kristi yana aiki a cikin ranmu a kan abubuwan kawo rauni wanda muka gamu da su da. (3) Warkasuwa ta ciki ba jerin darasai na sharadin mutum ba, ko da ma a ce na nuna shi kamar haka. Warkasuwa mai zurfi, kamar sauran shawara daga wurin Allah, saduwa ce ta rai tare da Allah mai rai.

Akwai littafai masu yawa wanda a wallafa game da wannan darasi ta warkasuwa mai zurfi a wannan zamani ta mu. David Seamonds ya rubuta wata littafi mai lakabi a turanci, Healing for Damaged Emotions da kuma Rita Bennett ta rubuta wani mai suna You Can Be Emotionally Free, ina karfafa kowa wanda ke neman kari game da wannan darasi ya karanta wadannan littafan. A gaskiya, ba zan iya fadin dukan abin da wannan darasi ta kumsa a guntun babi daya kurum ba. A maimakon haka zan bada 'yar rahoto na wannan darasi daga ayukan Yesu wanda ke kumshe a Bishara ta Yohanna.
Wannan tarihin ta fara ne daga dare ta ranar kafin a giciye Yesu. Bitrus, mutum mai karfi da jimrewa yayi kokari domin ya kare abokinsa na ainihi. A cikin kokarinsa sai ya waina takobi a gaban askarawan da suka zo domin su kama Yesu, a wannan kokarin ya ci nasara ta wurin cire kunnaen mutum daya ne kurum. Amma a maimakon Yesu ya yi masa godiya da goyon baya sai Yesu ya tsauta masa sosai har ya sake

mayar wa ba'askarin kunnensa. Daga nan sai aka kai Yesu gaban babban firist domin shari'a, kuma babu abin da Bitrus za ya iya yi game da wannan. Ya jira mallaminsa a bakin kofar fada, domin ba ya so ya yi nisa da Ubangijinsa.

A yayin da yana duma kansa tare da sauran mutane a bakin fadar, sai wata kuyanga ta zo ta fallasa shi cewa "Kai ai kana tare da Yesu mutumin Galili." A cikin tsoro Bitrus yayi musun maganarta, ya kuma ware kansa daga wurin. Ba da dadewa ba, sai wani bawa ya sake maimaita wannan zance, nan kuma Bitrus ya yi musun sanin kome, har ma ya yi musun sanin Yesu gaba ki daya. A karshe, sai daya daga cikin wadanda ke tsaye a wurin ya nace da cewa, "Yadda ka ke magana ta tauna asirinka, Lalle kai daya ne daga cikin masu binsa." Nan da nan sai Bitrus ya sake yadda yake magana, har ya soma la'anta da rantsuwa, cewa, "Ni ban taba sanin wannan mutumin ba!" A bayan zakara ta yi shara ta wayewan gari, Bitrus ya fita ya yi kuka mai tsamani. A dukan Littafi ba mu taba jin wata labari wai Bitrus ya yi kuka ba sai a yanzu. A sarari dai wannan aukuwa ta kawo rauni mai tsanani a rayuwansa. Domin wannan ma sai ya bar kiran Allah a gare shi ta wurin aikinsa, har ya koma ga irin aikin da da ya ke yi.

Kwanaki masu yawa sun wuce. Yesu ya bayana wa almajiransa masu yawa a wurare masu yawa. Har ma ya je bakin tekun Galili wurin da wani babban mai kamun kifi yana kokarin ya manta da ababa na da domin ya ci gaba da rayuwarsa. A daidai wayewan gari, sai Yesu ya bullo mashi tare da abokaninsa wanda ke kamun kifi tare da shi. Shi kuma ya shirya masu abinci na kifi da gurasa daga wata yar wuta ta garwayi. Bayan sun gama cin abincin, sai Yesu ya soma tambayan Bitrus, "Siman, dan Yohanna, kana kauna na?" Bitrus kuma ya amsa, "I, Ubangiji, ka san ina kaunanka." Yesu ya amsa masa, "Ka lura da 'yan tumakina." Yesu ya sake maimaita abin da ya rigaya ya tambaye shi, Bitrus kuwa ya ba shi daidai irin amsar da ya ba shi a farko. Sun maimaita wannan ganawa har so uku.

To, mene ne manufar irin wannan saduwa? Na badagaskiya Yesu yana yin aikinsa na warkasuwa mai zurfi a rayuwar Bitrus domin irin sakamakon da musunsa na Yesu sau uku ya jawo. Ka lura da yadda wannan zani mai biye ta yi tagwaye da juna:




Matakin Da aka Dauka

MISALI DAGA BIBUL

(Bitrus: Matta 26:69-75/

Yoh.21:2-17)


1.

Ta wurin amfani da

wahayi, ka koma zuwa

cikin rauni ko azaba ta

da.


Gawayi mai wuta Safeya

Furta Kalmomi so uku



2.

Ta wurin amfani da

wahayi, ka shigo da Yesu

cikin wannan faruwa ta

da.


"Yesu ya tsaya a gabar

teku..." (Yohanna 21:4-

15)


3.

Ta wurin wahayi, ka bar

Yesu ya yi aiki hannu

sake, domin ya warkar da

raunin ta wurin fuskarsa

ta kauna.


Kalmomi na Yesu Domin

karfafa kauna.

- Yi kiwon yayan

tumakina


- Zama makiyayin

tumakina


- Yi kiwon tumakina

Bari mu yi zance game da wadannan mataki na kawo warkasuwa ta rai wanda aka yi amfani da shi a rayuwar Bitrus.

(1) Ka yi amfani da tunani ta wahayi domin ka koma zuwa ga lokacin da wannan rauni ta faru. Ta kamata ka ga duk irin abin da da ta faru ka ji irin zafi da kuma juyayi wanda ka ji a loton da abin ta faru. Amma kada ka bar irin yawan ji ta jiki wanda ta faru a lokacin ta mamaye hankalinka har ka manta da ganin Kristi a aukuwar. Idan irin wannan aukuwa ta zama da tsanani sausai, babu wuya Yesu ya kai ka wata wuri dabam a nan da nan. Amma dai, a tuna, amfani da wahayi tana da muhimmanci kwarai.

Ka lura da yadda Yesu ya canza wa Bitrus yanayin azabarsa: Kome ta faru a daidai lokacin da gari tana wayewa. Ta faru kuma a kusa da wuta daga gawayi. (A dukan cikin sabon Alkawali, a nan ne kurum sau biyu ake jin magana a kan wuta ta gawayi.) Kuma wannan ta shafi furta magana wajen sau uku.

(2) Ta wurin wahayi, ka gayaci Yesu domin ya zo ya bayana a filin wannan faruwa. Warkasuwa tana faruwa ne kadai, idan Yesu ya taba mu. Yana nan ma a wurin lokacin da wannan faruwa ta azaba ta abko mana. Watakila za mu iya tunani cewa, "Ai wannan maimunar abu ce! Ban yi sammani zai iya zama da ni a wannan lokacin ba." Amma Dauda mai Zabura ya ce, "Ko da a ce Ina nan cikin Hades, Kai kana nan tare da ni a wurin." Babu wata aukuwa wanda ta yi muni har ta iya sa shi ya bar mu. Muna tambayarsa ne ya bude idanunmu domin mu ga abin da ya ke yi a lokacin, domin kuma mu san abin da shi yake so ya yi a lokacin idan da a ce mun ba shi dama.

A Yohanna 21:4-15, "Yesu ya tsaya a gabar teku..." Ya zo ne wurin Bitrus domin ya shiga filin kasawarsa da kuma azabarsa.

(3) Ka yi amfani da wahayi, ka bar Yesu yayi aikinsa a saukake, domin ya warkar da azabarka ta wurin fuskarsa ta kauna. Zan sake nanatawa, cewa, wahayin da muke gani a nan ba na karya ba ce. Yesu na nan a lokacin da wannan bala'in ta abko mana. Rashin gani da kuma yawan barin rikicewa ta jiki ce ta boya shi daga fuskarmu. Yana aiki da kuma motsi, ko da shike mu bamu iya jin tafiyarsa ba. Amma yanzu bayan idanunmu sun budu, muna ganin Kristi kuma muna samun warkasuwarsa. A nan zan dakata, domin ba zan iya gaya maku irin abin da shi za shi yi ba, domin ba shi da iyaka ta irin hikima wanda za ya nuna game da damuwarmu. Zan iya fada ba da tsoro ba cewa, zai yi amfani da abubuwanda mu ba mu yi zato zai yi amfani da su ba. Daga wurin da muke za mu iya ce, "Shi zai yi wannan ko kuma wancan." Amma kikkirowa ta nazari ba za ta kawo warkasuwa ga rayukanmu ba. Ta wurin ma'amala da Kristi mai rai ne kadai za mu sami kubuta.

Akwai darasai na gaskiya masu yawa wanda za mu iya koya daga ganawan nan tsakanin Bitrus da Yesu, amma za mu sa hankalinmu game da daya ne kurum. Wace amsa ce Yesu ya ba Bitrus game da zancensa ta kauna? "Yi kiwon yayan tumakina; zama makiyayin tumakina; Yi kiwon tumakina." Abin nufi a nan shi ne, Yesu na cewa, "Bitrus, na yi maka aikin gafara. Na kuma karbe ka, ina so ka ci gaba da aikin da na nada ka ka yi. Na yi maka cikakken gafara."

Me ya sa Yesu bai sha hannu kurum da Bitrus ya ce masa, "Na yi maka aikin gafara, Bitrus. Ci gaba da aikinka?" Don me zai sa ya ba kansa wahala domin ya sake yanayin filin wannan azaban da ta faru? Dalilin ita ne, ji ta ruhaniya ba ta azanci da irin ji ta zance. Ruhu tana yare kamar ta hoto ne, kuma ta wurin wahayi ne ruhu tana samun tabuwa da kuma warkasuwa.



TAKAITAWA


Ta wurin aikin Yesu wanda muke kira warkasuwa ta rai ko kuma warkasuwa mai zurfi, muna iya ganin Kristi a cikin sakiyar azabar mu ta da. Idan mun mika idanunmu ta zuciya zuwa gare shi, kuma muka tambaye shi domin ya nuna kanshi da aikinsa a wadannan aukuwan, babu wuya a kullum zai ce mana mu gafarci wadanda sun yi mana laifi: Ba wai muna sha'awar maganganunsu ko ayukansu ba, amma ta wurin aikin gafara, muna iya kubutar da kanmu domin mu karbi gafara da warkasuwa daga wurin Allah. Su ma wadanda suka saba mana, suna samun yanci domin su karbi warkasuwa mai iko ta wurin Ruhun Kristi.

AMSA


Warkasuwa ta rai tana iya faruwa a hanyoyi dabam dabam. A yawancin lokaci tana faruwa ne a gaban bagadi wurin da mukan zuba duka damuwarmu da fushinmu a gabar Allah. Yana kuma ba mu ru'ya da wayewan kai irin ta Ruhunsa domin mu fito da warkewa da kuma sabon rayuwa daga gabansa. Ni kullum ina samun wannan warkasuwa a yayin da na ke rubuta rahoto. Bayan na gama mika kukekukena a gabensa. Yana amsa mani da kauna, da kuma alheri, ta haka hankalina ta ruhaniya tana dawowa. Idan mun ci gaba da girma cikin Ubangiji, irin wannan warkasuwa mai zurfi, tana faruwa "da kanta" wato (cikin ruhaniya). Idan mun karu a cikin saninsa, da kuma ganewansa, wannan ma'amala mai zurfi da shi tana kawo warkasuwa.

Wannan warkasuwa mai zurfi tana iya faruwa idan wani ko wasu sun yi addu'a tare da mu. Irin wannan tana da amfani sosai idan mun ci karo da al'amura wanda sun hana Kristi karasa aikinsa a rayuwarmu.

Idan kana da bukatar irin wannan aikin warkasuwa a rayuwara, ina baka shawara, ka fara zuwa wurin Ubangiji da kanka ta wurin rubuta rahoto. Ka tuna ka yi amfani da wahayi a dukan wannan. Ka rubuta dukan abin da za ta faru a zuciyarka a cikin rahotonka. Idan ka kasa samun saki ta wannan hanya, shawaran da zan baka ita ne ka nemi wani kwararre mai ma'aikaci ta addu'a da kuma warkasuwa mai zurfi, ka tabbata wannan irin mutumin yana da imani kuma ana zance mai kyau a kansa.

Mai-Shawara mai al'farma namu, yana marimari ya yantar da kai daga kowane irin hali ta fushi, da rauni, da asawa, da bakin ciki, da tsoro da kuma rashin cin nasara irin ta da wanda ke daura ka domin ya hana ka farin ciki a cikinsa. Idan ka iya ganin shi a dukan ababan da ke faruwa da kai, lalle ranka za ta sami warkasuwa.



Babi Na 8

Daga Fushi Zuwa Kauna

Wai akwai wani mutum ko mutumiya wanda ke kawo maka hawan jini daga ka ji sunansa ko ita? Ko akwai wani wanda shigowarsa zuwa dakinka ya kan kawo maka fushi da murdawan ciki? Akwai wasu abubuwan da suka taba faruwa a rayuwarka a da wanda zuciyarka na ta tuna maka a kullum, kuma tana cika ka da haushi da kuma bakin ciki? Idan ka ji an kira kalmomin nan "fushi" da " gafartawa", akwai wani suna wanda zuciyarka na tunawa a nan da nan?

Babu wuya mutum ya fadi cikin jaraban shuka fushi da kuma rashin gafartawa! Idan wani ya ci amanarmu ko kuma nuna mana sonkai, babu wuya tunani ta fushi su taso daga zukatanmu. Amma mene ne irin wannan tunani ta ke jawo mana idan mun yi fushi? Naman jikinmu tana yin tauri, wannan na ba ciwo da cuta dama su kama mu kuma ruhohinmu na rasa samun sakewa, wannan tana hana ruhunmu samun cikakkiyar karban karfi daga wurin Ruhu Na Rai. Wannan na sa mu zama bayi ga irin hali ta fushi, da kuma ga wanda mu ke fushi da shi. Domin muna ganin ayukansu kamar sanadin damuwanmu, wannan zata kawo rayuwanmu zuwa bauta ga wadannan mutane.

A cikin cututtuka da damuwa wanda ke jawo mutane zuwa wurin likitoci da masu bada shawara a duniya su ne fushi da kuma rashin yin aikin gafara. Za mu iya samun kubuta da warkasuwa daga wadannan illoli masu gurgunta mu idan mun zo wurin Yesu mai bamu shawara? I, wannan za ta yiwu, abin nema ne wurinsa domin ya ba mu Ruhu ta kauna wanda za ya ba ka yanci - yanci irin wanda ta fi kowane irin yanci wanda ke a rayuwarka.



Sanin Tushen Fushi

Fushi ba zunubi ba. Littafi ba ta bada umurni cewa kada a yi fushi ba. Amma ta ce, "Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi ... (Afisawa 4:26)." Fushi ba ita ce damuwar ba.

Amma yadda muke yi da fushin ne abin damuwa. Yadda muke bi da fushinmu ita ne take nuna ko muna nasara da zunubi ko kuma kasawa.

Idan fushi ba zunubi ba, to mene ne shi? Bill Gotthard ya ba da wata ma'anar kamar haka: "Fushi murya ne mai galgadi wadda ke cikinmu mai fallasa yancinmu wadda mun ba Allah ko kuma hana shi," Bari mu binciki wannan zance a hankali.

"Fushi murya mai galgadi ne na cikinmu ... " Fushi yana nuna mana cewa akwai damuwa a cikinmu. Tana bamu sako cewa akwai wata illa mai damun ruhunmu. Tana bude mana idanu domin mu yi tsaro akan zunubi wadda ke neman mallakar wata farnen rayuwarmu. Abu na farko shi ne mu bincike ko mene ne ta tada wannan murya mai kiran tsaro, bayan haka sai mu nemi hanya mu kashe wannan wuta wanda magabci yana nema ya kunna domin ya sata kwanciyar rai namu.

"Fushi ... na fallasa yancinmu wadda mun ba Allah ko kuma hana shi." An haife mu duka da yancinkai. Ka'idodin kasarmu suna karshe da "yancin kai ta rayuwa, sakewa da kuma neman samun nishedi. Amma a garemu masu bi muna iya kara wasu "yancin kai" wanda Allah ya ba yayansa - kamar su farin ciki, koshin lafiya, arziki, amsar addu'a da kuma duk abin da duk darikanka ke koyarwa na sakamakon ceto da alkawari. Muna cikin duniya ta yau wanda ta sa hankalinta ga k_re kanta daga dukan cin amana ta yancin kai da kuma neman karin yanci. Kotunanmu suna cike da mutane masu kawo karan juna ko kuma kungiyoyi domin an hanasu yancinsu. Wannan hali ta yadu har zuwa cikin Ikkilisiya, wadda ke neman abin samu, har ma daga wurin Allah. Da muka ji cewa kalmar Allah ya yi magana akan wata alkawali, sai ka ji mun tashi kim kim da cewa wannan namu ne. Ai dama wannan namu yanci ce!

Wannan ta kasa kwarai da gaskiya daga misalin da Ubangijinmu ya nuna mana. A cikin Filibbiyawa 2:5-8 mun ga wata tsari wanda ta banbanta sosai daga irin wannan ra'ayi.

"Ku kasanche da wannan Hali a chikinku wanda ke chikin Kristi Yesu kuma: Shi da shi ke chikin surar Allah, ba ya maida kasanchewarsa daidai da Allah abin rairaito ba, amma ya wofinta kansa da ya dauki surar bawa, yana kasanchewa da sifar matane; da aka iske shi chikin kamanin mutum, ya kaskantadda kansa, ya zama yana biyayya har da mutuwa, i, har mutuwa ta giciye."

Yesu yana da yanci a bauta masa kamar Allah, domin shi Allah ne! Ya kuma kamata a ba shi daraja domin shi ne Ubangijin dukan halitta. Yana kuma da yanci ya yi mulki akan dukan abubuwan da an halitta, domin shi ne mahalicci. Yana kuma da yanci domin rayuwa, domin dai shi ne mai bada Rai. Yana da yancin kai domin a ba shi shari'a ta gaskiya, domin shi mai shari'a na Adilci ne. Yana kuma da yanci ya amshi hukunci ta gaskiya domin shi ne mai Gaskiya.

"Ku kasanche da wannan hali a chikinku wanda ke chikin Kristi kuma." Allah yana so mu mika dukan yancin kanmu, da kayanmu, da dukan albarkun da muna ganin namu ne zuwa gareshi, mu kuma barshi ya yi abinda ya ke so da kuma yancin tunanin lokacin da za ya mayar mana da namu yancin a ganin damarsa. Watakila za mu iya bada gaskiya da cewa muna da "dama" a gan mu da daraja. Amma Allah ya ce "Ka ba ni darajarka." Muna ganin kanmu kamar muna da dama mu jera rayuwarmu da lokacinmu a daidai yadda ta kamata. Amma Allah na cewa, "Bari ni in zama Ubangijin lokacinka." Muna bada gaskiya cewa muna da yancin daraja kanmu. Amma Allah kuma na cewa, "Ka dangana a gare Ni." Nan ne shugabancin Ubangiji ta ke. Muna da marimari mu ba Allah dukan kome, kamar su yayanmu, aurenmu, gobenmu, lafiyarmu, abokanmu, hidimominmu, kudi da rayuwarmu, da jima'inmu? Mun bada gaskiya cewa yana kaunarmu, kuma yana so ya bi da komai domin ta zama mani abin nagarta? Za mu iya dangana a gare shi domin ya dauki dukan nauyin kowane abu mai muhimmanci ba tare da mun ba shi sharadi ko kuma taimakonsa akan yadda za ya aikata abin ba? Idan mun wofinta kanmu daga kome duka, kamar yadda Kristi ya yi, ba za mu sami fili domin fushi ba. Muna fushi ne domin mun bada gaskiya cewa an ci amanarmu. Ka yi tunani a kan wannan na dan lokaci. Ko ka tuna abin da ka yi fushi a kai na karshe kafin yanzu. Ko wata sonkai wanda ana nuna maka a wurin aiki ne? Me ta sa wannan ta baka haushi? Domin kana da "yanci" a gan ka da daraja da kuma a nuna maka gaskiya. Me ya sa kana fushi idan yayanka sun nuna maka rashin hankali? Domin kana da yanci ga darajanka da kuma neman ladabi daga garesu, kana kuma son gida mai kwanciyar rai da kuma son a sani cewa kai uba ko uwa mai daraja ne. Me ya sa kana fushi domin an bata maka kaya? Domin kayan ka ne, ka saye su da kudin zufanka, nauyin amfani da su na a hannunka, kana kuma da yanci ka sha romonsa sosai.

Domin haka, fushi ta zama hanya ne na ba mu galgadi akan abubuwan da muna rikewa da karfi domin bamu mika su ga Ubangiji ba ko kuma mun kwace ta daga wurinsa. Idan mun sake jin fushi na tasowa daga zukatanmu, bari amsar tsaronmu ta zama bincike ta zukatanmu, a ta hasken Ruhu, domin mu dago kowane "yanci" ne aka saba mana akai. Idan mun mayar masa da wannan yanci, nan da nan wannan fushi za ta kare.

Domin mu sami cikakken yanci daga fushi, dole ne mu: 1. Mika wa Allah wannan yanci (Fillibiyawa 2:5-8). 2. Mu sani cewa Allah zaya gwada wannan yancinsa (Farawa 22:1-14). Yanda an saba, dukan kowane mikawan kai yana jawo lokaci na jarabawa, ba domin ta kaskantad da mu ta wurin kasawarmu ba, amma domin ta nuna mafificin iko wadda muke kwancewa ta wurin ba da mulkin rayuwarmu ga Ubangiji ya yi ganin damarsa da rayuwarmu. 3. Idan rashin yanci ta abko maka, ka amsa da hali irin na Allah. Ba wai za mu zama taburman kofa marasa ra'ayi domin kowane bala'i ta musgune mu ba. Ba kuma wai za mu zama `yan tauri ba. Za mu zama masu sujada muna daukaka iko na Allah domin ya taimaka mana a kasawarmu, ya kuma juya wannan harka mai azaba ta zama abin nagarta a garemu. "Ubangiji ya bayas, Ubangiji ya karba, albarka ga sunan Ubangiji (Ayuba 1:21b)."

Ya kamata mu tuna cewa bin wannan tsari da naciya irin na doka ba za ta haifi rai ba amma sai mutuwa. Idan mu da kanmu, ta wurin iyawanmu, muka tashi da karfi dominmu hallaka fushi, mu kuma ba Ubangiji yancinmu, za mu zama marasa aukin ruhu, marasa auki a halayenmu, da kuma dolidoli na addini kurum. Wannan ba ita ne Allah ke nema daga wurinmu ba. Yana son mu cika da farin ciki, da murna da kuma lafiya da karfi! Abin da yana so tana zuwa ne ta wurin haduwa da Kristi.

Wannan aukuwa ta hanya zuwa Imwasu ita ce hanya zuwa yanci. Bari mu sake yin gyara ga tunaninmu a kan tsarin warkauswa. Idan mun ji haushi na tasowa mana daga ciki, dole mu 1) juya nan da nan zuwa ga Yesu mu kuma gaya masa abin da muke ji a cikinmu (Luka 24:13-24). A wurina, rubuta rahoto ita ce mafi aiki. Tuna fa, za mu fara yin magana da Yesu ne, ba tare da makwabtanmu ba. Idan mun fara zance a cikin fushi da wani, zamu ci gaba da fusata ne kurum kuma a karshe za mu kara fushi ne kurum ba tare da mun ci nasara na yin sulhu ba. Kada ka fara wata magana ta jan baya ba sai idan wani ya kawo hikima na Kristi, ta wannan hikima ne dukan ji na zuciya za ta sami sulhunta 2) Bayan mun janye zukatanmu sarai daga dukan tunani ta hallaka, dole mu yi tsit a gaban Ubangiji domin mu ji amsar da za ya ba mu (Luka 24:25-30). A wani lokaci zai ba mu wayewan kai game da wata aya. A wata loton kuma zai iya amfani da wani dan'uwa. Wani loton kuma za ya yi magana da mu ta wurin rubuta rahoto. Za ya nuna mana baiwa wanda shi ya ke so ya ba mu ta wurin bala'in da muke ciki. Watakila zamu kosa a cikin

halinmu ko ra'ayinmu, ko ibadarmu, ko bangaskiyarmu ko kuma jimrewarmu domin abin da ta faru, idan mun bar Ubangiji ya yi aikinsa domin ya juya wannan bala'i zuwa nagarta a garemu. Shi baya yarda da hali ta zunubi wanda ke kawo mana ciwon rai amma ya yi alkawali cewa za ya yi amfani da wannan bala'in domin nasa. 3. Dole ne mu hada maganarsa da bangaskiya mu kuma bi irin hali nasa. (Luka 24:31-35). Tabbatacciyar warkasuwa da kuma gafara na zuwa ne kadai ta wurin aikin Allah a cikin lokacin ciwon rai da kuma karban baiwa wanda yana bamu ta wurin wannan hali.
Gane Nufin Kauna

Na iske cewa wasu mutane sun fi wasu saurin fushi. Wasu kuma ba abin wahala ne ba su iya gafarta wa masu kawo masu hari. A garesu, ba abu mai wuya ba ne su ga hannun Allah a cikin yanayi ta wahala, kuma suna iya karban baiwa ta Allah daga wannan lokaci ta wahala ba tare da damuwa ba. Ga wasu kuma fushi abu mai sauki ne, kowane dan damuwa ya kan sa su yi fushi. Mutane kamar mu (i, ni daya ne daga irin wadannan mutane) yana bamu wuya mu yarda cewa wanda ya yi mana laifi yana da yanci a yi masa aikin gafara.

I mana, domin ni Kirista ne, fushina ai tana da gaskiya. Ba ma fushi na ke kiranta ba, "fushi ta adilci" ne bisa zunuban wasu! Idan na ga kuskure a koyasuwar wani, fushin Allah na motsa ni domin in fadi gaskiya. Idan wani dan'uwa ya kauce daga mikakkiyar hanya ta adilci har ya aikata abin kunya ga sunan Kristi ta wurin zunubi, tsarkakiyar fushi yana motsa ni in yi masa fada da kuma gyara. A lokacin, irin gani nawa kenan. Ina gani a lokacin cewa sanin gaskiya da kuma batawa, ita ce tushen addinin Kirista. Na bada gaskiya a lokacin cewa, tsabta ta koyaswa da kuma naciya ga koyarwa ta ibada ita ne lamba na addinin Kirista, da kuma lamba ta ba mutum izni ya yi zumunci da sauran yan'uwa.

Godiya ta tabbata ga Allah, wanda a cikin tausayinsa gareni (da matata, da yaya na, da kuma ikkilisiyata!) ya nuna mana wata hanya mafi kyau ta rayuwa. Ya nuna mani ta wurin littafi cewa Allah Haske ne da kuma kauna. Kowane kalmomi biyun nan suna nuna daya daga cikin irin halinsa. Me a ke nufi da wadannan kalmomin? Yaya ne hali ta haske ke bayana daga Allah, kuma ta yaya yake nuna kauna? Ka karanci wannan jeri a kasa.

Alla shi ne:

Haske da Kauna
Adilci ……………………………………………… Kauna

Shari'a Gafara

Kalubale …………………………………………… Sulhu

Kai Hari……………………………………………Warkasuwa

Rabawa………………………………………………Hadin kai

Kin Zunubi………………………………Kaunar Mai Zunubi

Kayaswa……………………………………………..Ta'aziya

Hukunci………………………………………………..Jinkai

Rashin Kuskure………………………………Matukar Alheri
Hali da aikin Allah suna a bayyane a wannan jeri ta sama. Rayuwata ta kunshi abubuwanda ke a jere ta farko ne kurum. Ina shiga yin kowane harka a shirye domin in sharanta adilcin bangaskiya na mutane, ina kuma kalubalantan dukan abin da na ga bata tsaya cikin tsari ba, kowane mutumin da na ke shakka da halinsa sai in guje shi, kuma ina naciya in gani cewa a bi daidai tsarin Doka idan za a hukunta dukan masu laifi. Irin wannan hali ne ta cika dukan ikkilisiyoyin da na taba shiga, har ma da koyasuwa na malamin makarantan Kirista wanda na shiga. Ina ce ko wannan daga Allah take. Amma dai wannan rabin gaskiya ne. Allah na nuna dukan irin wannan hali. Amma rayuwata bata nuna irin halin da aka jera a sashi na "kauna" din nan ba.

Ubangiji ya ja hankalina zuwa littafin Mikah 6:8: "Ya dai nuna maka, ya mutum, abin da ke mai-kyau; me ne Ubangiji yake bida gareka kuma, sai aikin gaskiya, da son jinkai, ka yi tafiya da tawali'u tare da Allahnka?" Allah na son nuna jinkai, amma yana yin hukunci domin adilci na nacewa game da ita. Ba ni da kamannin wannan irin halin ba ko kadan a d_: Ina son gaskiya a hukumci sosai amma ina nuna jinkai in dai na ga cewa ya kamata ga mai laifin. Na so abin da Allah ya yi, kuma na yi abin da Allah ke so. Babu mamaki, rayuwata ta yi mani daci sosai.

Ko da shike Allah haske ne wanda ke kai wa duhu hari, amma farincikinsa shi ne ya nuna kauna, ko da shi ke ya kamata mu kalubalanci zunubi, amma yana ba da sulhu tsakaninmu da shi da kuma tsakaninmu da wasu. A wurinsa hadin kai ta fi koyasuwa ta gaskiya amfani. A gareni, wanda ke hanyar gaskiya fiye da dukan komai, wannan ta zama mani babban wata wayewan kai a lokacin da na iske cewa ashe gaskiya da kanta mutum ne, kuma wannan mutumin kauna ne.

Yohanna ya rubuta bishara domin duk wadanda su ka karanta su yi bangaskiya domin su sami rai ta har abada (Yohanna 20:31). Ya kuma rubuta wasikarsa ta fari zuwa ga "wadanda kun bada gaskiya ga sunan Dan Allah ... domin ku sani kuna da rai na har abada (Yohanna I, 5:13)." Wannan wasikar ta kunshi dalilai da alamu game da ceto wanda ta kamata mu yi amfani da su ta wurin sharanta kanmu da kuma sauran mutane. An takaita wannan a Yohanna ta daya 3:23, "Umurninsa ke nan, mu bada gaskiya ga sunan Dansa Yesu Kristi, mu yi kaunar junanmu kuma, kamar yadda ya umurche mu." Ga hanyar guda biyu: Wane ne Yesu? da kuma kaunaci juna. Koyasuwa ta gaskiya wanda bata kamata a canza ta ba ita ne mai cewa Yesu Kristi shi ne Dan Allah na har abada. Duk sauran kikkirowa da bangaskiyarmu ba hujja ba ne domin

kawo rabuwa. Idan ka karbi wankewa daga wurin Yesu wanda ya aikata a bisa giciye, to, ka zama dan'uwana kenan, kuma dole ne in kaunaceka.

Ganewa da karban irin yadda Allah ke ganina ita ce mataki ta fari domin samun canji. Ko da shi ke an bani umurni domin in yi kauna, babu iko a jikina domin in aikata wannan. Dole in yi tuba daga zunubaina, in kuma bar hanya nawa ta d_, in karbi gafara nasa, da kuma alherinsa da ikonsa domin in canza (yawan naciye a kan tsarkaka tana iya zama zunubi idan mun mance da cikakkiyar hanya ta kauna). Ya bani aikin yi domin ina aiki da yarda tare da ruhun da ke cikina. Da farko, na karanta dukan Bisharu sau da yawa, in bincike da lura a kan yadda Yesu ya kaunaci mutane. Na yi nazari a cikin Zabura, domin in koyi yadda zan kawo wa Allah damuwana da ji nawa a gabansa domin in sami warkasuwa ba tare da na yi wa wani rauni ba. A karshe, sai na sake karanta rahotona, da sa hankali ga yadda Allah ke sona. A yayin da raina da kuma ruhuna ke kafa hankali ga kauna mai ban mamaki wadda ke cikin dukan kalma da aiki wanda Yesu ya yi, sai Ruhu Mai Tsarki ya sami dama ya canza zuciyata domin in zama kamar shi. Zuciyata mai shari'a da kuma ciwo ta sami warkasuwa, sai na zama na'ura a hannun Allah domin kawo sulhu da kuma warkasuwa. Babban kubuta! Abin farin ciki!


Takaitawa

Fushi a rayuwarmu tana nuna mana cewa akwai wata abu a rayuwarmu wanda ba mu mika wa shugabancin Yesu Kristi ba. Idan mun sunsuna fushi na tasowa daga cikinmu, dole mu ruga zuwa wurin Ubangiji, domin mu ji muryarsa mu kuma yi biyayya ga ita. Dole kuma mu koyi yadda za mu kawo dukan ji na ranmu a gaban Allah, domin mu ba shi izni ya bayana kansa yana aiki cikin rayuwarmu.

Allah kauna ne kuma shi Haske ne. Yana so ya nuna jinkai da kuma tausayi ga yayansa. Dukan kalmarsa da dukan aikinsa tana zuwa ne cikin kauna wanda ba ta da algus. Domin shi mai adilci ne, yana neman tsarki da gaskiya, amma dukan shari'arsa tana kunshe da jinkai.

Idan mun ci gaba da zama a gabansa, muna daukan lokaci domin mu gana da shi, muna kallon yadda kuma yana aiki a duniya ta ruhaniya, wato aikinsa na canza kome ta zama nagarta a garemu, zukatanmu za su canza a tsiffa su kuma zama kamar nasa. Za mu soma kaunar jinkai. Za mu nemi kowane irin zarafi domin mu nuna wa wasu tausayi da kuma kauna irin wanda ta yalwata a zukatanmu.


Amsa

Akwai wanda ka ke jin fushinsa? Ko kuma akwai wanda ya ci maka mugun amana wanda ba ka iya yi masa aikin gafara ba? Ubangiji yana yi maka magana a zuciya game da wasu irin yancin kai wanda har yanzu ba ka mika masa ba? Ka furta duk abin da ke zuciyarka a gaban Ubangiji, sai ka kuma ba shi

zarafi domin ya amsa maka. Watakila za ya bi da kai zuwa hanya mai kawo warkasuwa mai zurfi wanda an yi magana akai a babi ta biyar. Watakila ma za ya nuna maka wani baiwa wanda ya ke so ya baka bayan wannan halin da ka shiga ciki. Idan ka ba shi zarafi, za ya nuna maka yanda shi ya ke gani. Ka dama maganarsa da bangaskiya domin ka sami warkasuwa.
Babi Na 9
Daga Renin Kai Zuwa Daraja
Ko ka taba ji kamar bukatun da ke kanka sun fi karfinka kuma ba ka da karfi ka cika su? Ko kuma nauyin alhakin da ka dauka tana neman ta mamaye ka har ka soma firgita sosai? A ganinka mutane mafi kusa da kai masu irin wannan damuwa, ko kana ganin kamar sun fi ka karfi da jimrewa ga damuwarsu? Kana wahal da kanka ka domin ka cika aikin da ana jiranka ka gama a rana, kuma gashi baka isa ko'ina da ita ba tukun? Ko ka taba ji kamar kai ba kome ba, kuma kana firgita da kuma jin kasawarka?

Na tabbata ka sha kokuwa da irin wadannan juyayi a loto loto. Watakila a gareka wannan tana faruwa a jefi jefi ne kurum. Ko kuma naka ta zama mugun damuwa wanda ke gurgunta ka a rai, tana kuma hana cin gaba da aikata nufin zuciyarka. Ko Yesu na kula da irin wannan rai? Ko yana iya da kuma so ya zare mu daga irin wannan mugun hali ta firgita ya kuma ba mu kwanciyar rai da koshin lafiya wanda muke bukata?

Yabo ga sunansa, ba so kawai ya ke yi ba, tun d_ma yana ta addu'a ne domin ka zo ka san darajarka a cikinsa tun daga lokacin da ya zo wannan duniya a kamanin mutum. Har ma tun daren nan kafin mutuwarsa, ko da shi ke ya san cewa yana shan azaba a ruhu da kuma jiki, kana nan a zuciyarsa, yana kuma addu'a da naciya domin kai ka karbi zumunci tare da shi, wanda zata kubuta ka, daga kasawa da kuma rashin daraja (Yohanna 17:21,23).
Me Ke Kawo Renin Kai?

Ka san yadda rainin kai da kuma kin kai take yi maka a jiki. Ka gwada kanka da wasu kuma ka ga kasawar kanka. Kana kuma kokarin ka rufe wannan kasawa ta wurin kara kulawa da kayan sutura ko kuma ta wurin kokari ka boye duk abin da ba ka son wani ya sani a kanka. Ka kuma san irin bakar zuciyar wanda kana iya furta wa kowan da ya yi kusa da kai amma kuwa ka sani cewa kana yin wannan furtawan ga kanka ne da kuma ga Allah, wanda shi ne ya yi ka yadda ka ke. Watakila ka yi ta kokarin yin abubuwa daidai, domin ka rama

wa kasawarka. Watakila harshenka ya rufu kuma kwakwalwarka ta daskare saboda kunya domin kai baka yarda da kanka ba kana ganin kamar babu wani wanda zai so ya sanka.

Wai, daga ina ne irin wadannan miyagun ji da aiki su ke fitowa? Ba shakka, wadannan ayukan shaidan ne a rayuwarmu. Amma wai ta yaya ne ya ke rudinmu har gaba daya mu zo muna yaki da kanmu? Amsar daya ce da sauran irin yanayi ta zunubi wanda mun rigaya mun bincika. Idan mun cire idanunmu daga wurin Yesu muka zura wa kanmu, da wasu ko kuma walawala ta shaidan, zamu ga wata karyan yadda mu muke. Ta wurin zura wa Yesu ido ne kurum za mu iya gannin kanmu a sarari.


Dalili ta 1: Gwadawa Mara Kyau

Daya daga cikin babban dalilai na rashin ganin kanmu da daraja ita ne gwada kanmu da wasu. "Amma su da kansu, domin suna gwada kansu da kansu, suna kwa auna kansu da kansu, sun rasa fahimi (Korantiyawa 10:12b.)" Za mu iya gwada kanmu ta wurin irin siffanmu ta jiki kamar, tsayi, fadi, gashin kai, fata da wasu ababa dai na ganin damar ra'ayinmu. Za mu iya gwada kanmu ta hanyar ruhaniya, kamar, irin yawan lokacin da muke dauka a yin addu'a, da kama ayoyi ta Bibul a kai, da yawan mutanen da muka jawo wurin Ubangiji. Ko kuma za mu iya gwada baiwanmu kamar iyawa ta baiko, baiwa ta muzika ko kuma irin hanya dabam dabam wadda Allah ya bamu baiwansa.

Gwada kanka da wasu a kullum, za ya kawo ka cikin kuskure. Idan na gwada kaina da wadanda na ga cewa na fi karfinsu, babu wuya zan soma dagan kai. Ida kuwa na gwada kaina da wadanda ina gani sun fi ni a kowane irin hanya, sai na ji ni na zama kankani. Ta yaya ne zan gwada kaina? Idan bai kamata in gwada kaina da wasu ba, ta yaya ne zan iya sani cewa kome nawa na tafiya daidai? A wannan jam'iyya namu wanda babu magwaji, ba mu da abin gwada kanmu sai dai da kanmu, ta haka mun zama "marasa fahimi." Ko a makaranta ma ba a gwada mu da iyawar kanmu ba amma sai da wasu a wannan aji. Babu mamaki mana makaranta tana kawo mugun rauni ga rayuwar yaranmu.

Ta yaya ne za mu sani cewa mun ci nasara? "Gama ba shi ne wanda ke koda kansa a ke yarda da shi ba, sai wanda Ubangiji ya koda (Koranthiyawa II, 10:18). Sanin darajarmu

ta gaskiya tana zuwa ne idan mun gwada kanmu daidai yanda Ubangiji ke shirya mana a rayuwanmu. Ya halicci kowannenmu da siffa ta jiki ta musamman, da kuma ilimi da baiwa ta ruhaniya. Ya kuma bamu aiki ta musamman wanda ta kamata mu yi a rayuwarmu, kuma ya siffantamu domin mu zama daidai da aikata nufinsa. Shi kuma ba ya sharantamu domin aikin da ya ba wani ba, amma sai abin da ya adana mana mu yi. "Kuma dukan wanda am ba shi dayawa, za nemi dayawa a gareshi (Luka 12:48). " Idan, mun ba shi dama ya nuna mana kanmu a daidai yadda shi yake ganinmu, lalle za mu yi mamaki mu kuma maimaita kalmomin mai zabura din nan mai cewa, "Zan yi godiya gareka; gama kirata abin ban tsoro che, abin al'ajibi che kwa: Ayukanka suna da ban al'ajibi; wannan ma raina ya sani sarai (Zabura 139:14).

Ubangiji yana yi mana hukunci ne daidai da cikakken sani wanda ya ke da shi a kanmu. Ka tuna da wannan misali na baiwa wadda ke cikin littafin Matta 25:14-30. Mai gidan nan ya ba kowane bawansa daidai gwargwadon iyawarsu. Bayin nan biyu na fari, wanda suka karbi talent biyar da kuma biyu sun yi hikima a hidimarsu har sun ci riba na talent biyar da kuma biyu. Zuwa ga shi wannan bawa na fari, wanda ya ci riban talent biyar, shi maigidansa ya ce masa, "madalla, kai bawan kirki, mai-maiaminchi: K_ yi aminchi chikin matsaloli kadan, ni sanya ka a bisa mai-yawa: Ka shiga chikin farin zuchiyar Ubangiji ka (Matta 25:21)." Shi bawa na biyun ya kara masa talent da guda biyu kurum. Amma me maigidansa ya gaya masa? Ko ya tambaye shi dalilin da ya sa bai ci riba ba talent biyar kamar shi bawa na farko ba? Ko ya hukunta shi domin ya kasa aikata hidima kamar shi na farkon? Babu ko kadan. A maimakon haka ya ma ba shi daidai irin magana ta albarka wanda ya ba shi bawa na farko wanda ya ci riban talent biyar din nan: " Madalla, kai bawan kirki mai-aminchi: ka yi aminchi chikin matsaloli kadan, ni sanya ka bisa mai-yawa: ka shiga chikin farin zuchiyar ubangijinka." Shi Ubangiji ya san iyawarmu kuma ba ya zato kasa da haka ko kuma fiye da haka.

Yaya za mu yi da matsalolin rayuwarmu wanda kasawarmu ta nuna a sarari? Ta yaya ne za mu ci gaba a cikin irin wannan kasawarmu wanda muke gani a fili? "Amma ya che mani,

Alherina ya ishe ka: gama chikin kumamanchi ikona ya ke chika. Na gwammache fa in yi fahariya chikin kumamanchina, wannan kwa da farin chiki ma yawa, domin karfin Kristi shi innuwantadda ni. Domin haka fa ina jin dadi chikin kumamanchi ... gama sa'anda ina rashin karfi, sa'annan mai-karfi ni ke (Koranthiyawa 12:9,10)." Idan mun mika kasawarmu (kumamancinmu) domin Kristi ya cika shi da karfinsa, wannan sashi ta kasawarmu za ta zama sashi ta karfinmu mafifici. Ba ya kamata mu ji kunya ko kuma ji fushi da kasawarmu ba, domin su ne hanya wanda Kristi za ya yi amfani da su domin ya nuna al'ajibin daukakarsa a rayuwarmu. "Amma Allah ya zabi abubuwan marasa -hikima na duniya, domin shi kunyatadda wadanda su ke masu-hikima ... domin kada kowane mai-rai shi yi fahariya gaban Allah ... domin bisa ga yadda an rubuta, wanda shi ke yin fahariya, shi yi fahariya chikin Ubangiji (Koranthiyawa 1:27, 29, 31)."

A lokacin da nake a makaranta Ni ba dalibi mai kwazo sosai ba ne. Na ki jinin Turanci, da hada harufa, da nahawu, da Karatu da kuma yin magana a gaban jama'a. Ni ba kwararen dalibi ne a irin wadannan farne ba, har wa yau wadannan sun zama mani abubuwa ne na kasawa sosai. Amma Allah ya kira ni domin ya yi amfani da ni duk da irin muni nawa ta hada yare (nahawu) da kuma irin rashin iyawata ta wurin hada harafi domin in ba Ikkilisiyarsa sakonsa ta wurin rubutacciyar kalma. Ni ba na fahariya da kasawata, kuma ba na hura hanci domin abin da na aikata ta hannuna, domin a sarari wannan aikin Kristi ne.

Su abubuwan da ma iya yi sosai fa? Yaya zan yi da su? A farko, ana so in yi cikakkiyar amfani da dukan iyawata. Idan na yi amfani da baiwata domin bauta wa Ubangiji, dole in karu in kuma yi girma a cikinta. Kamar wannan bawan nan da ya ci riba na talent biyar, aka ba shi karin guda daya, ta haka mu ma za mu iya yin amfani da abinda aka bamu domin mu karu a cikin baiwarmu. Na biyu, ya kamata mu yi amfani da karfinmu domin mu taimaki marasa karfi. A maimakon yin fahariya da kuma danne marasa baiwan da muke da shi, ya zama dole mu mika baiwanmu a garesu domin mu rufe asirin kasawarsu mu kuma ba su karfi.

Wannan hali ne ta kamata mu nuna a dukan hidimomin rayuwarmu, daga gida har zuwa ikkilisiya da kuma hidimominmu. Misali ita ne, yawancin mazaje sun banbanta da matansu sosai. Irin wannan ne ta ke jawo su ga juna a farko. Kowa a cikinsu na hangar abinda babu a rayuwarsa daga cikin halin dayan, wannan kuma ta jawo su kusa. Amma abin damuwa ita ce, bayan an yi aure, sai wata canji za ta shigo ba tare da saninsu ba. A maimakon mu daraja karfin dayan, sai mu soma hukunci a kan kasawarsa. A maimakon mu goyi bayan juna da karfinmu, sai mu soma g_sa domin mu kunyata dayan domin mu kuma mu sami daraja da yarda. Allah na so duk wadannan hali ta g_sa da juna da kuma sara su daina. Shi ya hada mu domin mu hada karfinmu wuri daya, mu kuma yaki dukan kasawarmu, a cikin karfinsa kuma za mu iya fuskanci dukan matsaloli.
Dalili ta 2: Rashin Sani Ko kuma bin Ka'idodin Littafi Mai Tsarki

An halicce ka a kamanin Ubangiji Allah. Kana da muhimmanci a gabansa, har shi ya sa ya ba da Dansa shi kadai domin ya yi mugun mutuwa domin ya dawo da kai zuwa cikin zumunci da shi. Shi Allah, mahaliccin dukan duniya da abubuwanda ke kewaye da ita, ya san ka har ma yana kiranka da sunanka. A cikin Littafi Mai Tsarki, akwai zance mai yawa game da darajan mutum, da kuma dalilin da Allah na so ka ga kanka da daraja. Akwai Littatafai masu yawa wanda an rubuta game da wannan darasi, kuma ina karfafa duk masu fama da rashin daraja kansu su karanta ko da a ce daya ne kurum a cikinsu, domin karfafa iliminsu da bangaskiyarsu a kan yadda suna daukan kansu. Akwai, "You're someone special" (Kai Mutum Mai Muhimmanci ne) wanda Bruce Narramore ya rubuta, da kuma "His Image, My Image (Yadda ya ke Gani na, da yadda nake ganin kaina) wanda Josh McDowell ya wallafa.

Ba zan bata lokaci akan darasai wanda wasu sun rigaya sun yi magana ko rubuta a kai ba, za a iya samunsu a wasu wurare. Ina so in kara wata darasi ta ruhaniya guda daya wanda mutane suna mantawa. Farawa sura 2 da 3 sun nuna a tsarari cewa an halicce mu ne domin mu yi sarauta kamar

sarki da sarauniya. Allah a farko ya shirya mu domin mu zama makaddashinsa a duniya, domin mu yi mulki daga wurin ikonsa mafifici. A cikin zurfin ranmu, akwai wata yunwa domin a ba mu daraja kamar ta sarki, wanda kuwa mu ne. Bayan kuwa mun karbi sulhu ta Allah ta wurin cetonsa, muna sake samun wannan girma da masayi ta sarakuna da firist, kuma wannan yunwa tana samun koshi. Idan mun yi kokari mu sami wannan daraja da iko ta wata hanya illa mika kanmu ga sarkin sarakuna, to, lalle, zunubi da kasawa za ta mamaye mu.

Wannan gaskiya, da kuma wanda za ka samu a sauran littatafai wanda an karfafaka ke karanta, ba za su kubuta ka daga rena kai mai zurfi ba. Wahayi daga wurin Ruhu Mai Tsarki wanda ke zuwa cikin zukatanmu bayan mun gamu da Yesu fuska da fuska shi ne kadai mai iya warkar da rayukanmu. Wannan hanya ce ke ba da tushen gaskiya daga wurin Ubangiji wanda ke kawo kalmarsa ta filla filla domin ta yi mana amfani a wata bukatarmu. Gamuwa da Allah mai rai ne kadai kan iya ba mu rai.

Bin ka'idodin gaskiya ba za ta taba bamu lafiya ko warkasuwa ba, kome kyaun wadannan ka'idodin. Masu bin addini na lokacin Yesu suna "... bin chikin littatafai, domin suna tsammani a chikinsu suna da rai na har abada." Yesu kuma ya ce masu "Su ne fa suna shaidata: amma ba ku yarda ku zo wurina ba, domin ku sami rai (Yohanna 5:39,40)." Rai na har abada ita ce sanin Allah, wato yin cikakken ma'amala da shi (Yohanna 17:3). Irin wannan ma'amala ta gaskiya mai zurfi tare da Allah ne Yesu ya yi



Dalili ta 3: Rayuwar ta Sama Sama

A karshe, daraja kanmu ta ainihi tana faruwa ne idan mun sami sanin zumunci mai zurfi tare da Yesu Kristi. A cikin Littafi an ce, "Rayuwata Kristi ne," da kuma "Kristi shi ne rayuwana." A kai da kai mun ga an fada a Sabon Alkawali a lafiyayyen harshe cewa, "An giciye ni tare da Kristi; yanzu kuma ba ni ba ne ina rayuwa, amma Kristi ke rayuwa daga chikina: Wannan rai kuwa da ni ke rayuwa chikin jiki yanzu ina rayuwa chikin bangaskiya, bangaskiya wadda ta ke chikin Dan Allah ... (Galatiyawa 2:20)." Samun zumuncimai zurfi ne ta warkar mani da renin kai, da tsoro, da kuma kasawata har ta kuma ba ni dama domin in sami sanin hadinkai tawa da Kristi.

Babu wuya mu manta da wannan zumunci har mu koma zuwa rayuwa ta sama sama. Ina jin kamar cikina tana nan kango, domin "Ni" ba "Ni na Kristi" ba amma ni na kaina ne, wannan na sa ina fuskantar abubuwar rayuwa ni kadai. Darajar kaina za ta lalace; Ina ji kuma kamar an kakkarya ni, kaina kuma a birkice kamar roba wanda an j_.

Watakila dukanmu muna da lokaci wanda muna ji kamar haka. Akwai wasu ranaku wanda in na shiga offishi da safe, sai in ga tulin wasiku wanda ke jiran amsata, da kuma sakonni masu jiran amsa, shiri domin koya darasi a ajujuwa, da kuma littafai wanda ta kamata in rubuta. Domin ni mai son aiki ne, sai in dukufa da aiki, da bangaskiya cewa ai zan iya gama wannan aiki duka. Amma kafin rana ta sauka, sai in soma karban waya na tarho, kuma ga mutane masu shigowa domin neman izni su yi magana da ni, ga kuma ma'aikatana na neman taimako daga wurina, nan ne damuwata za ta soma tashi. Kafin a ce rabin rana ta yi, ta zama a sarari cewa ba zan iya karasa wannan aiki a ranar ba. Idan na ci gaba a ranar a kamar yadda na fara ta cikin dangana ga nawa iyawa, wannan rana za ta zama bala'i. Ba wuya in zama da fushi, da pitina, da kuma in sabawa kowa da magana domin rashin iyawata a ranar. A karshen ranar, kadan kurum daga abubuwan da na shirya zan yi za ta yiwu kuma duk alamar salama wanda ke zuwa ta wurin zumunci da Kristi za ta bata gaba daya.

Amma ba haka ranar ta kamata ta zama ba. Daga lokacin da na farka da barci da safe, zan iya mika duka ayukana ga shugabancin Ruhu Mai Tsarki. A yayinda na shigo ofishi na kuma taras da wannan aiki mai yawa mai neman in ba su lokaci, zan yi tsit a gaban Ubangiji, in kuma tambaya ko me ya ke so na yi a wannan rana. A yanzu zan iya furta cewa ba ni ke rayuwa ba amma Kristi shi ne rayuwata. Yanzu kuma na dangana a gareshi domin ya nuna mani yanda zan bi da rayuwata, ya kuma ba ni haske game da irin hanyar da zan bi. Za ya nuna mani wurin da zan fara, za ya kuma ba ni alherinsa domin in yi albarka

a cikin yin abin da ya gaya mani in yi. A wasu lokatai ma za ya iya sa ni in yi abin da ba ta cikin nawa lissafi. Amma idan na nace zan bi hikimarsa, ina da salama a wannan rana, domin na sani cewa Ina yin nufinsa a cikin karfinsa, shi kuma za ya dauki nauyin dukan matsaloli. Idan wata harka ta abko mani, sai in yi maraba da ita kamar ta fito ne daga wurin Ubangiji. Idan dai na manne masa, zan sami salama da farin ciki a zuciyata, har kuma da zukatan duk wadanda nake yi masu bisharan Kristi.

Zumunci nawa da Kristi abu ce ta har abada idan na sami haihuwa ta biyu. Babu abin da za ya raba ni da shi. Ba wai ina rayuwa dabam da shi ba; amma irin na wa gani ne tana da algus. Domin haka, idan na iske cewa na soma dangana ga yancin kai na wa ta karya domin aikata al'amura, nan da nan sai in jawo kaina, in yi tuba da sauri in kuma dawo wurin gaskiyar da ke zuciyata. Ta cancanta dukanmu mu san hanya mafi kyau wanda za ta dawo da mu daga rayuwa ta sama sama zuwa rayuwa ta zurfi mai gaskiya. A gareni, yabo daga zuciyata, da sujada da kuma rubuta rahoto su ne hanyoyi mafi amfani. Ga wasu kuma, yana iya zama karatun Littafin Allah, ko kuma zama a bakin rafi, ko kuma a dunkule kusa da wuta a waje, ko kuma a yin wata aiki mara jan karfin mutum (wato yin amfani da na'ura ke nan) Ka fahimci abin da za ka iya yi wanda za ta sa ka jin kamshin fuskar Allah a cikin zuciyarka ka kuma yi amfani da ita a duk lokacin da ka ke so ka dawo zuwa ga wannan zumunci da shi mai rai.

Takaitawa

Renin kai wata illa ce wanda ke mamaye al'ummanmu. Akwai ababa da yawa masu jawo wannan kamar: gwada kanmu da wasu a hanya mara kyau, rashin sani da kuma amfani da wasu darasi ta gaskiya wanda ke cikin maganar Allah wanda ke magana game da yadda za mu auna kanmu, da kuma rayuwa wanda ba ta san zancen zumuncinmu da Kristi ba. Samun sanin darajar kai ta gaskiya ta na zuwa ne daga lokaci wanda aka bata a gabar Ubangiji. Shi za ya koya mana ababa a kanmu, ya kuma koya mana yadda za mu gane karfinmu domin ya yi amfani da ita ta wurin yabonsa da kuma taimaka wa wasu da kuma mika.masa kasawarmu domin ya cika ta domin kuma shi ya sami daukaka. Za ya dauki gaskiya ta littafi ya maida su ru'ya ta sani wanda ke iya canza zukatanmu. Za ya jagorancemu a cikin sannu zuwa ga rayuwa mafifici mai kara sanin zumunci tare da shi.



Amsa


Yaya ne girman renin kai, tsoro da rashin iyawa a rayuwarka? A yayin da kake karanta wannan babi, ko Ruhu Mai Tsarki ya nuna maka dalilan da ke jawo maka wannan rainin kai? Idan haka bata faru ba, ka tambaye shi domin ya nuna maka a yanzu. Sai ka yi shiru da kanka, ka kuma karbi wahayi wanda yake so ya ba ka domin ya warkar da zuciyarka mai rauni.


Yüklə 361,5 Kb.

Dostları ilə paylaş:
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©genderi.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

    Ana səhifə